Amfanin dawa ga lafiyar ɗan'adam

Asalin hoton, Getty Images
Dawa na daya daga cikin hatsi mafiya muhimmanci da ake nomawa a Najeriya, musamman a arewacin kasar.
Masana kiwon lafiya sun ce dawa na dauke da sinadaran gina jiki masu amfani ga jikin dan adam.
Dawa na ɗauke da sinadaran furotin da iron da magnesium da phosphorus da potassium da bitamin B, waɗanda ke taimakawa wajen gina jiki da kara karfin ƙashi da lafiyar jini, kamar yadda ƙwararriya a fannin abinci Habiba Haruna ta shaida wa BBC Hausa.
Ta kuma ce dawa na ɗauke da sinadarin fiber da ke sauƙaƙa narkewar abinci da kare hanji da sauran sinadaran da ke da matuƙar muhimmanci ga lafiyar kowane mutum, musamman yara da mata masu juna biyu da kuma tsofaffi.
Ga wasu muhimman amfanin dawa ga lafiyar dan adam da kuma hanyoyin da ake sarrafa ta;
Ƙara ƙarfin jiki da kuzari
Habiba ta ce saboda sinadaran furotin da bitamin B da ke cikin dawa, ta na ba jiki kuzari mai dorewa.
"Idan ka ci abinci mai dauke da dawa, ka fi samun kuzari na dogon lokaci ba tare da jin yunwa cikin sauri ba."
Wannan ne ya sa ya fi dacewa ga masu aikin gona da 'yan ƙwadago, da yara masu zuwa makaranta.
Taimaka wa lafiyar zuciya
Masana sun gano cewa cin dawa na rage haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya saboda yawan fiber da ke cikinsa. Fiber na taimakawa wajen rage kitse a jini, wanda ke hana toshewar jijiyoyin zuciya.

Asalin hoton, Getty Images
Kariya daga ciwon jini (Anaemia)
Dawa na ɗauke da sinadarin iron, wanda ke taimaka wa jiki wajen samar da jini mai kyau in ji ƙwararriyar.
"Mata masu juna biyu na iya amfana sosai daga cin abinci da aka yi da dawa, saboda yana taimakawa wajen hana matsalar rashin jini."
Ƙarfafa ƙashi da haƙora
Sinadarin magnesium da phosphorus da ke cikin dawa na taimaka wajen ƙarfafa ƙashi da haƙora. Wannan ne ya sa yake da amfani ga yara da ke tasowa da kuma tsofaffi da ke fuskantar raunin ƙashi.
Inganta garkuwar jiki
Ƙwararriyar ta ƙara ce cewa sinadaran bitamin da ke cikin dawa suna ƙara ƙarfin garkuwar jiki, suna taimakawa wajen kare mutum daga kamuwa da cututtuka.
Daidaita narkewar abinci
Saboda yawan sinadarin fiber, dawa na taimaka wa hanji wajen aiki yadda ya kamata. Yana sauƙaƙa narkewar abinci domin yin bayan gida cikin sauƙi da rage kumburin ciki.
Ba shi da sinadarin gluten
Wani muhimmin amfanin dawa shi ne cewa ba shi da sinadarin gluten wanda ke taɓa hanji. Don haka, ya dace da mutanen da ke da matsalar rashin jure gluten, musamman masu fama da cutar celiac, in ji ƙwararriyar.
Rage haɗarin ciwon suga (Diabetes)
Saboda yawan sinadaran da take da su, dawa na sa jini ya rika karɓar sukari a hankali. Wannan na taimaka wa masu fama da ciwon suga wajen sarrafa yadda jinin su ke ɗaukar glucose.
Amfanin dawa wajen sarrafa abinci daban-daban

Asalin hoton, Getty Images
Habiba ta ce dawa na daga cikin hatsi da ake iya sarrafawa ta hanyoyi daban-daban bisa ga abinci ko abin sha da ake son yi. Sun haɗa da
- Niƙa: Ana niƙa dawa domin a samar da garin tuwo, wanda ake yin tuwo dawa da shi.
- Tsamiya/fermentation: Ana jika dawa a ruwa a bar shi ya yi tsami, daga nan ake amfani da shi wajen yin fura ko kunun dawa da wasu abin sha na gargajiya.
- Shinkafar dawa: Wasu na sarrafa shi ta hanyar dafawa kamar shinkafa, ana ci kai tsaye da miya.
- Fulawar dawa: A kasuwannin zamani, ana tace dawa zuwa fulawa ko a shirya ta a gwangwani domin sauƙin amfani.
Habiba Haruna ta ce; "Al'ummar Hausa sun dade suna cin amfanin dawa wajen girke-girke na gargajiya kamar tuwo da fura da kunun dawa. Wannan ya kara masa daraja a al'adu da rayuwar yau da kullum."
Dawa ba wai kawai abinci ba ne na gargajiya, amma abinci ne mai cike da sinadaran gina jiki da ke kare jiki daga cututtuka da kuma ƙara ƙarfin lafiya.
Masana sun yi nuni da cewa ya kamata a ƙara amfani da dawa a cikin abincin yau da kullum, ba wai kawai a matsayin tuwo ko fura ba, har ma a matsayin madadin abinci na zamani.











