Wane tasiri kwamitin da Tinubu ya kafa zai yi kan matsalar tattalin arzikin Najeriya?

...

Asalin hoton, TINUBU FACEBOOK

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa wasu manyan kwamitoci biyu na tattalin arziki domin warware matsalar tattalin arzikin ƙasar.

Kwamiti na farko shi ne kwamitin tattalin arziƙi na shugaban ƙasa (PECC) wanda ya ƙunshi mambobi 31, ciki har da shi kansa shugaba Tinubu da mataimakinsa da shugaban majalisar dattawa, da kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya.

Ɗaya kwamiti kuma shi ne kwamitin kar ta kwana kan farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya EET mai mambobi 19 da shugaban ya umarcesu da su dinga ganawa sau biyu a mako tare da tsara wani cikakken tsarin shiga tsakani na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar na tsawon watanni shida na shekarar 2024.

Majalisar zartaswa ta Najeriya ta amince da Kwamitin na EET a ranar Litinin.

Shugaban ya bai wa kwamitin na EET umarnin aiwatar da shirin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar wanda ya ƙunshi watanni shida masu zuwa, ba tare da ɓata wani lokaci ba a cikin makonni biyu da ƙaddamar da kwamitin.

Kwamitin na EET, wanda ya haɗa da ministoci da gwamnoni, da wakilan kamfanoni masu zaman kansu, an wajabta masa gabatar da rahoto ga kwamitin PECC, wanda kuma ke sa ido kan kokarin daidaita tattalin arziki.

Fitattun ƴan kwamitin na PECC sun haɗa da ministoci 13, da gwamnan babban bankin Najeriya, da fitattun ‘yan kasuwa kamar su Aliko Dangote da Tony Elumelu.

Wannan tsarin haɗin gwiwar yana nuna ƙudurin Tinubu na tsayawa tsayin daka wajen shirya tsarin tattalin arzikin ƙasar da kuma aiwatar da shi yadda ya kamata.

Waɗan nan tsare-tsare na nufin gyara tsarin tafiyar da tattalin arzikin Najeriya da magance matsalolin kudi da ƴan ƙasar ke ci gaba da fuskanta, kamar yadda fadar shugaban ƙasa ta bayyana a wata sanarwa da mai bai wa Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar.

Wadan nan ci gaban sun zo ne sakamakon ƙalubalen tattalin arziki na baya-bayan nan da suka kara tabarbarewa biyo bayan sauye-sauyen manufofin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar da suka haɗa da cire tallafin man fetur da taɓarbarewar darajar naira da ya haifar da tashin gwauron zabin abinci da dai sauransu, lamarin da ya jefa ‘yan Najeriya da dama cikin halin kunci.

Kafa kwamitin PECC da EET na nuni da yunƙurin dabarun magance waɗannan ƙalubalen gaba ɗaya. Ta hanyar hada manyan masu ruwa da tsaki daga gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu.

Abin da masana ke cewa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Aliyu Da'u Aliyu, mai sharhi ne kan sha'anin tattalin arzikin Najeriya kuma ya shaida wa BBC cewa wannan kwamitin da shugaba Tinubu ya kafa kusan an makara, inda ya ce ya kamata a ce tun farkon hawan Tinubu mulki kuma tun kafin a ce an janye tallafin man fetur da kuma janye tallafin dala da ake badawa ya kamata a ce akwai waɗannan kwamitoci.

"Ya kamata a ce waɗannan kwamitoci suna ƙasa tun kafin wani abu, inda za a ce sun zauna sun fitar da tsari cewa idan aka cire tallafin man fetur da na dala, dole akwai wasu abubuwa da za su iya faruwa, su fito da tsarin yadda za su yi su tunkari waɗannan matsaloli da kuma hanyar da za a bi a kawo wa ƴan Najeriya sauƙi." in ji mai sharhin.

"Amma masu iya magana na cewa gwara a makara da a ƙi zuwa baki ɗaya, saboda haka wannan kwamitin da Tinubu ya kafa, abu ne mai kyau." Aliyu ya ƙara da cewa.

Mai sharhin ya kuma ce "na tabbata cewa idan aka duba irin mutanen da aka ɗauko musamman masu zaman kansu kamar irinsu Aliko Ɗangoto da sauran manya-manyan mutane, na tabbata waɗannan abubuwa za su yi tasiri sosai."

"Tabbas, ni a ganina za a sami sauƙi bayan kafa waɗannan kwamti amma kamar yadda bahaushe ke cewa ciwo shi ne yake shiga farar ɗaya, amma sauki sai a hankali."

Aliyu ya ce idan dai aka bai wa waɗannan kwamtin dama wajen gudanar da ayyukansu kuma suka yi yadda ya kamata, ya tabbata a hankali ƴan Najeriya za su fara ganin canji da sauƙin da ake nema nan gaba.

"Amma kuma ya dangata da muhimmancin da gwamnati ta bai wa kwamitocin da mutanen da ke ciki da kuma yadda take a shirye wajen aiwatar da shawarwari ko da suna da ɗaci da kuma nauyi."

"Amma kuma ni a lissafina kan halin da aka shiga a Najeriya a yanzu, dole shugabanni su kansu sai sun shiga taitayinsu, na tabbatar idan aka bayar da shawarwarin kuma suka duba, idan ba ba su yi ɗari bisa ɗari ba, za su yi wasu daga ciki."

Mai sharhin ya ce nasarar wadannan tsare-tsare dai ya ta’allaka ne kan yadda kwamitocin za su iya magance matsalolin da ke addabar Najeriya da tabarbarewar tattalin arziki da suka hada da hauhawar farashin kaya da rashin aikin yi, da nakasar ababen more rayuwa yayin da kuma ’yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan mawuyacin halin da ake ciki.