Me ya sa Iran ke bayyana rumbunan makamanta na sirri da ke ƙarƙashin ƙasa a yanzu?

Ɗaya daga cikin biranen makamai masu linzami kenan a Iran, inda aka jibge nau'in makamin Kheibar Shekan mai cin dogon zango

Asalin hoton, Tasnim

Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin biranen makamai masu linzami kenan a Iran, inda aka jibge nau'in makamin Kheibar Shekan mai cin dogon zango
    • Marubuci, Farzad Seifikaran
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
  • Lokacin karatu: Minti 5

"Idan muka fara buɗe biranen makamai a kullum tsawon shekara biyu ba za mu gama ba har nan da shekara biyu..."

Da irin wannan kalaman Iran ta fara bayyana wasu jerin unguwanni na ƙarƙashin ƙasa da ke ɗauke da makamanta masu linzami da za ta yi amfani da su wajen abin da ta bayyana a matsayin ramuwar hare-hare kan Isra'ila da Amurka.

An ce Amurka ta fara tura jiragen yaƙinta shida a makon da ya gabata masu ƙarfin kai hari da manyan bamabamai a Iran da Yemen, kamar yadda wasu majiyoyi suka faɗa wa kamfanin klabarai na Reuters.

Iran ta mayar da martani tana cewa yawan dakarun Amurka a yankin "na nufin suna zaune cikin gidan gilashi" kuma bai kamata su "yi jifa da dutse ba".

Ira ta kuma yi barazanar yin ruwan wuta kan wani sansani da ke tsibirin Diego Garcia ƙarƙashin ikon Birtaniya, wanda kuma ake shirin bai wa ƙasar Mauritius. Ba ta taɓa yin barazana irin wannan ba.

Me waɗannan unguwanni da ake kira "missile cities" a Turance ke nufi, kuma me ya sa Iran ta zaɓi ta bayyana wa duniya su a yanzu da kuma yiwuwar ɓarkewar yaƙi a Gabas ta Tsakiya?

Mene ne unguwannin Iran na makamai masu linzami?

An ce wannan ɗaya ne cikin wuraren haɗa makaman na rundunar IRGC ta Iran da ke ƙarƙashin ƙasa?

Asalin hoton, IMA Media

Bayanan hoto, An ce wannan ɗaya ne cikin wuraren haɗa makaman na rundunar IRGC ta Iran da ke ƙarƙashin ƙasa?

"Missile cities" ko kuma unguwanni na makamai wata jimla ce da rundunar sojin Iran Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ke amfani da ita domin siffanta manyan rumbunan ƙarƙashin ƙasa na makamanta.

Sansanonin wasu jerin wurare ne da hanyoyi masu faɗi, masu ɗamfare da juna da suka jaraɗe ƙasar baki ɗaya, kuma akasarinsu suna yankuna ne masu duwatsu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akan ajiye kayayyakin, da shirya su, da kuma harba makamai masu cin dogon zango, har ma da jirage marasa matuƙa da kuma makaman kare sararin samaniya.

A cewar kwamandojin IRGC, ba makamai masu linzami kawai ake ajiyewa ba a cikinsu, wasu daga cikinsu ma'aikatu ne "da ake harhaɗawa da samar da makaman kan su".

Ba a san takamaiman inda waɗannan rumbuna suke ba kuma ba a taɓa bayyana su ba a hukumance.

Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh, kwamandan sojin sama na rundunar IRGC, ya ƙaddamar da unguwar makamai ta baya-bayan nan cikin wani bidiyo da ya nuna makaman da jirage marasa matuƙa a ƙarƙashin ƙasa yayin hira da kafar gwamnatin ƙasar ta IRIB.

Game da me ya sa aka fito da su a yanzu, kafar yaɗa labarai ta gwamnatin ƙasar ta ce Iran za ta yi amfani da su ne wajen rama "duk wani hari da aka kai kan Iran".

"Ba za a bambance ba wajen kai wa dakarun Amurka ko na Birtaniya hari matuƙar aka takali Iran daga kowane irin sansani ko yanki da makaman Iran za su iya kaiwa," in ji Iran ɗin.

Cikin shekara 10 da suka wuce, IRGC kan fitar da hotunan hanyoyin ƙarƙashin ƙasa masu ɗauke da makamai masu yawa, da jirage marasa matuƙa, da makaman kariya, inda take kiran su da "ɓoyayyun unguwannin makamai".

Ko Amurka da Isra'ila za su iya ja da waɗannan rumbuna?

Iran na fatan ta dakatar da aniyar Isra'ila da Amurka ta kai mata hari ta hanyar bayyana ƙarfinta.

Bidiyon baya-bayan nan ya nuna makaman Kheibar Shekan, Haj Qasem, Emad, Sejjil, Qadar-H, Paveh.

Iran ta yi kurin cewa za ta iya kai wa ƙasashe hari masu nisan kilomita 2,000.

Makamin Emad na cikin waɗanda ta yi amfani da su wajen kai wa Isra'ila hari a watan Afrilun 2024, wanda ya yi ɓarna a sansanin sojin sama na Navatim da ke tsakiyar Isra'ila.

Hanya mafi sauri daga Iran zuwa Isra'ila ita ce ta saman ƙasashen Iraƙi, da Syria, da Jordan mai nisan kilomita 1,000. Isra'ila ta ce ta kakkaɓe kashi 99 cikin 100 na makaman a harin watan Afrilu. Harin watan Oktoba ma bai yi wata mummunar ɓarna ba.

Amma kuma ana nuna tantama game da nisa da kuma kaifin makaman na Iran, abin da ya sa ake kallon barazanarta na kai wa Tsibirin Diego Garcia hari a matsayin wani muhimmin abu.

Sansanin da Amurka da Birtaniya ke amfani da shi, an ƙaddamar da shi ne tun shekarun 1970. Amma kuma sansanin na da kariya sosai, wanda ke da nisan 3,800 daga wurin mafi kusa a cikin Iran.

A wannan makon, Iran ta yi iƙirarin cewa jirginta maras matuƙi samfurin Shahed 136B zai iya yin tafiyar kilomita 4,000, kodayake dai ba a tantance wannan iƙirari ba.

Duk da cewa akwai yiwuwar Iran ba ta da makamin da ya zarta nisan kilomita 2,000, akwai hanyoyin da za ta iya kaiwa ga tsibirin, kamar amfani da jiragen ruwa, ko kuma yi wa makaman rokarta kwaskwarima.

Yanzu haka akwai dakaru da kayan aikin Amurka masu yawa a Gabas ta Tsakiya, kuma nan gaba kaɗan jiragenta na ruwa biyu masu dakon jiragen yaƙi za su isa yankin.

Hotunan tauraron ɗan'adam da ke ƙasa sun nuna jiragen yaƙi samfurin B-2 a tsibirin Diego Garcia, waɗanda aka yi amfani da su wajen kai wa mayaƙan Houthi hari a Yemen.

"Idan har Iran ko ƙawayenta suka yi wa kadarori ko dakarun Amurka barazana a yankin, Amurka za ta ɗauki mataki nan take domin kare al'ummarmu," a cewar mai magana da yawun fadar tsaron Amurka Sean Parnell a makon nan.

Rundunar sojin Amurka ta ƙi bayyana adadin jiragen B-2 da ta aika tsibirin na Diego Garcia.

Amurka na da samfurin B-2 guda 20 ne kawai, saboda haka a kodayaushe ake yin kaffa-kaffa wajen amfani da su.

Me ya sa Iran ta bayyana unguwannin makaman a yanzu?

Bidiyon na baya-bayan nan ya ɓulla ne a daidai lokacin da zukata ke ƙara zafi tsakanin Iran, da kuma Amurka da Isra'ila, sai kuma barazanar mayaƙan Houthi na Yemen. Haka nan, akwia yunƙurin cigaba da tattaunawa kan yarjejeniyar makamin nukiliya na Iran.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Iran barazana a ranar Lahadi ta kai hari da kuma ƙarin haraji idan ta ƙi yarda da ƙulla sabuwar yarjejeniya kan shirin nukilyar nata.

Kazalika, lamarin na zuwa bayan hare-haren da Isra'ila da Iran suka kai wa juna, kuma bayyana makaman na tabbatar da iƙirarin cewa tana da ikon rama duk wani hari da gayya.

Har yanzu Iran na alƙawarin cewa za ta kai wa Isra'ila hari a karo na uku. Sai dai ana yawan neman kada ta yi hakan, inda wasu ke nuna damuwa kan yadda ramuwar da Isra'ila ta yi ta lalata shirin makaman nata.

A cikin gida, gwamnatin ƙasar na son ta tabbatar wa 'yan ƙasarta cewa har yanzu tana nan da ƙarfinta, kuma za ta iya kare kan ta daga duk wata barazanar Amurka.

Dabarar gina unguwannin makamai a ƙarƙashin ƙasa ita ce kare su daga hare-hare ta sama. Gina su ya bai wa ƙasar damar ɗaga wa Amurka da Isra'ila yatsa cewa za ta iya ramawa ko da an lalata sansanoninta da ke kan ƙasa.

Rumbunan da ke ƙarƙashin ƙasa na bayar da damar harba makamai daga wuraren da abokin hamayya bai sani ba, wanda zai ƙara rikita tunaninsa.