Shin Trump zai iya lallashin Iran ta yi watsi da shirinta na nukiliya?

Asalin hoton, Reuters / Getty Images
Donald Trump mutum ne da yake son gudanar da al'amuransa da gaggawa.
A ƴan watanni ƙalilan da ya ɗauka kan mulki, shugaban na Amurka ya gaza samar da zaman lafiya a Gaza da kuma Ukraine.
Ya yi ruwan bama-bamai a Yemen. Ya kuma kaddamar da yaƙin kasuwanci a duniya. Yanzu yana son mayar da hankalinsa ga Iran.
Wannan na cikin jadawalin shugaban. Ga Trump, akwai sauran rina a kaba tsakaninsa da Iran.
Matsalar har yanzu tana nan kamar yadda take a baya: Me zai dakatar da Iran daga mallakar makaman nukiliya?
Iran ta musanta cewa tana shirin mallakar makaman nukiliya. Sai dai wasu ƙasashe sun yi imanin cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran na son mallakar makaman nukiliya, abin da zai iya janyo ƙoƙarin mallakar makamai ko kuma babban yaƙi a Gabas Ta Tsakiya.
A 2015, Iran ta cimma wata yarjejeniya (JCPOA) da Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha da kuma China.
Ƙarkashin yarjejeniyar, Iran za ta rage burinta na son mallakar nukiliya - da kuma bai wa masu sa ido na ƙasa da ƙasa shiga ƙasar - inda ita kuma za a ɗage takunkumim tattalin arziki da aka ƙaƙaba mata.
Sai dai Trump ya janye daga yarjejeniyar a 2018, inda ya yi iƙirarin cewa yarjejeniyar ta mara wa ta'addanci baya ta hanyar tallafa wa ƙungiyoyin mayaƙa da ke samun goyon bayan Iran irin su Hamas da Hezbollah. Amurka ta sake ƙaƙaba takunkuman.
Daga baya Iran ta yi watsi da wasu takunkuman yarjejeniyar, inda ta kara mayar da hankali kan shirin nukiliyarta.
Masu sharhi na fargabar cewa nan ba da jimawa ba Iran za ta iya mallakar makaman nukiliya.
Hukumar nukiliya ta duniya (IAEA) ta yi ƙiyasin cewa makamashin uranium da Iran ke da shi wanda ya kai kashi 60, zai iya ƙera manyan bama-bamai har guda shida idan ya kai matakin ƙarshe.
A kwanakin rantsar da shi kan mulki, Trump ya mayar da tsohon tsarinsa na "matsa wa Iran lamba".
A ranar 4 ga watan Fabrairu, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya, inda ya umarci baitil-malin Amurka ya ƙaƙaba ƙarin takunkumai kan Iran da kuma hukunta ƙasashen da ke hulɗa da ita, musamman masu sayan man Iran.
Yanzu, fadar White House na fatan magance matsin tattalin arziƙi ta hanyar diflomasiyya.
A watan da ya gabata, Trump ya aika wasika zuwa ga shugaban addini na ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei. Shugaban ya nemi tattaunawa da kuma cimma yarjejeniya cikin watanni ƙalilan.
A yanzu, ya amince ya karkata tattaunawa tsakanin jami'an Amurka da Iran zuwa Oman a ƙarshen mako.
Barazanar Amurka ga Iran ta fito ƙarara: Su amince da yarjejeniya ko su fuskanci ɗaukar matakin soji a kansu.
"Idan ba a cimma yarjejeniya da Iran ba, ina ganin Iran za ta shiga babbar matsala," in ji Trump ranar Litinin.

Asalin hoton, Getty Images
Shin ta yaya Iran za ta mayar da martani?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu masu tsare-tsare a Tehran suna da yaƙinin cewa cimma yarjejeniya, za ta saka a ɗage wa ƙasar takunkumai.
Tattalin arziƙin Iran na cikin mawuyacin hali, inda ake samun ƙaruwar hauhawar farashi da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar.
Sai dai duk wata yarjejeniya da za a cimma za ta buƙaci sadaukarwa waɗanda zai yi wuya a iya ɗauka.
Iran ta fuskanci koma-baya a ƴan watannin nan, inda yaƙi da Isra'ila ya ƙarya lagon mayaƙa da take mara wa baya da kuma hamɓarar da gwamnatin da ƙawarta a Syria, shugaba Bashar al-Assad.
Wasu a Tehran sun bayyana cewa yanzu ne ya fi dacewa a gina makamin nukiliya domin taka burki ga wasu.
Ga alamu Amurka da Iran ba sa kan turba ɗaya. Matsayarsu kan tattaunawar ba ta fito fili ƙarara ba.
Sai dai Amurka ta bayyana ƙarara cewa tana son Iran ta yi watsi da shirinta na nukiliya, ciki har da kawo karshen mallakar makamashin uranium da kuma dakatar da goyon baya ga Hezbollah a Lebanon da kuma Ƴan Houthi a Yemen.
Amma zai yi wuya Iran ta amince da hakan.
Haramta shirin mallakar nukiliya gaba-ɗaya - ko don dalilin farar hula - an daɗe ana ganin haka a matsayin abu da Tehran ba za ta amince da shi ba.
Akwai kuma matsalar ƙwarewa kan fasaha a Iran: masana kimiyyarta yanzu sun fi sanin ilimin ƙera makamin nukiliya idan aka kwatanta da shekara goma da suka wuce.
Ga Isra'ila, ta faɗa ƙarara cewa za ta amince ne kawai da dakatar da shirin mallakar nukiliya baki-ɗaya na Iran. Firaiminista Benjamin Netanyahu ya ce zai amince da "yadda aka yi a Libya".
Yana magana ne kan matakin da marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi ya ɗauka na watsi da ɗaukacin shirinsa na nukiliya a 2003, inda aka ɗage musu takunkumi bayan haka.
Sai dai da wuya Iran ta yi irin haka.
Me zai faru idan aka gaza cimma yarjejeniya?
Isra'ila ta daɗe tana yunkurin son afamdani da karfin soja don wargaza shirin nukiliyar Iran. Sai dai ta binne da yawa a can karkashin ƙasa.
Masana harkar soji sun ce Isra'ila na son ba Amurka kaɗai ba wajen tayar da Iran, za ta kuma buƙaci samun dakaru na musamman a ƙasa domin tabbatar da cewa an wargaza nukiliyarta.
Wannan na nufin cewa matakin soji zai kasance mai haɗari, kuma ba lallai a samu nasara ta hakan ba.
Trump ya kuma yi alkawarin cewa ba zai shiga yaƙe-yaƙe ba lokacin da ya sha rantsuwa, amma shiga rikici da Iran zai iya kasancewa ɗaya daga cikin yaƙe-yaƙe da yake gudu.
Wannan bai sa shugaban na Amurka ya daina bai wa Isra'ila makaman kariya na sama ba da kuma aika jirage marasa matuki masu cin dogon zango na B2 zuwa yankin.
Don haka, zuwa yanzu, alamu sun nuna cewa Trump na duba hanyoyin diflomasiyya domin samun mafita - wani abu da Isra'ila za ta gani a matsayin gazawa, ba tare da duba tanade-tanadensa ba.
Amma idan aka ƙasa cimma yarjejeniya, zai ɗauki matakin amfani da ƙarfin soji, abin da kuma ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Yanzu dai, shugaban ya bai wa dukkan ɓangarori watanni biyu domin a samu cimma yarjejeniya.
Watakila ya manta cewa an ɗauki tsawon shekara biyu kafin cimma yarjejeniyar JCPOA. Hanyar diflomasiyya da aka yi ta cikin gaggawa, ba ta cika haifar da ɗa mai ido ba.











