Mece ce lambar TIN, kuma wane ne ke buƙatar ta?

Asalin hoton, FIRS
A baya-bayan nan an samu ruɗani dangane da sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar ta wajabcin mallakar lambobin TIN ga ƴan ƙasa domin samun damar amfani da asusunsu na bankunan a nan gaba.
Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan gyaran fuska ga sha'anin kuɗi da haraji na Najeriya, Taiwo Oyedele ne ya sanar da hakan da farko to amma daga baya sai ya fayyace abin da yake nufi bayan al'amarin ya tayar da ƙura.
"Wajabcin mallakar wannan lambar ta taƙaitu ne ga mutane da kamfanonin da ya kamata su biya haraji - ba ta shafi ƴan Najeriyar da abin da suke samu bai kai a cire musu haraji daga ciki ba," in ji Oyedele.
Shin mece ve ita wannan lambar? Kuma yaya ake samun ta? BBC ta yi nazari kamar haka:
Mece ce lambar TIN?
Shafin intanet na hukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS ya bayyana ma'anar lambar TIN kamar haka:
"Lambar TIN wasu lambobi ne guda 13 da hukumar ta FIRS ko hukumomin karɓar haraji na jihohi suke bayarwa ga keɓaɓɓun masu biyan haraji domin tantance dalilin biyan harajin nasu. Kowane mai biyan haraji yana da lambar guda ɗaya," in ji shafin FIRS.
Dangane da kuma wanda ya kamata ya mallaki wannan lamba, shafin ya ce duk wani mutum da ke samun kuɗaɗen shiga a Najeriya - ko dai ta hanyar aiki ko kasuwanci ko sanya hannun jari da sauran su dole ne ya mallaki wannan keɓaɓɓiyar lambar ta TIN.
Lambar na taimaka wa hukumomin karɓar haraji bin diddigin masu biyan haraji a tsawon shekaru.
Yaya ake samun lambar TIN?
Shafin hukumar ta tattara harajin ta Najeriya, FIRS, ya zayyana wasu hanyoyi da ya kamata mutanen da suka cancanci wannan lamba su bi domin samun tasu.
- Ta hanyar yin rijista a intanet a shafin Join Tax Board (JTB) TIN.
- Ko kuma mutum zai iya ziyartar ofishin FIRS ko hukumar tattara haraji ta jiharsa mafi kusa da shi.
- Ko kuma ta hanyar ejan da ke tattara haraji wanda aka tantance kuma aka amince ya yi hakan.
Abubuwan da ake buƙata domin rijista
Shafin FIRS ya nuna wasu abubuwa guda huɗu da ake buƙata domin yin wannan rijista kamar haka:
- Takardar haihuwa ta gaskiya
- Lambar asususn banki ta BVN
- Tsohuwar lambar TIN (amma ga wanda yake da ita a baya)
Gaske ne sai da TIN mutum zai hulɗa da bankuna?
Tun bayan buƙatar da gwamnati ta fito da ita kan mallakar lambar ta TIN, aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa nan gaba idan mutum ba shi da lambar ta TIN to ba zai iya cire ko saka kuɗi a asusunsa na banki ba, al'amarin da ya tayarwa ƴan ƙasar musamman masu ƙaramin ƙarfi hankali.
To sai dai hukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS ta ce babu ƙanshin gaskiya a labari.
"A baya-bayan nan an samu mahawara dangane da lambar TIN a Najeriya, inda aka rinƙa yaɗa labarin ƙanzon kurege cewa wai idan ba ka da TIN ba za ka iya cire ko kuma zuba kuɗi a asusunka na banki ba.....Ba haka labarin yake ba. TIN an keɓe ta ne ga masu samun da suke biyan haraji." A martanin Arabinrin Aderonke Atoyebi, mai magana da yawun shugaban hukumar, Zacch Adedeji.
Dalilin gwamnati kan TIN
Kwamitin shugaban Najeriya na gyaran fuska da sauye-sauye kan kuɗi da haraji, ya ce dole ne ƴan ƙasar da suka isa biyan haraji su mallaki lambar ta TIN.
Shugaban kwamitin ya ce hakan ya zama dole a ƙoƙarin da suke yi na ganin duk wanda ya kamata ya biya haraji ya biya kuma ya shiga lalitar gwamnati.
Ita dai lambar ta TIN ita ce kamar wata hanyar gano adadin abin da mutum ko kamfani yake samu a shekara sannan kuma ta taimaka wajen tantance kason da ya kamata mutumin ko kuma kamfanin ya biya haraji a shekara.
A watan Janairun 2026 ne dai dokar haraji da aka yi wa gyaran fuska kuma shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sakawa hannu za ta fara aiki.
Kuma hakan na nufin hukumomi sun fara dasa ɗanba na ganin tsarin karɓar haraji bai samu tasgaro, ciki har da tabbatar da cewa an gano yawan mutanen da suka cancanci biyan harajin.











