Yadda Trump da Tinubu ke tafiye-tafiye cikin ayarin motoci

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da a ranar Larabar nan ne shugaban Amurka, Donald Trump ke kai wata ziyarar aiki zuwa Burtaniya a karo na biyu a matsayinsa na shugaban ƙasa, shi ma shugaban Najeriya ya koma ƙasar tasa daga hutun da ya ɗauka wanda ya kamata ya ƙare ranar 19 ga watan Satumbar nan.

Abin lura a nan shi ne irin yadda shugabannin ke gudanar da tafiye-tafiyensu a ayarin motoci masu sulke da jami'an tsaro masu yawa.

BBC ta yi duba dangane da abubuwan da ke cikin ayarin shugabannin guda biyu.

Donald Trump ke tafiya cikin ayari

..

Asalin hoton, Getty Images

A tafiye-tafiyen Donald Trump da yake yi musamma zuwa ƙasashen waje kamar ziyarar tasa zuwa Burtaniya za a kashe miliyoyin daloli da jami'an tsaro na farin kaya da kuma ƴansanda.

An jibge ƴansandan jiha 6,000 a lokacin irin wannan ziyarar da ya kai Burtaniya a 2019 abin da ya laƙume fiye da fam miliyan 3.4.

A wannan lokacin kuma an ƙara tsaurara matakan tsaro ga shugaban ƙasar sakamakon kisan da aka yi wa abokinsa, Charlie Kirk a jami'ar Utah.

Masana harkar tsaro na cewa ana fara shirye-shiryen ziyarar shugaban Amurkar ne makonni da dama kafin a yi ta inda ake tattaunawa da jami'an tsaro kamar ƴansanda da ma mayar da hankali kan ko akwai barazanar tsaro.

Trump ya kai ziyarar ne da rakiyar uwargidansa, Melania Trump, inda suka yi amfani da jirgi samfurin Boeing 747-200B wanda kuma ake kira da Air Force.

..

Asalin hoton, Getty Images

An tsara jirgin ne ta yadda zai bujure wa hare-hare ta hanyar lalata na'urar abokan gaba sannan kuma zai iya sakin makamai masu linzami. An kuma ƙera jirgin ta yadda zai iya shan mai alhali yana tafiya a sama.

Cikin jirgin na da girman ƙafa 4,000 kuma a ciki akwai ɓangaren shugaban ƙasa da asibiti mai ɗauke da gadon yin tiyata da ɗakin ƴanjarida da jami'an tsaro da ma'aikata da ma manyan baƙi.

Da zarar shugaban ya sauka daga jirgi, akwai motoci guda biyu ƙirar Cadillac da ake kira Cardillac One samfurin doguwar mota da ake kira limousine wadda ake yi wa laƙabi da "The Beast" da ke jiran sa.

Motocin biyu masu kama da juna za su kasance a cikin ayarin sauran motocin jami'an tsaro na farin kaya - ana sa su a cikin jirgin kaya domin kai su inda za a je kamar Burtaniya a wannan karo.

..

Asalin hoton, Getty Images

Ita wannan motar tana da sulke a jikinta da gilasan tagoginta abin da ya sa motar take da nauyin ton 20,000. An ce ma tana ɗauke da na'urar da ke harba gurneti da kamarorin gani da daddare da kuma tarho mai amfani da tauraron ɗan'adam.

Sauran abubuwan da motar ke da su sun haɗa da tukunyar iskar oxygen saboda ko da tsautsayi zai faru da firji da ke ɗauke da jini samfurin na shugaban ƙasar ko da za a samu tsautsayi.

Shugaban ƙasar da ke cikin wannan mota na samun rakiyar gomman sauran motici na ƴansanda da jami'an tsaron farin kaya da jami'an kare haɗurra da jami'an lafiya da ƴan jarida, ta yadda da wuya mutum ya iya gane a wace motar shugaban ƙasa ke ciki.

Kasancewar shugaba Trump zai yi tafiye-tafiyen nasa a Burtaniya da jirgin sama to za a yi amfani da jirage masu saukar ungulu da suke yi masa rakiya.

Yadda Shugaba Bola Tinubu ke tafiya cikin ayari

..

Asalin hoton, Getty Images

A duk lokacin da shugaba Tinubu zai yi ziyara musamman a cikin Najeriya to shi ma a kan samu yanayi irin na shugaba Trump - yawan motoci a ayarin shugabannin.

Duk da cewa shugaba Tinubu a baya ya rage yawan motocin da ke ayarinsa da na ministocinsa da sauran jami'an gwamnati amma har yanzu ƴan Najeriya na muhawara dangane da yawan ababan hawan da ke yi masa rakiya.

Kafin zuwan shugaba Tinubu, mota ƙirar Marsandi da ake kira S Class ita ce shugabannin ƙasa da ma gwamnoni ke hawa saboda tsaro.

To sai dai a yanzu haka Cardillac Escalade 2023/2024 mai sulke ita ce motar da shugaban ƙasa ke hawa a hukumance, wadda aka ƙaddamar da ita a yayin ziyarar shugaba Tinubu a ƙasar Equitorial Guinea.

Bayanai sun nuna an sauya motar ne sakamakon ƙaruwar barazanar tsaro da ƙasar ke fuskanta a yanzu.

..

Asalin hoton, TVC/GRAB

Bayanan hoto, Shugaba Tinubu a cikin motarsa lokacin bikin ƴancin kai na 2024

Bayan kasancewarta mai sulke domin tsare lafiyar shugaban ƙasar, motar ta kasance ta alfarma.

Jikin motar da gilasanta duk masu sulke ne inda babu wani harbi ko kuma jifa da zai fasa gilashinta - har ma tashin bam ba zai yi mata illa ba.

An kuma gina motar da na'urorin zamani da za su bayar da damar gano duk wata barazanar tsaro tun ma ba ta faru ba sannan tana da tsarin sadarwa na zamani da ke hana katse ko kuma sauraron tattaunawar shugaban da wani.

Motar tana kasancewa a cikin ayarin gomman motoci da wasu ke cewa wani lokaci sun wuce 100 musamman a lokutan bukukuwan sallah ko kuma lokacin da ya je gida Legas.