Iran da Amurka sun amince su tattauna kan makamin nukiliyar Iran

Asalin hoton, Getty Images
Iran ta tabbatar da kalaman Trump cewa za ta tattauna da Amurka ranar Asabar game da batun shirinta na nukiliya.
Sai dai kuma gwamnatin Iran ta ce tattaunawar ba za ta kasance ta gaba da gaba ba saɓanin iƙirarin Trump.
Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce za a yi ganawar ne a Oman - tattaunawar da za ta kasance zakaran gwajin dafi.
Tuni Mista Trump ya yi gargaɗin cewa idan tattaunawar ta ranar Asabar ta gagara Iran na cikin haɗari.
Da yake magana daga ofishin shugaban ƙasa, Trump ya ce " muna babban taro da Iran kuma za mu tattauna kai tsaye...kuma akwai yiwuwar cimma matsaya da za ta zama abar yabawa."
Sai dai kuma Trump ɗin ya yi gargaɗin cewa "idan Iran ɗin ta ƙi amincewa da yarjejeniyar to za ta fuskanci haɗari", inda ya ƙara da cewa "ba zai yiwu Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, idan kuma tattaunawar ba ta yi nasara ba, ina tunanin abin ba zai yi wa Iran ɗin kyau ba."
To amma Trump bai bayar da cikakken bayani dangane da tattaunawar ba da su haɗa da cigaban da aka samu ko kuma waɗanne jami'an ne za su kasance a tattaunawar ba.
A makon da ya gabata ne shugaba Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Iran bayan da jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei ya fito fili ya yi watsi da buƙatar Amurka na neman tattaunawa da Iran kai tsaye.
A watan Maris, ne Trump ya aike wa da jagoran addinin na Iran wasiƙa ta hannun wani jakada daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa inda ya bayyana aniyarsa na tattaunawa da Iran ɗin.
Yunƙurin ƙasashen yammaci na daƙile aniyar ƙasar Iran ta ƙera makaman nukiliya na ɗaya daga cikin tsare-tsaren Amurka na ƙasashen Amurka da ƙawayenta a tsawon shekaru.
A 2025 ne dai tsohon shugaban Amurka, Barack Obama ya cimma yarjejeniyar da Iran kan taƙaita samar da makamin nukiliya da kuma bai wa masu sa ido na ƙasa da ƙasa damar shiga ƙasar domin tantance yanayin da makamashin na nukiliya ke ciki - Iran dai ta sha faɗn cewa tana ƙoƙarin samar da makamashin na nukiliya ne domin zaman lafiya.
Ita kuma Iran an sassauta mata takunkuman da aka ƙaƙaba mata da suka raunata mata tattalin arziƙi.
Ƙasashen China da faransa da Jamus da Rasha da Burtaniya duk sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar.
To sai dai a shekarar 2018, Donald Trump ya yi gaban kansa inda ya fice daga yarjejeniyar, wadda ya daɗe yana suka tun ma a lokacin yaƙin gangamin zaɓensa.











