Waɗanne yaƙe-yaƙe ne Trump ya kawo ƙarshensu?

Shugaban Amurka Donald Trump a tsaye a bayan dandamalin da ke ɗauke da hatimin fadar White House da kuma wani ƙyalle a bayansa da aka rubuta kalaman "neman zaman lafiya".
    • Marubuci, Jake Horton & Nick Beake
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
  • Lokacin karatu: Minti 7

A yayin da shugaba Donald Trump ke ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine, ya ci gaba da irin rawar da ya taka a tattaunawar zaman lafiya tun bayan fara wa'adinsa na biyu kan karagar mulki.

Da yake magana a fadar White House a ranar 18 ga watan Agusta, inda shugabannin Turai suka matsa masa lamba kan ya yi ƙoƙarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, ya yi iƙirarin cewa: "Na kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe guda shida… dukkan waɗannan yarjejeniyoyin da na kulla an cimma su ne ba tare da an ambaci kalmar 'tsagaita wuta ba'."

Washegari adadin da ya ambata ya ƙaru zuwa "yaƙe-yaƙe bakwai".

Gwamnatin Trump ta ce shugaban ya cancanci lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel inda ta bayyana shi a matsayin "shugaban zaman lafiya", kuma ta lissafa "yaƙe-yaƙen" da ake iƙirarin ya kawo ƙarshen su.

A wasu an tsagaita wuta na ƴan kwanaki ne kawai - ko da yake sun kasance sakamakon tashe-tashen hankula da aka ɗaɗe ana yi - kuma babu tabbas ko wasu daga cikin yarjejeniyoyin za su ɗore.

Trump ya kuma yi amfani da kalmar "tsagaita wuta" sau da dama lokacin da yake magana a kansu a shafukansa na sada zumunta.

Sashen tantance gaskiya na BBC Verify ya yi nazari sosai kan waɗannan rikice-rikicen da kuma ko wane irin rawa shugaban ya taka domin kawo ƙarshen su.

Isra'ila da Iran

Rikicin na kwana 12 ya fara ne bayan Isra'ila ta kai wasu hare-hare kan Iran a ranar 13 ga watan Yuni.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Trump ya tabbatar da cewa Firaministan Isra'ila Benjamin Natanyahu ya sanar da shi gabannin ƙaddamar da hare-hare.

Amurka ta kuma ƙaddamar da hare-hare kan wasu cibiyoyin sarrafa makamashin nukiliya na Iran - lamarin da ake ganin ya taimaka wurin hanzarta kawo ƙarshen rikicin.

A ranar 23 ga watan Yuni Trump ya wallafa a kafafen sada zumunta cewa: "A hukumance, Iran za ta fara TSAGAITA WUTA, kuma bayan sa'a 12, ita ma Isra'ila za ta TSAGAITA WUTA, kuma bayan sa'a 24, duniya za ta yi maraba da kawo ƙarshen yaƙin na kwanaki 12."

Bayan dakatar da yaƙin, jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya dage kan cewa ƙasarsa ta samu ''gagarumar nasara'' amma bai furta kalmar tsagaita wuta ba.

Isra'ila ta yi nuni da cewa za ta iya sake kai hari kan Iran domin daƙile sabbin barazanar da za su iya ɓullowa daga ƙasar.

Michael O'Hanlon, wani babban jami'i a cibiyar bincike ta Brookings ya ce "Babu wata yarjejeniya kan samar da zaman lafiya na dindindin ko kuma yadda za a sa ido kan shirin nukiliyar Iran a gaba."

"Don haka abin da aka cimma shi ne ƙwarya-ƙwaryar tsagaita wuta wadda ba ta tabbatar da kawo ƙarshen yaƙin ba, amma zan ɗan yaba masa, saboda raunin da Isra'ila ta yi wa Iran- tare da taimakon Amurka - yana da matukar muhimmanci."

Ma'aikata a Iran na aiki a cikin ɓaraguzan ginin da Isra'ila ta kai wa hari a Tehran, a ranar 16 ga Agusta, 2025.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, An yi musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila a rikicin da aka yi na kwana 12.

Pakistan da India

An shafe shekaru ana takun saƙa tsakanin waɗannan ƙasashen biyu masu makaman nukiliya, amma a watan Mayun da ya gabata ne rikici ya ɓarke bayan wani hari da aka kai a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya.

Bayan kwashe kwana huɗu ana musayar wuta, Trump ya wallafa cewa Indiya da Pakistan sun amince da "CIKAKKEN tsagaita wuta nan take".

Ya ce hakan ya samo asali ne sakamakon doguwar tattaunawar da aka yi wadda Amurka ta shiga tsakani.

Pakistan ta gode wa Trump sannan daga baya ta miƙa sunansa a matsayin wanda ya cancanci lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, inda ta yi nuni da abin da ta kira "ƙwarewarsa a shiga tsakani na diflomasiyya".

Indiya, dai ta kwarara ruwan sanyi a kan rawar da Amurka ta taka: "Tattaunawar da ta shafi dakatar da ayyukan soji an yi ne kai tsaye tsakanin Indiya da Pakistan ta hanyar amfani da kafofin da aka riga aka tsara tsakanin rundunonin sojin ƙasashen biyu," in ji sakataren harkokin wajen Indiya Vikram Misri.

Rwanda da Jamhuriyar Dimokuraɗiyar Kongo

Rikicin da aka daɗe ana gwabzawa tsakanin waɗannan ƙasashen biyu ya ɓarke ne bayan da ƙungiyar ƴan tawayen M23 ta ƙwace wani yanki mai arzikin ma'adinai a gabashin DR Congo a farkon wannan shekarar.

A watan Yuni, ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Washington da nufin kawo ƙarshen rikice-rikicen da aka shafe shekaru da dama ana yi. Trump ya ce hakan zai taimaka wajen haɓaka kasuwanci tsakanin su da Amurka.

Takardar yarjejeniyar ta buƙaci "a mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta" da aka ƙulla tsakanin Rwanda da DRC a watan Agustan 2024.

Ƴan tawayen M23 sanye da kayan sojoji na gadin wani ɓangare na jami'an ƴan sandan Kongo da suka miƙa wuya waɗanda za a ɗauka aiki a cikin ƙungiyar ƴan tawayen a ranar 22 ga Fabrairu, 2025 a yankin Bukavu, a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Ana alaƙanta ƴan tawayen M23 da gwamnatin ƙasar Rwanda

Tun bayan cimma yarjejeniyar na baya bayan nan, ɓangarorin biyu sun zargi juna da keta sharuɗɗan yarjejeniyar kuma ƴan tawayen M23 - wanda Burtaniya da Amurka suka alaƙanta da gwamnatin Rwanda sun yi barazanar janyewa daga tattaunawar.

Har yanzu ana rikici tsakanin Congo da Rwanda - saboda haka wannan tsagaita wutan ba ta ɗore ba,'' in ji Margret MacMillan, farfesa a sashen tarihi wadda ke koyarwa a jam'iar Oxford.

Thailand da Cambodia

A ranar 26 ga Yuli, Trump ya wallafa a dandalin sada zumunta na 'Truth' cewa: "Ina kiran muƙaddashin Firaministan Thailand, a yanzu, domin in buƙaci a tsagaita wuta, a kuma kawo ƙarshen yaƙin, wanda a halin yanzu ake ci gaba da gwabzawa."

Bayan wasu ƴan kwanaki, ƙasashen biyu sun amince da "tsagaita wuta ba tare da wani sharaɗi ba" bayan kusan mako guda ana gwabza faɗa a kan iyakar da ke tsakanin ƙasashen.

Malaysia ce ta gudanar da tattaunawar zaman lafiyar, amma shugaba Trump ya yi barazanar dakatar da tattaunawa kan rage harajin da Amurka ta ƙaƙaba wa ƙasashen muddin Thailand da Cambodia ba su daidaita tsakaninsu ba.

Tattalin arzikin ƙasashen biyu dai ya dogara ne kan fitar da kayayyki zuwa Amurka.

A ranar 7 ga watan Agusta, Thailand da Cambodia sun cimma yarjejeniya da nufin rage tashin hankali a kan iyakar ƙasashensu.

Armenia and Azerbaijan

Shugabannin kasashen biyu sun ce kamata ya yi a bai wa Trump lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, saboda ƙoƙarin da ya yi wajen tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya, wadda aka sanar a fadar White House ranar 8 ga watan Agusta.

"Ina ganin ya samu babban yabo a nan - bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ofishin Oval na iya ɗora bangarorin biyu kan hanyar tabbatar da zaman lafiya," in ji Mista O'Hanlon.

A watan Maris, gwamnatocin biyu sun ce a shirye suke su kawo ƙarshen rikicin da suka shafe kusan shekara 40 suna yi, wanda ya shafi matsayin yankin Nagorno-Karabakh.

Riciki mafi muni da ya ɓarke a baya-bayan nan shi ne a cikin Satumba 2023 lokacin da Azerbaijan ta ƙwace yankin (inda yawancin ƙabilun Armeniyawa ke zaune).

Shugaban Amurka Donald Trump ya gana da shugaban Azabaijan Ilham Aliyev da firaministan Armeniya Nikol Pashinyan yayin bikin sanya hannu a dakin cin abinci na fadar White House ranar 8 ga watan Agusta, 2025 a birnin Washington, DC.

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, A watan Augusta Trump ya karɓi bakuncin Shugaban Azerbaijani da Firaministan Armenia a fadar White House

Masar da Habasha

Babu wani ''yaƙi'' a nan da shugaba Trump zai dakatar amma an daɗe ana takun saƙa kan madatsar ruwa da ke kan kogin Nilu.

An kammala ginin babbar madatsar ruwan ƙasar Habasha a wannan bazara inda Masar ta ce za ta iya shafar ruwan da ta ke samu daga kogin Nilu.

Bayan shafe shekara 12 ana samun rashin jituwa, a ranar 29 ga watan Yuni ministan harkokin wajen Masar ya bayyana cewa tattaunawar da ake yi da Habasha ta tsaya cak.

Trump ya ce: "Idan ni ne Masar, ni ma zan so ruwan da ke cikin kogin Nilu." Ya yi alƙawarin cewa Amurka za ta magance matsalar cikin gaggawa.

Masar ta yi maraba da kalaman na Trump, amma jami'an Habasha sun ce akwai haɗarin kalaman za su iya tayar da zaune tsaye.

Babu wata yarjejeniya da aka cimma a hukumance tsakanin Masar da Habasha domin warware saɓanin da ke tsakaninsu.

Serbia da Kosovo

A ranar 27 ga watan Yuni, Trump ya yi iƙirarin hana ɓarkewar rikici a tsakaninsu, yana mai cewa: "Serbia, Kosovo sun shirya bai wa hammata iska, kuma da zai iya zama ƙazamin yaƙi, na ce idan har kuka yi faɗa, hakan zai kawo ƙarshen kasuwancinku da Amurka . Suka ce, to, da alamar ba za mu yi rikicin ba."

Ƙasashen biyu sun daɗe suna yi wa juna gani-gani - lamarin da ya samo asali daga yaƙin Balkan na shekarun 1990 - kuma takun saƙa ya ƙara ta'azzara a cikin ƴan shekarun nan.

"Serbia da Kosovo ba su yi fito-na-fito ko artabu da juna ba, don haka ba yaƙi ne da za a kawo ƙarshensa ba," in ji Farfesa MacMillan.

Fadar White House ta yi nuni da ƙoƙarin diflomasiyyar da Trump ya yi a wa'adinsa na farko.

Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin daidaita tattalin arziki a Ofishin shugaban na Amurka a shekarar 2020, amma babu wani yaƙi a tsakaninsu a lokacin.

The BBC Verify banner.