Me dokar sa ido kan wa'azin malamai a jihar Neja ta ƙunsa?

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Batun sa idon gwamnati a kan wa'azin da malamai ke yi na ci gaba da janyo cece-kuce a Najeriya.

Ana samun ra'ayoyi masu cin karo da juna daga malamai da kuma al'umomin ƙasar, kan dacewar sanya bakin gwamnati a kan harkokin wa'azi ko kuma 'a'a.

Wata hira da gwamnan jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar, Mohammed Umaru Bago ya yi da wani gidan talbijin na TVC a ranar Lahadi a ƙasar, ta tayar da sabuwar ƙura.

Gwamna Bago ya ce "Duk wanda zai yi huɗuba a ranar juma'a , dole ya miƙa takardun huɗubarsa don a duba.. don ka samu damar zama malamin addinin Kirista ba zai yiwu ka je ka yi ta wa'azin nuna kyama tsakanin al'umma ko a kan gwamnati ba, kuma kana ganin hakan ba wani abu ba ne"

Gwamna Bago ya yi ƙarin haske da cewa gwamnatin na yin hakan ne domin magance matsalar lalata tunanin al'umma, lamarin da ya danganta da matsalar tsaro a jihar.

Abin da ya sa muka waiwayi dokar wa'azi

Shugaban ma'aikatar kula da al'amuran addini na jihar Neja, Umar Faruk Abdullahi ya ce manufar gwamnati ita ce tsaftace yadda ake wa'azi a jihar.

Haka kuma hukumar na aiki ne da dokar wa'azi wadda aka kafa a shekarar 1983 kuma ba a share ta ba, amma ba a aiki da ita ne.

Sai dai a yanzu yin la'akari da yawaitar ƙararrakin da take fuskanta kan malamai yasa suka yanke shawarar tattara bayanan masu wa'azi a jihar. Kuma suna fatan fitar da takardun a ƙarshen watan Satumba domin samun bayanan malamai a jihar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Idan aka bar komai a sake dole a samu matsala. Harkar addini kuma abu ne da sai anyi hattara ciki sosai. A Najeriya, musamman a arewacin ƙasar akwai matsalolin tsaro ba iyaka. Kuma yadda wasu masu wa'azi ke tafiyar da wa'azi akwai tsoro matuƙa. " In ji Umar Faruk Abdullahi.

"Boko Haram ta faro ne ta wa'azi, su ISIS ɗin nan duka ta wa'azi ne. Boko Haram basu ƙare ba, amma rayuka nawa suka salwantar. A lokacin da ace gwamnatin Borno ta sa ido a lokacin da Muhammad Yusuf ke wa'azi kamar yadda muaka sanya ido a nan yanzu da haka bata faru ba." Inji Umar

Ya kuma bayar da misalai da cewa kamar a Makka da Madina da wasu ƙasashe kamar Masar da Sudan cewa malamai basa wa'azi ko karantarwa sai idan gwamnati ta san da kai. Amma a Najeriya lamarin ba haka yake ba, kuma shi ke haifar da faɗace-faɗace a tsakanin malaman a wurin wa'azi.

Shugaban ma'aikatar ya ƙara da cewa sai da suka zauna da shugabannin ƙungiyoyin malaman jihar kafin su ɗauki matakin sanya ido kan wa'azin. Yana mai watsi da zargin da wasu ke yi na cewa gwamnati ta sanya siyasa cikin lamarin.

Martanin Malaman Neja

Ahmed Ibrahim Khalil wanda aka fi sani da Malam Bala, shi ne shugana cibiyar nazarin kimiyya da fasaha a addinance da ke jihar Neja, kuma ya yi watsi da matakin gwamnatin, yana mai cewa zuwan dimokradiyya ya rusa dokar wa'azin.

Ya danganta matakin gwamnatin da siyasa " su suka yi amfani da malamai suka kawo kansu, kuma za suce wasu ba za su yi amfani da malamai ba. Kuma abin da ke basu tsoro shi ne ba jihar Neja ba, gaba ɗaya Najeriya sun gane cewa malamai sun fi 'yan siyasa tasiri."

Malam Bala na ganin cewa ba ta hanyar wa'azi ake gurɓata ko sauya tunanin al'umma ba, don haka kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali kan makarantun ƙungiyoyin addinai, indan tana so ta inganta batun tsaro a jihar, domin a can ne ake gurɓata tunanin mutane.

Ya kuma bayyana cewa ko sun ƙi ko sun so a dimokradiyya ba a hana wani faɗar ra'ayinsa ba. Kum dokar Najeriya ta bayar da zamar zuwa kotu ga duk wanda ya ga cewa an ci mutunsa.

A cewarsa ƙasashe kamar Saudiyya ƙasar musulunci ce, suna horar da malamai kuma suna basu albashi. Sai dai batun ba haka yake ba a Najeriya.

A nasa ɓangaren Reberan Dokta MS Dada tsohon shugaban ƙungiyar addinin kirista ta CAN, a jihar Neja kuma tsohon mataimakin shugaban ƙungiyar na jihohi 19 da ke arewacin Najeriya da kuma Abuja, ya ce matakin ya dogara da waɗanda za su aiwatar da dokar.

"In dai za a yi shi a kan gaskiya cewa baƙin da suka zo zasu yi wa'azi, a san daga ina suka zo, wannan ba laifi ba ne. Amma kamar waɗanda an sansu suna nan tare da mu shekara da shekaru ba dole ba ne ace sai sun nemi izini kafin su yi wa'azi.

Ya ce batun sanya ido kan wa'azi ba sabon abu bane a jihar, kuma lamarin matsalar tsaro ce ta sake taso da shi. Sannan a ganinsa gwamnan ba mutum ba ne da zai karkata kan batun da ya shafi addini.

Me kundin tsarin mulki ya ce?

To ko me kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce kan sanya ido kan ayyukan wa'azin malamai, Barista Sulaiman Magashi, wani lauya mai zaman kansa a birnin Kano.

Ya taɓa shaida wa BBC cewa "Abu ne mai yiwuwa kuma mai fa'ida a ɗauki matakin tsara yadda ya kamata a gudanar da wa'azi domin shi ma fanni ne na wata sana'a wadda shari'ar addinin Musulunci da tsarin ƙasar suka amince a kyautata su."

Tsarin mulkin Najeriya ƙarƙashin sashe na huɗu na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da ƴancin gudanar da addinin da mutum yake so ciki kuma har da wa'azi wato kira ga addinin da yaɗa shi.

To sai dai kuma wannan ba yana nufin a yi wa'azin ta-ci-barkatai ba ko kuma yadda zai saɓa da tsarin zamantakewar jama'a kamar cin mutumcin wani ko kuma tayar da tarzoma. Saboda haka akwai buƙatar a yi dokokin kyautata wa'azi abu ne da ya dace a yanzu haka." In ji barista Sulaiman Magashi.

Sai dai ya bayyana buƙatar sanya masu-ruwa da tsaki a cikin al'amarin.

Jihar Neja dai ba ita ce jiha ta farko ba da ke ɗaukar irin wannan mataki na sanya ido kan ayyukan wa'azi, ko a baya ma majalisar dokokin jihar Kaduna da ke makwaftaka da Neja, ta taɓa amincewa da wani ƙudurin doka mai kamar haka, sai ba a kai ga zartarwa ba.

A watan Fabrairun 2025 ne Majalisar Ƙoli kan harkokin Shari'ar Musulunci ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin, Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III, ta nemi a samar da dokokin da zasu tantance masu wa'azi.