Ko Iran za ta iya kauce wa takunkuman Amurka?

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, Jeremy Howell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Iran ta samu raguwa a yawan man fetur da take fitarwa zuwa kasashen waje sakamakon takunkumai masu tsauri da shugaba Donald Trump da Joe Biden su ka ƙaƙaba mata a cikin watanni kalilan.
Trump ya ce ya na son tattalin arzikinta ya durkushe, domin ya kawo cikas ga shirinta na nukliya.
Wannan dai tsari ne da ya jadada ''matsin lambar'' da ya yi wa kasar a farkon wa'adinsa kan mulki.
Shi da Biden sun sanya takunkumi akan ''jerin jiragen ruwan maso dakon mai'' da ake amfani da su domin fitar da man fetur din kasar zuwa kasashen ketare
Trump ya maida hankali ne a kan '' kamfanonin kasashen waje ''da ake zargin su na taimaka wa Iran a cinikayyar man fetur ta haramtacciyar hanya

Asalin hoton, Getty Images
Mene ne adadin man fetur da Iran ke fitarwa zuwa ƙasashen waje?

Asalin hoton, Getty Images
Iran na cikin jerin kasashen duniya masu arzikin albarkatun man fetur
A farkon shekarar 2024, kasar ta rika fitar da gangar mai miliyan daya da digo takwas a kowace rana a cewar alkaluman kamfanin S&P Global, mai tattara bayanai.
Sai dai S&P Global ya ce takunkuman baya baya nan sun sa yawan man fetur da kasar ke fitarwa zuwa kasashen waje ya ragu zuwa ganga miliyan daya da digo biyu a watan Janairun badi.
Masu sharhi sun yi amanar cewa kashi 90 cikin dari na man fetur din da Iran ke fitarwa ana wucewa da shi zuwa China.
China na sayan man fetur din duk da takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran kan cinikkayar man fetur saboda ba ta amince da takunkuman a matsayin hallataciyya ba.
Dalilan da suka sa aka kakaba wa Iran takunkumai

Asalin hoton, Getty Images
Amurka da wasu kasashe sun kakaba wa Iran takunkumi domin dakile shirin nukliyarta da na makamai masu cin dogon zango.
Manufar takunkumin ita ce ta hana kasar tura kudi ga kungiyoyin irinsu Hamas da Hizbullah da kuma 'Yan Houthi, wadanda Amurka da wasu kasashe suka bayyana a matsayin kungiyoyin 'yan ta'ada.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 2002 aka gano cewa Iran ta na sarafa kayayakin nukliya, abinda yasa Majalisar dinkin duniya da tarayyar turai da Amurka da sauran kasashe suka kakaba mata takunkumi domin hanata inganta shirin nukliyarta.
Sun ce Iran ta saba wa alkawarin da ta yi, lokacin da rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makamin nukliya a 1967 a kan cewa ba za ta taba zama kasa da ta mallaki makamin nukiliya ba
Iran ta ce tana da hakkin tace sinadaran makamin nukiliya.
Ta ce tana son ta yi amfani da shi ne domin inganta wutar lantarki.
Sai dai hukumar da ke sa ido kan nukliya ta duniya ta kasa tabbatar da hakan.

Asalin hoton, Iranian presidential handout / Reuters
A shekarar 2018 shugaba Trump ya janye daga yarjejeniyar, tare da sake kakaba wa Iran takunkumai.
Takunkuman dai masu tsauri ne saboda a 2020 yawan man fetur da kasar ke fitar wa zuwa kasashen waje ya ragu zuwa gangar mai dubu dari hudu a kowace rana.
Sai dai bayan zuwan mutumin daya gaji mulki daga hannunsa watau Joe Biden ya yi wa takunkuman sassauci domin Iran ta koma teburin shawara kan shirin nukliyarta.

Asalin hoton, Iranian presidential website / Reuters
Iran ta ce takunkman da Amurka ta kakaba mata kan man fetur da take fitar wa zuwa kasashen waje kan iya kawo cikas ga kasuwar man fetur ta duniya. Ta yi kira ga mambobin kungiyar kasashe masu arzikin man fetur Opec da su dauki mataki sasauta takunkuman na Amurka.
Waɗanne takunkumai ne aka ƙaƙaba wa Iran?

Asalin hoton, EPA
Amurka ta kakaba wa Iran takunkumi a 1979 bayan da aka kai wa ofishin jakadacinta na Tehran hari tare da yin garkuwa da mutane.
Ta fara kakaba wa shirin nukiliyar gwamnatin kasar takunkumi a 1992

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Amurka ta kuma sanya wa bankunan Iran da babban banki kasar takunkumi. Ta kuma hana cibiyoyin kudi sassan duniya da ke kasuwanci da Iran amfani da dala. Manufar hakan ita ce ta kara maida kasar saniyar ware a harkokin kudi na kasashen duniya.
Yadda takunkumai suka shafi rayuwar Iraniyawa

Asalin hoton, Getty Images
Daga 2012 zuwa 2016 Iran ta yi asarar fiye da dala biliyan160 na kudade shiga a lokacin da Amurka da EU suka sanya mu su takunkumi.
A lokacin da Trump ya fara matsa mata lamba a 2018, tattalin arzikin kasar ya durkushe tare da faduwar darajar kudin kasar watau rial

Asalin hoton, Getty Images
Ta ya ya Iran za ta kauce wa takunkumai?

Asalin hoton, Reuters
'Yan siyasar kasashen yama da kungiyoyi masu adawa da Iran irin su United Against Nuclear Iran sun ce Iran ta na da jerin jiragen ruwa masu dakon man fetur da ke kai mata danyen man zuwa kasashen waje.
Waɗannan jiragen ruwa ne da ake zargi an yi wa rajista a cikin ƙasashe waɗanda ke ba masu mallakar jiragen damar ɓoye bayanansu ko sunnyensu. Har ila yau, an ba da rahoton cewa su kan kashe na'urar da ke bibiyar tafiyar jirgin ruwa a lokacin da suke cikin teku .
Iran ba ta amince da cewa tana amfani da "jiragen ruwan ba " amma ba ta musanta yin hakan ba, kuma kafofin watsa labarai na Iran sun kira jiragen ruwan a matsayin abinda ''zai tayar da hankalin '' wadanda suka kakaba mata takunkumai.







