Me ya sa ake tababa kan alƙaluman haɓakar tattalin arziƙin Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba tafka muhawara game da ƙididdigar Bankin Duniya da ke nuna cewa tattalin arzikin Najeriya na samun tagomashi, lamarin da wasu ƴan ƙasar ke kwatantawa da al'amara.
A wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar, tattalin arzikin Najeriya ya samu cigaba a 2024, fiye da kusan shekara 10.
Waɗannan alƙaluman sun fito ne a daidai lokacin da mutanen Najeriya musamman ma'aikata da masu ƙananan sana'o'i suke ƙorafin taɓarɓarewar tattalin arzikinsu, musamman wajen ɗaukar ɗawainiyar iyali da harkokin yau da kullum.
Tun bayan cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya sanar a ranar da ya ɗare karagar mulki ne farashin kayayyaki suka yi tashin gwauron zabi a ƙasar, wanda har ya kai ga ƴan ƙasar sun gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a shekarar da ta gabata.
Sai dai shi kansa bankin na duniya ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar na ci gaba da zama babban ƙalubale ga tattalin arzikin ƙasar da ma walwalar jama'arta.
Haka kuma bayan rahoton cewa tattalin arzikin ƙasar, Babban Bankin ya kuma yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunƙasa da kashi 3.6 a shekarar 2025, sannan bankin ya ce dole gwamnatin ta ɗore kan manufofin da take ɗauka.
Ana gani a ƙasa?
Ba tun yanzu ba ne ƴan Najeriya suke nuna shakku kan irin waɗannan rahotannin na Bankin Duniya da Asusun Bayar da Lamuni na Duniya wato IMF, inda a lokuta da dama idan sun fitar da alƙaluman haɓakar tattalin arziki ƴan ƙasar suke cewa ba su gani a ƙasa ba.
Domin jin ko yaya lamarin yake, BBC ta tuntuɓi masanin tattalin arziki a Najeriya, Shu'aibu Idris Mikati, wanda ya ce ci gaba ne irin na mai haƙar rijiya ake gani a tattalin arzikin Najeriya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce, "Wannan abu ne da yake ba mu mamaki. Lokuta da dama hasashe Bankin Duniya da na Asusun Bayar da Lamuni sukan bambanta. Hasashen IMF mako uku ko huɗu da suka gabata ya sha bamban da na Bankin Duniya," in ji shi.
Ya ce idan aka lura da yanayin rayuwar ƴan Najeriya, za a fahimci komai, inda ya ce, "Bahaushe yana da karin magana cewa wai an ce wa kare ana biki a gidansu, sai ya 'mu gani a ƙasa'. Idan an ce tattalin arzikin Najeriya yana bunƙasa, anya akwai ƴan Najeriya da za su ce suna jin daɗin halin da ake ciki a yanzu?"
Ya ce akwai mamaki ganin yadda hauhawar farashi da rashin wutar lantarki da rashin tsaro suka addabi ƴan ƙasar, "ga kuma lafta mana haraji da ake yi sannan sai wani ko wata hukuma ta ce wai tattalin arzikin Najeriya na samun ci gaba, ai sai dai ci gaban mai hakar rijiya," in ji Mikati.
A game da abin da ya sa hasashen hukumomin kuɗin na duniya suke shan bamban, Mikati ya ce dama kowa na da yadda kallon abubuwa.
"Misali kofi ne aka zuba ruwa rabin kofi, wani zai ce a cike yake, wani kuma ce babu ruwa a ciki. Abu ɗaya ne, amma bayanin da ke fita ya sha bamban."
Sai dai ya ce ana samun ci gaba a ɓangaren karɓar haraji, wanda a cewarsa ya sa gwamnati ke da kuɗaɗen da za ta biya bashi da kuɗin ruwa da ake binta. "Wannan za ka iya cewa an samu ci gaba."
Sai dai ya ce, "Daga lokacin da Tinubu ya karɓa mulki zuwa yanzu kamfanoni nawa suka daina aiki? mutane nawa ne jarinsu ya karye suka koma marasa aiki? Talaka zai saya taki ya yi noma, amma ya sayar a asara, ma'aikata da dama albashinsu ba ya wuce musu mako ɗaya. Sannan a ce tattalin arziki yana ci gaba, ta ina?"
Me ya kamata a yi?
A game da ko akwai abin da gwamnati da ma ƴan ƙasar za su yi domin tabbatar da cewa tattalin arzikin ƙasar da na ƴan ƙasar suna bunƙasa a tare, Mikati ya ce dole gwamnati ta riƙ tausayin talakawa a lokacin ɗaukar matakai.
Ya ce, "A saka idon basiri da tunani da tausayi. Za a cire tallafin mai, me ya kamata a yi wa talaka da zai ji sauƙi? za a cire tallafin lantarki, me za a yi wa mara Ƙarfi? ba zai yiwu a ce wai ba za a ba talaka tallafi ba," in ji shi.
Ya ce dole ne gwamnati ta fito da hanyoyin da ya na taimakon marasa ƙarfi da talakawa na karkara.
"Idan ba mun samu wannan salon ba, haka za ai ta tafiyar da harkokon tattalin arzikin ƙasar, ana ganin ana ci gaba, amma mutane ba sa gani a ƙasa."











