Yadda Birtaniya da ƙasashen duniya 28 suka caccaki Isra'ila kan yaƙin Gaza

GAZA

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Wata sanarwa da ƙasashe 28 suka fitar, ta ce ba za su amince da buƙatar Isra'ila na sauya wa ɗaukacin al'ummar Gaza miliyan 2.1 matsuguni zuwa wani wuri ba, inda suka ƙara da cewa "tilastawa al'umma tashiwa ya saɓa wa dokokin jin-ƙai na ƙasa da ƙasa."

Ƙasashen sun yi kira ga Isra'ila da Hamas da kuma al'ummomin ƙasashen waje da su "kawo karshen wannan rikici ta hanyar tsagaita wuta na dindindin nan take ba tare da wani sharaɗi ba."

Sun kuma bayyana cewa a shirye suke don "ɗaukar ƙarin matakai da za su taimaka wajen tsagaita wuta nan take da kuma bayar da hanyar samun zaman lafiya da tsaro."

Birtaniya da wasu ƙawayenta na yamma 27, ciki har da Faransa da Italiya da Canada da kuma Australiya sun yi kira da a kawo karshen yaƙin Gaza "nan take", inda sanarwar da suka fitar ta ce uƙubar da fararen-hula Falasɗinawa ke ciki ya kai maƙura."

Sanarwar haɗin gwiwa da ƙasashen 28 suka fitar ranar Litinin, sun "buƙaci dukkan ɓangarori da al'ummomin ƙasashen waje da su haɗa-kai domin ganin an kawo karshen wannan rikici nan take ba tare da sanya wani sharaɗi ba.

Sai dai, Isra'ila ta yi watsi da sanarwar, inda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Oren Marmorstein, ya ce sanarwar ta "sauka daga aininin abin da ke faruwa" kuma gwamnatin Isra'ila ta yi "watsi" da ita.

"Kowane irin zargi ya kamata a miƙa shi kai-tsaye ga ɓangaren da ya ƙasa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin sauran mutanen da ake garkuwa da su da, musamman Hamas, wadda ta fara wannan yaƙi da kuma haƙikance kan cigaba da yin yaƙi," in ji Oren.

Masar ta yi maraba da sanarwar, inda ta yi kira na kawo karshen yaƙin Isra'aila a Zirin Gaza - ta kuma yi Alla-wadai da abubuwan da Isra'ila take aikatawa a Zirin, da dakatar da shigar da agaji ga al'ummar yankin, a cewar wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta Masar.

Masar dai ta goyi bayan matsayar da ƙasashen da suka fitar da sanarwar suka ɗauka, waɗanda suka yi watsi da buƙatar tayar da Falasɗinawa daga Gaza da sauya musu matsuguni zuwa wani wuri na daban.

Haka kuma, Masar ɗin ta yi na'am da watsi da buƙatar Isra'ila na faɗaɗa wuraren ƴan kama wuri zauna a Gaɓar Yamma da kuma tashin hankali da ƴan kama wuri zaunan suka haddasa a can.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Masar ɗin ta fitar, ta ƙara nanata ƙoƙarin da ƙasar ke yi wajen ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, ta hanyar haɗin gwiwa da Qatar da kuma Amurka - kuma da buƙatar al'ummomin ƙasashen waje su ɗauki matakai na amincewa da mafitar samar da ƙasa biyu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban hukumar lafiya ta duniya ya buƙaci Isra'ila ta saki wani jami'in hukumar wanda dakarunta suka kama a lokacin wani hari da suka kai tsakiyar Gaza a jiya Litinin.

Har yanzu dai Isra'ila ba ta ce komai ba a kan batun.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce dakarun Isra'ila sun jefa rayuwar ma'aikatansa da iyalansu cikin haɗari lokacin da suka kutsa cikin sansanin da suke zaune a Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza.

Haka nan kuma ya ce hare-haren sama da dakarun Isra'ila ke kai wa yankin sun yi ɓarna mai muni a mazaunin jami'an hukumar lafiya ta duniya.

Duk da haka, ya yi alƙawarin cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan ta a yankin.

Yaƙin da aka shafe kusan shekara biyu ana yi a yankin ya tilastawa Falasɗinawan da suka rasa muhallinsu komawa Deir al-Balah domin neman mafaka.

Amma a karon farko, motocin yaƙin Isra'ila sun kutsa yankunan kudanci da gabashin Gaza a jiya Litinin.

Jami'an lafiya sun ce dakarun Isra'ilan sun yi luguden wuta kan gidaje da masallatai a yankin.

Tuni dai Majalisar Dinkin Dunya ta yi martani, inda sakataren janar na majalisar ya ce ya kaɗu da yadda ake ci gaba da kaya sharuɗɗan mutumta ɗan Adam a Gaza, yayin da ƙasashen duniya ke ci gaba da sukar Isra'ila a kan yaƙin.

Antonio Guterres ya ce fatan ƙarshe ta rayuwa ga Falasɗinawa ya ɗauki hanyar kuɓuce masu. Ya kuma koka da yadd yunwa ke ci gaba da addabar Falasɗinawa.

Ƙorafin nasa na zuwa ne bayan sanarwa da wata gamayyar ƙasashe aƙalla 30 ta fitar, ciki harda Birtaniya da Faransa, inda ƙasashen suka ce ''Dole Isra'ila ta kawo ƙarshen yaƙin da take a Gaza.''

Isra'ila ta bayyana sanarwar ƙasashen a matsayin wani abu mai nuni da yadda ba su fahimci "haƙiƙanin abin da ke faruwa" ba.

Ta zargi Hamas da kawo cikas da kawo cikas ga aikin bayar da tallafi ga mabuƙata, a madadin mutumta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin mutanen da ta yi garkuwa da su.