'An kashe duk mutanen nan' - Binciken BBC kan zargin kisan kiyashi a Congo

Asalin hoton, Freddy Mukuza / Facebook
- Marubuci, Orla Guerin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Goma
- Lokacin karatu: Minti 10
Wani abokin mawaƙi Freddy Mukuza ne ya ga lokacinsa na ƙarshe a duniya tsawon mita 50 tsakaninsu, babu yadda zai yi.
Da aka shaida masa cewa ƴantawayen M23 sun harbe Freddy - shi da wasu mutane sun yi gaggawar zuwa wajen da ke Goma, a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.
"Da muka isa mun ga Freddy yana numfashi kuma mun so mu ɗauke shi daga wajen amma M23 suka hana mu," in ji abokin, wanda za mu kira Justin.
"Lokacin da muka dage kan haka, sai suka yi harbi a ƙasa a matsayin gargaɗin "idan kuka kuskura kuka tsallaka iyakarku, za mu kashe ku ku ma."
Sai suka ja baya, har Freddy mai shekara 31, ya cika. Lokacin ne kuma M23 suka bari muka je wajen gawarsa muka tafi da ita.
Jim kaɗan kafin kashe shi, wasu motocin ɗaukan kaya uku maƙare da mayaƙa sun shiga unguwar su Freddy - Kasika.
Wajen ƙarfe 3 a ranar Asabar 22 ga Fabarairu - kusan wata guda bayan mayaƙan sun ƙwace birnin Goma a nausawar da suka yi ta gabashin ƙasar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cikin kimanin sa'a ɗaya, mutum 17 zuwa 22 aka kashe, galibinsu matasa maza a cewar majiyoyi.
Mun tattaro bayanan wasu mazauna wurin, waɗanda za mu ɓoye sunayensu, saboda kare su.
Mun nemi ji daga M23 kan zargin gagarumin harin da suka kai a yankin. Ba su ce komai ba.
Jami'ai a Kasika ba su fitar da alƙaluman mutanen da suka mutu ba, sannan babu wani bincike kan abin da mutanen garin ke bayyanawa a matsayin kisan kiyashi.
Sai dai mazauna garin sun dage cewa M23 ita kaɗai ce ƙungiyar mayaƙa da ke aiwatar da ayyukansu ba tare da shamaki ba sannan suna harbe mutane da tsakar rana a Goma.
Tun bayan da suka ƙwace iko da garin a ƙarshen watan Janairu, mayaƙan ne ke da iko. Cikin waɗannan kwanaki 18 da muka yi kwanan ƙasa, ƙungiyar na da ƙarfi.
A baya, an sha zargin su da aikata miyagun laifuka a wasu yankunan.
Mayaƙan riƙe da bindiga ba su kaɗai suke aiki ba. Suna samun goyon bayan Rwanda mai maƙwaftaka, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da Amurka. Rwanda ta musanta haka, duk da cewa ta daina musanta kasancewar sojojinta a Kongo, inda ta ce suna wajen ne a matsayin kare kai.
Ana ganin M23 na kai hari Kasika saboda tsohon sansanin sojojin Congo a wajen yake.
Sansanin Katindo a yanzu yana rufe amma wasu sojoji da iyalansu har yanzu suna zaune a gundumar.

"Ba duka sojojin ba ne suka iya guduwa," in ji mazauna yankin. "Wasu sun ajiye makamansu suka kuma zauna a garin."
Sai dai Freddy Mukuza farar hula ne - yana da mata da ƴaƴa biyu, yana kuma fafutukar inganta rayuwarsa. Lokacin da gari ya yi zafi, yana samun kuɗin shiga ne ta hanyar yin kabu-kabu.
Ɗan fafutuka ne kuma mai rubuta waƙa da yake rera waƙa kan matsalolin da suka yi katutu a ƙasarsa - da ke da arzikin albarkatun ƙasa da mutanen ciki suka kasance mafi fama da talauci a duniya.
Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo ta yi fice kan rashawa da rashin zaman lafiya - da yawan tashin hankali, tsawon shekaru 30.
Cin zarafi ta hanyar lalata ya zama ruwan dare. Gwamnati tana da rauni.
Akwai abubuwa da dama da Freddy zai yi waƙa a kai.
Ɗaya daga cikin waƙoƙinsa mai suna Au Secours (Taimako da Faransanci) kalaman waƙar na cike da tambayoyin da ba a amsa su ba:
"Wa zai kai wa waɗannan mutanen agaji? Wa zai taimaki matan da aka yi wa fyaɗe? Wane ne zai agaza wa maza marasa aikin yi?... Mutane na cikin haɗari, ba su da isasshen abin da za su ci. Hukumomi na sayen motoci."
A ranar da ya mutu, Freddy ya koma wani sabon gida da ya karɓi haya a Kasika. Ɗan'uwan matarsa yana taimaka masa saka tampol (tarpaulin) a rufin gidan.
Ƴar'uwar matarsa ita ma tana wajen, tana taya su gyara gidan. Da suka ji ƙarar harbi, suna cikin gida sai suka yi sauri suka rufe kofa, amma sai mayaƙan M23 suka gan su.
Mayaƙan sun harbe ƴan'uwan matar Freddy, a cewar abokinsa Justin.
Tun lokacin, Justin ba ya iya barin gida, ko ma ya fita neman kuɗi. Iyalinsa na rayuwa ne kawai ta hanyar cin ganyayyaki da kayan marmari. Shayi kuwa ya zama gwal - ba sa samu su sha.
Ƴaƴansa sun daina zuwa makaranta saboda fargabar M23 za su iya far masu a makaranta su kuma tilasta masu shiga ƙungiyarsu.
"Muna ganin kasancewa a raye shi ne ya fi muhimmanci," in ji shi.
Duniyarsa ta zama yana yin ta ne a cikin gidansa. Akwai fargabar cewa mayakan za su iya komawa garin domin farautar matasa maza su zama cikinsu.
Ganin ɗaya daga cikin motar ɗaukan kaya ta mayaƙan kaɗai a kan titi, ke sa mazauna garin rantawa a-na kare, in ji shi.
A baya-bayan nan yana wahala ka ga tawagar matasa suna magana tare, ya faɗa mana, sannan maƙwafta ba sa kokawa kan hukumomi kamar yadda suke yi a baya kafin ƴantawayen su ƙwace iko.
"A baya, babu nagartacciyar gwamnati, amma muna da ƴanci," in ji shi. "Akwai almundahana. Akwai rashin alkinta kuɗin gwamnati kuma muna magana a kai. Muna da damar zuwa kotu. A yanzu, akwai gwamnati maras magarta, amma muna zaune cikin yanayi na ta'addanci kuma ba mu iya magana."
Justin yana magana da mu saboda yana son a tuna da Freddy Mukuza kuma yana son duniya ta san yadda suke rayuwa a karƙashin mulkin M23.
Tun bayan kashe-kashen, al'ummar Kasika na cikin fargaba. Ƴanjarida a yankin ba su iya bayar da rahoton labarin ba.
Amma washegari - 23 ga Fabarairu - an wallafa wani bidiyo da aka ɗauka a tsorace a shafukan sada zumunta, da ke nuna wasu daga cikin mutanen: ana iya ganin gawarwaki 10 - da aka yasar a wani kango. Babu tabbaci ko cikin mutanen akwai sojoji.
A gefe kuma, ana jiyo ihu da kararraki. Wata mata na ta nanata cewa "Su 10 ne," yayin da take bi gawa-gawa.
"Za su halaka mu duka," in ji ta. "Sun kashe duka waɗannan matasan. Ba wannan ba ne Junior? Kamar shi ne. Magini ne."
Da babu bidiyon, labarin kashe-kashen watakila ba zai karaɗe garin ba.
Ɗaya daga daga cikin majiyoyi ya ce sahihi ne. Wani ya tabbatar da wurin da aka ɗauki bidiyon a Kasika ne.
Ya ziyarci wajen bayan da aka kwashe gawawwakin. Sannan ya gane ɗaya daga cikin waɗanda aka gani suna kuka a bidiyon, daga kusa da garin.
Majiyoyinmu biyu sun ce mafi ƙanƙantar shekaru da ya mutu a Kasika yaro ne da shekarunsa ba su wuce 13 zuwa 14 ba. Matashin yana gidansa, ɓoye a bayan ƴar'uwansa mata.
"M23 sun ce: "Idan yaron nan ya ƙi bin mu, za mu kashe dukkan ku," wani mutum ya faɗa mana.
Sai aka tafi da yaron zuwa wurin mutuwarsa.
Akwai kuma wata matashiya cikin waɗanda suka mutu. Tana sayar da madara a titunan da ke cunkushe da jama'a.
Akwai kuma wani mai talla da shi ma aka kashe wanda shekarunsa ba su wuce 20 ba.
Lokacin da aka soma harbe-harben, yana zaune a inda yake talla - kan dandamalin da ke wajen gidansu, inda yake sayar da katin waya da fanken doughnut.
An ji shi yana roƙon mayaƙan cewa "shi ba soja ba ne.
"Ina sayar da katin waya ne kawai. Waɗannan kayana ne - katunan kiran waya da kwandon fanken doughnut ɗin da nake sayarwa."
Sai ya gudu. Ɗaya daga cikin abokansa ya ci gaba da labarin. Za mu kira shi John.
"Ina gida sai na j ƙarar harbin bindiga," John ya shaida mana. "Mutane suna cewa: 'Suna ɗaukan matasa ta ƙarfi. 'Na ga mutane suna gudu, har da abokina, sai ni ma na ranta a-na kare.
"Da muka kai bakin titi, ana ci gaba da harbe-harbe sai na ji ƙarar bindiga ta bayana, wani ya faɗi ƙasa.
Shi ne mai sayar da fanken doughnut ɗin.
Duk da shekarunsa, yana sakandare ne, a shekararƙarshe. Ɗalibi ne mai hazaƙa da bai soma makaranta da wuri ba saboda iyayensa ba za su iya ɗaukar nauyin karatunsa ba.
Amma John ya ce: "Kamar sauran matasa, yana da buri." Na shi burin shi ne ya zama injiniya.
John ya ce mayaƙan ba su damu da wanda suka kashe ba.
"Ba sa bincike kafin su harbi mutum," in ji shi. "Kawai suna harbin kan mai uwa da wabi ne da kuma kuma mutanen da suka tsere."
Lokacin da M23 suka ƙwace Goma, sun bayyana cewa ba su da gidajen yari. John ya ce ba a buƙatar wani ƙarin bayani: "Hkan na nufin duk wanda aka yi tunanin sojan gwamnati ne, ko ɓarawo ko duk wanda ya yi kuskure, za a kashe shi nan take."
Makonni bayan nan, mutane ƙalilan ne suke iya fitowa su yi magana. "Babu wanda yake son ya zama wanda zai rasa ransa," in ji John.
Iyalan da aka kashe wa ƴan'uwa sun yi jana'iza a gaggauce - ba tare da zaman makokin da aka saba a gida ba.
"Mayaƙan ba sa son zaman makoki," in ji wata ƴar garin, da za mu kira Deborah. "Ba sa son mutane su yi kuka. Mun ɗauka sun zo su kawo zaman lafiya amma sai suka ɓuge da kashe mu. Suna kashe duk wanda suka gani kan titi."
Yayin da ake kame maza, ta yi ƙoƙarin fita waje. Mayaƙan sun umarce ta ta koma ciki, inda suka nuna mata bindiga.

Asalin hoton, Göktay Koraltan / BBC
Denis Baeni yana kan hanya lokacin da mayaƙan suka isa Kasika. Ya yi sauri ya faɗa cikin wani karamin shago domin ɓoye kansa tare da sauran mutane, in ji majiyarmu.
Malamin firamaren ya fito da katin shaidar maluntarsa daga aljihu. Ya yi tunanin za su tseratar da shi idan ya nuna masu shi farar hula ne.
Wata da ta san yadda lamarin yake - ta faɗa mana abin da ya faru. Za mu kira ta Rebecca.
"Sun ji murya a waje na tambayar: 'Sojoji ne?" in ji Rebecca. "Sai suka ce a a amma M23 suka fitar da su daga shagon."
An nemi mutanen su yi tattaki zuwa wani kwango inda aka jera su domin kashe su".
"Ƙarar harbi ta yi yawa sosai," in ji ta. "Muna jiyo ƙarar a kusa da mu. An kashe mutum 21 lokaci guda. Galibinsu masu wucewa ne."
Denis ya bar ƴaƴa biyu, wanda shi kaɗai ke kula da su.
Ba mutuwa kaɗai ba ce abin gudu. Mazauna garin suna kuma fuskantar haɗarin tilasta masu shiga ƙungiyar - ko suna so ko ba sa so.
"A kwanan nan dole maza su kasance a cikin gida daga karfe 5:30," in ji Rebecca. "Da zarar ƙarfe 6:00 ta yi, gari ya yi duhu, suna samun damar kwashe mutane cikin sauƙi."

Asalin hoton, AFP
Yayin da ake tilasta wa iyalai shiga yanayi na jimami a Kasika, M23 na ci gaba da kai hare-hare a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.
Bayan Goma, sun karɓe iko da birnin Bukavu a tsakiyar Fabarairu. Sun yi barazanar kutsawa har Kinshasa, babban birnin kasar mai nisan kilomita 1,600 daga wajen.
Sun yi iƙirarin su masu juyin-juya hali ne da ke son gyara ɓarnar da aka yi a ƙasar kuma su masu kare haƙƙoƙin al'ummar Tutsi tsiraru ne.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama suna bayyana wasu bayanai a kan M23.
Sun zargi ƴantawayen da munanan ayyukan cin zarafi tun kafata a 2012 - har da jefa bam kan yankunan farar hula da yi wa mata fyaɗe da kuma zartar wa mutane hukuncin kisa". Waɗannan zarge-zarge na ƙunshe a jerin rahotannin da aka gabatar.
A wata hira da BBC a baya-bayan nan, na tambayi jagoran ƴantawaye, Corneille Nangaa, don jin martaninsa. Yana shugabantar wata gamayyar jam'iyyun siyasa da mayaƙa - da ake kira ƙawancen Congo River - wanda ya haɗa har da M23.
"Ban ga rahotannin ba," in ji shi. "Ya ce ba zan iya cewa komai ba kan rahoton da ban karanta ba". Ya kuma ce bai damu da irin zarge-zargen da aka yi ba.
Da na kara neman sanin dalilin da ya sa bai duba rahotannin ba, sai ya ce: "Ba ni ɗaya, zan karanta."
Nangaa, wanda tsohon shugaban hukumar zaɓen Congo ne, yana yawan saka kaya masu kama da kakin soja da kuma kwata.
Gwamnatin Congo ta yi tayin bayar da dala miliyan 5 ga duk wanda ya ba da bayanin da ya kai ga kama shi.
Mayaƙan ba su kaɗai ne ke da taɓon cin zarafi ba a tarihi. Suma sojojin Congo da sauran ƙungiyoyin tawaye a gabashin Congo an yi masu irin waɗannan zarge-zarge.
Sai dai M23 a yanzu sune suke da iko a wasu yankunan gabashin ƙasar kuma sai yadda suka yi da miliyoyin ƴan Congo.
Da muka yi magana da wani mazaunin Kasika, matarsa ta kira shi, tana neman ya koma gida domin ɗauko ɗansu ɗan shekara takwas daga makaranta.
Ana cikin fargaba saboda rahotannin cewa M23 suna kwashe yara daga azuzuwansu.
Ya ɗauko yaronsa amma akwai fargaba game da abin da zai faru a gaba.
"Muna cikin tashin hankali. Sun ce sun zo domin ƴantar da mu," in ji shi. " Amma da alama yanzu suna neman yin garkuwa da mu."
Ƙarin gudunmawa daga Wietske Burema ta BBC.








