Amfanin kankana ga lafiyar ɗan'adam

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Amfanin kankana ga lafiyar ɗan'adam

Kankana na ɗaya daga cikin kayan gona na marmari da ke da matukar amfani ga ɗan Adam, in ji likitoci.

A wannan bidiyon na sama, Dakta Jawahira Muhammad ta Asibitin Murtala da ke Kano ta bayyana sinadaran da kankana take ɗauke da su.

"Akwai sinadarin da ke taimakawa wajen saukar da kumburi a jikin ɗan'adam, sannan tana ƙunshe da sinadaran vitamin A, C, B1, B6," in ji ta.