Ko ta yaya cigaban tattalin arzikin Najeriya ko akasi ya shafe ku?

mutane biyu na zaune a rumfar sayar da kayan miya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Farashin kayayyakin abinci sun tashi a watannin baya-bayan nan a Najeriya
    • Marubuci, Yusuf Akinpelu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos

Tattalin arziki mafi girma a Afrika sannu a hankali na ƙaruwa, amma ƴan Najeriya ba su fara gani a ƙasa ba, saboda hauhawar farashin kayayyakin amfanin yau da kullum.

Rayuwa na ci- gaba da ƙara tsada. Farashin abinci da na sufuri sun tashi ga kuma darajar kuɗin ƙasar, naira ta yi mummunar faɗuwa idan aka kwatanta da dalar Amurka.

Tattalin arzikin ƙasa na cikin gida (GDP) na daga cikin abubuwan da gwamnati ke amfani da su wajen fahimtar yadda tattalin arzikin ƙasar yake.

Mene ne tattalin arziki na cikin gidan Najeriya (GDP)?

Alƙaluma na baya-bayan nan da hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta fitar sun nuna cewa tattalin arzikin ƙasar na ƙaruwa da kashi 3.46 a cikin dari, a watanni uku na ƙarshen shekarar da ta gabata ta 2023.

A lokacin (GDP) ya fi na sauran watannin da suka gabace su a shekarar. Sai dai ƙarin bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta shi da watanni uku na ƙarshen shekarar 2022.

A lokacin ma'aunin ya nuna tattalin arzikin ya ƙaru da kashi 3.52 cikn ɗari. Haka kuma idan aka kwatanta ɗaukacin shekarar ta 2023 da ta 2022 da kuma 2021. Shekarar 2023 ce mafi rauni.

Me hakan ke nufi ga ƴan Najeriya?

Yana nufin saye da sayarwa na kayayyaki da kuma abubuwan da kamfanoni ke samarwa, gwamnatoci da ɗaiɗaikun mutane a Najeriyar sun ƙaru a cikin watanni uku na ƙarshen shekarar 2023.

Wasu masana tattalin arziki sun bayyana cewa raguwar da aka samu a lokacin ya faru ne bayan ci-gaban da aka samu gabannin babban zaben da aka yi a bara da kuma ƙaruwar kuɗaɗen da aka kashe lokacin bukukuwan karshen shekara da kirsimeti da kuma sabuwar shekara.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana ɗaukar alkaluman tattalin arziki na cikin gida (GDP) duk wata, amma alƙaluman watannin uku a jere, wato kowane kashi daya bisa hudu na watannin shekara - an fi ɗaukarsu da muhimmanci.

Yawan alƙaluman na nuna girman tattalin arziki. Saboda haka tattalin arziki na bunƙasa ne idan alƙaluman kowanne watan shekara na ƙaruwa fiye da waɗanda suka gaba ce su.

Tattalin arzikin da ke ƙaruwa, abu ne na farin ciki ga masana tattalin arziki da ƴan siyasa da ƴan kasuwa saboda hakan na nufin za a iya kashe ƙarin kuɗaɗe da ƙara guraben da kuma ayyuka ƙarin haraji da ake biya sannan za a iya ƙarin albashi ga ma'aikata.

Amma kuma dangane da tattalin arzikin cikin gidan da ke raguwa hakan na nufin mutane ba sa yin abubuwan da ke kawo ƙarin kuɗaɗe - a don haka ba za su iya sayen abubuwan da suke buƙata ba, kuma kasuwanci zai shiga wani hali.

Idan ƙasa ta kwashe watannin uku-uku a jere, watanni shida ke nan alƙalumanta na raguwa shi ake kira durƙushewar tattalin arziki, kuma hakan zai iya kai wa ga kasa biyan albashi da rasa ayyuka.

Ta ya ya GDP ya shafe ku?

Tattalin arzikin cikin gida ko kuma GDP abu ne mai muhimmanci da ke nuna yadda tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

Samun dogon lokaci alƙaluman ma'aunin na ƙaruwa na nufin mutane na ƙara samu, kuma kuɗaɗen da suke kashewa na ƙaruwa.

Kuma wata hanya ce da take taimaka wa gwamnati wajen shirya abubuwan da za ta yi nan gaba da kuma irin kuɗaɗen da za ta samu na haraji daga mutane.

Haka kuma yana taimaka wa kamfanoni da masana'antu yanke shawarar faɗaɗa kasuwancinsu da kuma ƙarin ma'aikata.

Ƙaruwar GDP na nufin gwamnati tana da kuɗaɗen da za ta ƙara kashewa a kan makarantu da asibitoci da tituna.

Shi ya sa gwamnati ke amfani da ma'aunin a matsayin wata hujjar cewa tana tafiyar da tattalin arziki yadda ya kamata.

Sannan idan ya yi ƙasa, su kuma ƴan adawar siyasa su ce gwamnati ba ta yin abun da ya kamata.

Bugu da ƙari, raguwar GDP na nufin mutane sun rage saye da sayarwa, wanda hakan ke shafar lalitar gwamnati.

Kuɗaɗen harajinta na raguwa, lamarin da zai sa ta tsuke bakin aljihu ko kuma ta ƙara kuɗin haraji.

A shekarar 2020 annobar korona ta jefa Najeriya cikin durƙushewar tattalin arziki mafi muni da ba ta gani ba a shekara 40.

Amma tattalin arzikin ya ci-gaba da ƙaruwa a 2021. Wanda kuma ya fara samun komabaya shekaru biyu bayan nan.

Ta yaya rashin aikin yi ke shafar GDP?

Idan mutane ba sa aiki, GDP na raguwa.

Ƙarin kuɗin da ake biya bayan an yi aiki na nufin ƙarin kudi a aljihun mutane.

Rashin aikin yi ya ƙaru da kashi biyar cikin ɗari a watanni uku na ƙarshen shekarar 2023 daga kashi 4.2 cikin ɗari a watanni uku da suka gabace su a shekarar da ta wuce. A cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasar, NBS.

Takardun naira mafiya girma

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Darajar naira ta yi mummunar faɗuwa a kan dalar Amurka

Me ya sa ba ma gani a ƙasa idan GDP na ƙaruwa ?

Saboda GDP bai ƙunshi duka abubuwan da ke faruwa a zahiri ba.

Idan alƙaluman GDP na ƙaruwa, hakan ba yana nufin ɗaiɗaikun mutane na samun ƙarin kuɗade ba ne.

Samun ƙaruwar GDP, ta yiwu saboda an samu ƙaruwar al'ummar ƙasa ne, saboda idan akwai ƙaruwar mutane to kuɗaden da suke kashewa za su ƙaru.

Amma ba lallai ba ne mutanen ƙasa su zama masu arziki ba. Ta yiwu ma suna ƙara talaucewa ne matsakaitansu, duk da cewa GDP na ƙaruwa.

Haka zakali za ta iya yiwuwa masu kuɗi na ƙara samun kuɗi ne, maimakon cewa kowa a ƙasar na ƙara samun kuɗi.

Masu suka kuma na cewa GDP bai ƙunshi duka ayyuka ba. Ga misali ayyukan da ba a biya kamar na gida da ayyukan sakai da ayyukan bayan fage duka waɗannan ba sa cikin abubuwan da tattalin arziki na cikin gida ke dubawa, saboda suna da wuyar sanin ainihin girmansu ko darajarsu.

A sauƙaƙe idan ka gasa burodi ka sayar wa wani, hakan zai shiga cikin GDP, amma idan ka gasa burodi don iyalanka ba ya cikin abubuwan da ake ƙirgawa duk da cewa kayan da ka saya wajen yin burodin za su shiga cikin lissafi.

Shi yasa ake da abun da ake kira (GDP per capita) wato tattalin arzikin mutane — ta wannan hanyar ana kwatanta tattalin arziki na cikin gida da yawan al'ummar ƙasa don gano matsakaicin kuɗin da ke hannun kowane mutum.

Misali, idan ƙasa na da GDP mai yawan dala miliyan hudu kuma tana da al'umma 4,000, to hakan na nufin matsakaicin kudin da ke hannun kowa shi ne dala 1000.

Idan kuma wata kasa na yawan tattalin arzikin GDP dala miliyan 400 kuma tana da al'umma miliyan hudu to matsakaicin kudin hannun kowa shi ne dala 100. Abun da ke nufin ɗaiɗaikun mutanen ƙasar farko sun fi na kasa ta biyu arziki.

Hakan ne ya sa yayin da Najeriya da Masar ke cikin ƙasashen da suka fi kowa yawan tattalin arziki na cikin gida a Afrika, ba sa cikin ƙasashe 10 da ke da ƙarfin matsakaicin kuɗi a nahiyar.