Abubuwa 8 da ke hana wasu mata gamsuwa lokacin kwanciyar aure

Asalin hoton, ISTOCK
Samun gamsuwa lokacin kwanciyar aure ga mata abu ne mai wahalar fahimta, hatta a tsakanin likitoci da kuma masana kan al'adar kwanciyar aure.
Akwai jan aiki wajen fahimtar lamarin, kasancewar mata da yawa ba sa samun gamsuwa, wasu ma sun ce ba su taɓa samun irin wannan gamsuwa ba a rayuwarsu.
Akwai abubuwa da dama da ke sanyawa mata su samu gamsuwa a lokacin saduwa, waɗanda suka haɗa da abin da mutum ke tunani, da abubuwan da ke faruwa a zahiri da kuma tasirin sanadaran jikin ɗan'adam.
BBC ta duba wasu abubuwa bakwai da ke hana mata gamsuwa ko kawowa a lokacin kwanciyar aure.
1. Abubuwa marasa kyau da suka faru a baya
Idan mace ta taɓa shiga wani tashin hankali da ya jiɓanci kwanciyar aure a baya, zai iya zama babbar matsala, saboda haka zai yi kyau ga mace idan ta taɓa shiga irin wannan halai ta bayyana wa mijinta domin sanin yadda zai taimaka mata.
Duk da cewa zai iya zama abu mai wahala mutum ya tattauna da wani, amma akwai buƙatar hakan domin za a iya samun taimakon da zai samar da mafita.
Haka nan wani muhimmin abu shi ne mace za ta iya tattaunawa da masana domin samun taimako.
"A irin wannan lokaci abin yana da wahala sosai, saboda suna cikin damuwa ne idan suka tuna abin da ya faru, kuma wata ƙila tattauna abin da ya farun zai iya janyo ƙyama," in ji Dr Hector Galvan, shugaban cibiyar nazarin tunanin ɗan'adam da kuma harkar saduwa ta Madrid.
2. Gajiya

Asalin hoton, ISTOCK
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da cewa Dr Galvan ya samu matan da suka je wurin shi domin samun shawarwari kan damuwar da suke da ita kan rashin samun gamsuwa a lokacin saduwa sanadiyyar rashin iya yin rayuwa kamar kowa, a sanadin tasowa daga gidan da ake tsaurara tarbiyya, ya ce amma irin wadannan mata ƙalilan ne.
Sai dai ɗaya daga cikin abubuwan da ya lura daga irin wadannan mata da ke zuwa wajen shi shi ne rashin samun gamsuwa sanadiyyar gajiya.
"Kafin mutum ya samu gamsuwa a lokacin saduwa jikinsa na buƙatar sakewa da hutu," in ji likitan.
"Jiki zai iya samun jin daɗi (matakin da ake kaiwa kafin kawowa a lokacin saduwa) ko da mutum na fama da gajiya, to amma kafin jikin ya kai matakin kawowa yana buƙatar ya saki sosai," in ji likitan.
Ɗaya daga cikin abin da ke kawo cikas a wannan yanayi shi ne gajiyar da ke taruwa a jikin ɗan'adam sanadiyyar kwashe sa'o'i ana aiki domin kammala wasu ayyukan ko kuma zirga-zirga daga gida zuwa wurin aiki, sai kuma ɗawainiya da yara.
A irin wannan yanayi wasu matan kan yi ƙaryar samun gamsuwa domin guje wa kwashe tsawon lokaci ana saduwa.
Sai dai masana tunanin ɗan'adam na bayar da shawarar kauce wa irin haka, a madadin haka ya kamata mace ta tattauna da mijinta domin fahimtar juna da kuma neman mafita.
3. Yin shuru
Za mu iya cewa: A batun kwanciyar aure babu yadda za a yi ka san yadda wanda/wadda kake tarayya da shi/ita ke ji.
Tabbas, za ka iya kwatanta yadda mutum ke ji ta hanyar sauraren muryarsa ko motsin jiki, amma hanya mafi inganci ta tabbatar da abin da kake tunani shi ne ta hanyar magana.
"Mutane da dama na jin nauyin faɗa wa abokan zamansu cewa su sauya yadda suke kwanciyar aure da su," in ji masanin.
Amma masana na ganin cewa idan dai ana son samun mafita, to abin da ya fi kyau shi ne ma'aurata su riƙa tattauna irin waɗannan matsaloli.
"Ya kamata su sani cewa abokan tarayyar tasu ba su iya takamaiman abin da ɗayansu ke bukata domin samun gamsuwa," sai dai idan ɗaya ya fada wa ɗayan.

Asalin hoton, ISTOCK
4. Rashin iya wasa
Dr. Kangwan ya ce a shekarun baya-bayan nan ya fahimci cewa ana samun ci gaba tsakanin ma'aurata game da yadda suke yin wasa sosai kafin kwanciyar aure.
"A gomman shekaru da suka wuce ba a samun wannan daidaito tsakanin mace da namiji. Maza kan samu gamsuwa cikin sauri. To amma yanzu abubuwa na gyaruwa."
Sai dai matsalar ita ce ba kawai tsawon lokacin da aka kwashe ne ke da muhimmanci ba, sanin abin da ya kamata a yi shi ne abin.
Yana da kyau mace ta sanar da mijinta takamaiman abin da take so ya riƙa yi da kuma yadda zai yi da kuma inda zai rika taɓawa.
"Sau da yawa matan kan faɗa mana cewa maza ba su san yadda za su yi wasa da su ba ko kuma ma suna cutar da su, amma suna jin tsoron faɗa wa mazan nasu saboda kada su ɓata musu rai ko kuma saboda suna jin kunya."
5. Rashin sha'awa
Hukumar Lafiya ta Birtaniya ta ce mata kan yi fama da matsalar rashin sha'awa a mataki daban-daban na rayuwarsu.
Misali, sha'awa na iya ƙaurace wa mace a lokacin da take da juna-biyu, ko bayan haihuwa ko kuma a lokacin da ta daina jinin al'ada.
Tsananin damuwa, firgici, amfani da wani magani ko kuma sauyi a sanadaran da jiki ke fitarwa duk za su iya shafar yadda mace ke jin sha'awa da kuma samun gamsuwa a lokacin kwanciyar aure.
Hukumar ta ce sha'awar mace kan ragu idan sinadarin testosterone da jikinta ke saki ya ragu. Hakan na faruwa ne idan aka samu naƙasu a yadda wajen samar da ƙwan halitta ko kuma ƙundun da ke samar da sanadarai da ke kan ƙoda suka samu matsala.
Idan har aka samu irin wannan matsala to ya kamata ta ga likita, domin zai iya ba ta shawarwari kan yadda za a samu mafita.

Asalin hoton, iStock
6. Ɗora ɗawainiya fiye da kima
Masana harkar kwanciyar aure sun ce a lokacin da cibiyar nazari kan tunani da saduwa ta yi nazari kan wasu mutanen da suka zo da ƙorafi, an gano cewa wasu mutanen na da ɗabi'ar nuna cewa dole sai an yi abin da suke so, ko tursasawa ko kuma son dole a yi abu a yadda suke ganin shi ne daidai.
Saboda haka nan sakin jiki da kuma samun hutu abu ne mai muhimmanci.
7. Zafi lokacin kwanciya
A harkar lafiyar mata, akwai abubuwa da dama da ke hana mace samun gamsuwa a zaman auratayya.
Ɗaya daga cikin wannan shi ne abin da ake kira 'vaginismus', wato matsewar tsokar da ke cikin al'aurar mace, wanda hakan ke sanyawa mace ta riƙa jin zafi a lokacin kwanciyar aure, a wani lokacin ma za ta ji ba ta son kwanciyar, kamar yadda hukumar lafiya ta Birtaniya ta bayyana.
"Irin haka na faruwa ne idan mace tana kallon kwanciyar aure a matsayin wani mummunan abu ko kuma idan ta samu ciwo a lokacin haihuwa ko kuma tiyata."
Dr Galvan ya ce idan har aka samu irin wannan yanayi "inda ƙwaƙwalwa ke ɗaukar kwanciyar aure a matsayin azaba, hakan na shafar sha'awar mace kuma yakan sa ta guji duk wata mu'amala ta aure."
Yana da kyau idan mace tana fuskantar matsalar bushewar gaba ko kuma cutar 'infection', ta ga likita domin a san maganin da za a ba ta, domin abin zai iya kawo ruɗani.
8. Matsalolin aure
Wata babbar matsalar kuma da masana suka gano ita ce matsala a zamatakewar aure.
"Wani lokaci ma'aurata za su zo mana da ƙorafi kan kwanciyar aure, kamar abin da ya shafi yadda mace ba ta samun gamsuwa, amma idan muka bincika sai mu gano cewa yana da alaƙa ne da wasu matsalolin zamantakewa," in ji likitan.
Idan haka ne, masalahar ita ce a mayar da hankali wajen magance ainahin matsalar, wadda baya ga kwanciyar aure, za ta iya haifar da wasu matsalolin a zamantakewa na auratayya.











