Shugaban ƴan tawaye da ya hana zaman lafiya a Kongo

Sultani Makenga.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sultani Makenga mutum ne da ba shi da tsoro ko kaɗan
    • Marubuci, Wedaeli Chibelushi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 6

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo na cikin ruɗani - mayaƙa daga gungun ƙungiyar ƴan tawayen M23 na ci gaba da dannawa zuwa gabashin ƙasar, inda suke fafatawa da sojoji da kuma ƙwace muhimman wurare.

A cikin makonni biyu, an ruwaito kashe dubban mutane kuma faɗan ya janyo yaƙin cacar-baka tsakanin Kongo da makwafciyarta Rwanda.

Shin ta yaya Kongo - ƙasa mafi girma a kudu da hamadar sahara - ta shiga wannan ruɗani?

Mafarin wannan rikicin mai sarkakiya ya faro ne ta labarin wani mutum - shugaban ƙungiyar M23, Sultani Makenga, wanda aka ɗora wa alhakin munanan hare-hare da aka kai a ƙasar.

An haife shi ne ranar bikin Kirsimeti na shekarar 1973, a wani gari mai suna Masisi a ƙasar ta Kongo.

Iyayensa sun kasance ƴan kabilar Tutsi, ya daina zuwa makaranta yana da shekara 17 - inda ya shiga cikin ƙungiyar ƴan tawaye ta kabilar Tutsi da ke kan iyaka a Rwanda.

Ƙungiyar wadda ake kira Rwandan Patriotic Front (RPF), na son a ƙara samun masu wakilcin ƴan Tutsi a gwamnatin Rwanda, wadda a lokacin ƴan kabilar Hutu suka mamaye.

Suna kuma son dubun-dubatar ƴan kabilar Tutsi da aka tilasta wa tashi daga ƙasar saboda rikicin kabilanci, su koma gidajensu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A tsawon shekara huɗu, Makenga da RPF sun gwabza da sojojin Rwanda waɗanda ƴan kabilar hutu suka fi yawa a ciki. An yi wa gwabzawar lakabi da 'Kisan kiyashin Rwanda na 1994' lokacin da ƴan Hutu masu tsattsauran ra'ayi suka kashe ƴan tutsi da suka kai 800,000 da ƴan Hutu kaɗan.

Yayin wata tattaunawa don tuna lamarin, Makenga ya ce: "Rayuwata tamkar yaƙi take, ilimina yaƙi ne kuma yarena ma yaƙi ne... amma ina girmama zaman lafiya."

Sannu a hankali ƙungiyar ta Rwandan Patriotic Front ta fara ƙwace garuruwa kafin ta isa zuwa Kigali, babban birnin Rwanda tare da hamɓarar da gwamnatin masu tsattsauran ra'ayi na Hutu - inda yawancinsu suka tsere zuwa Kongo.

Lokacin da RPF ta karɓi iko da mulki, Makenga ya shiga cikin rundunar sojin ƙasar Rwanda inda har ya kai muƙamin mataimakin kwamanda.

"Ya ƙware wajen tsara harin kwantan-ɓauna," kamar yadda wani mayaƙi kuma abokin Makenga ya faɗa wa wata cibiyar bincike.

Sai dai ya gamu da ɗan cikas wajen ƙarin girma a rundunar sojin ta Rwanda saboda ganin cewa bai yi karatu mai zurfi ba kuma Faransancinsa da kuma Ingilishi ba su yi ƙwari ba, a cewar cibiyar binciken ta Rift Valley.

Mayakan M23.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mayaƙan Makenga na M23 su ke iko da birnin Goma yanzu

An kuma ce har kawo yau - Makenga na fuskantar matsala wajen yin jawabi a bainar jama'a.

A 1997, yana cikin sojojin Rwanda da ke samun goyon baya waɗanda suka ƙwace iko a Kongo, tare da hamɓarar da shugaba Mobutu Sese Seko da ya daɗe yana mulki.

Sun naɗa wani sanannen shugaban ƴan tawaye a Kongo Laurent Kabila a matsayin shugaba.

Sai dai, Makenga ya fara samun saɓani da manyansa - sojojin Rwanda sun kama shi bayan da ya ƙi bin umarnin komawa ƙasar, a cewar rahoton kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

An tasa ƙeyarsa zuwa gidan yari na shekaru da dama a wani ɗan karamin tsibiri mai suna Iwawa a ƙasar.

A ɗaya gefen, dangantaka tsakanin Kabila da kuma sabbin shugabannin mulki a Rwanda sai ya taɓarɓare.

Rwanda ta yi yunƙurin murƙushe mayaƙa ƴan kabilar Hutu waɗanda ke da alhaki a kisan kiyashin ƙasar amma suka tsere ta kan iyaka a 1994. Fargabar da Rwanda ke da ita shi ne za su iya komawa da kuma kunna wata fitina a faɗin ƙasar bayan samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Sai dai Kabila ya kasa dakatar da mayaƙan daga haɗuwa, kuma ya fara korar sojojin Rwanda daga ƙasar.

Sakamakon haka, Rwanda ta mamayi Kongo a 1998. Lokacin da aka saki Makenga daga gidan yari, an naɗa shi muƙamin kwamanda a fagen daga da zai jagoranci ƙungiyar ƴan tawaye da ke samun goyon baya.

Youngsters in Goma watch as undertakers in white protective gear surround similarly white body bags

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An ruwaito cewa rikicin baya-bayan nan da ya kai ga ƙwace birnin Goma ya janyo mutuwar dubban mutane cikin makonni biyu kaɗai

A tsawon shekaru da suka gabata, Makenga ya samu tagomashi - inda aka san shi da ƙwarewa wajen tsarawa da kuma jagorantar dakarun soji masu yawa da ke fafatawa a fagen daga.

Bayan da sojojin Rwanda suka tsallaka zuwa Kongo, an samu ƙaruwar tsangama da ake nuna wa al'ummar Tutsi. Kabila ya yi zargin cewa ƴan Tutsi sun goyi bayan mamayar, yayin da sauran jami'ai suka ingiza al'umma da su far wa ƴan kabilar.

Makenga - wanda har yanzu ke Jamhuriyar Kongo - ya zargi shugaban Kongo da yaudarar mayaƙan Tutsi, inda ya ce: "Kabila ɗan siyasa ne, ni kuma ba ɗan siyasa ba. Ni soja ne, kuma yaren da na sani shi ne bindiga."

Ƙasashen makwafta da dama sun shiga cikin rikicin kuma an tura dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD da yawa zuwa ƙasar don kwantar da hankali.

An yi imanin cewa sama da mutum miliyan biyar ne suka mutu a yaƙin da kuma bayansa - yawanci sakamakon yunwa da kuma cutuka.

Faɗan ya zo ƙarshe a 2003, sai dai Makenga ya ci gaba da kasancewa cikin ƙungiyoyin mayaƙa da ke adawa da gwamatin Kongo.

A wani yunkuri na sasantawa, ƴan tawayen Tutsi kamar Makenga sun haɗe zuwa cikin rundunar sojin Kongo.

Sai dai ba a daɗe ba - Makenga ya sauya sheka daga rundunar sojin zuwa ƴan tawayen M23 da ke ƙara samun goyon baya.

An ƙara wa Makenga matsayi zuwa babban janar na M23, ba a jima ba kuma ya zama shugaban ƙungiyar.

A 2012 ya jagoranci ƴan tawayen wajen tayar da gagarumar tarzoma, abin da ya kai suka ƙwace Goma, birni mai muhimmanci da ke gabashin ƙasar ta Kongo mai al'umma sama da miliyan ɗaya.

Jamuriyar Kongo da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya sun zargi gwamnatin Rwanda da ƴan kabilar Tutsi suka mamaye da mara wa M23 baya - zargi kuma da Kigali ta sha musantawa.

Sai dai, a baya-bayan nan martanin ya sauya, inda gwamnatin Rwandan ta ce faɗan da ake yi a kusa da iyakarta barazanar tsaro ce.

A shekarar ta 2012, Makenga da waɗansu sun fuskanci zarge-zargen aikata laifukan yaƙi. Amurka ta kakaba masa takunkumi, inda ta ce yana da alhaki "wajen ɗaukar yara shiga aikin yaƙi da kuma cin zarafin fararen hula". Makenga ya ce zargin da ake yi wa M23 na amfani da yara a matsayin mayaƙa ba shi da tushe.

A wani ɓangare, MDD ta ce shi ke da alhakin kashe-kashe da jikkata mutane, cin zarafin mata ta hanyar lalata da kuma yin garkuwa da mutane.

Sultani Makenga, lokacin da yake jawabi ga mayaƙa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Makenga ya shiga sahun bore da dama da aka yi wa gwamnatin Kongo

Zaman tattaunawa don tsagaita wuta tsakanin M23 da hukumomin Kongo ya gaza samuwa, inda a bara wani alkali ya yanke wa Makenga hukuncin kisa a bayansa.

Yayin dannawa da M23 ta yi a baya-bayan nan - inda aka ce suna samun goyon bayan dubban sojojin Rwanda - Ba a ga Makenga a bainar jama'a ba.

Maimakon haka ya bar wa mai magana da yawunsa alhakin yin jawabai da kuma wani mai suna Corneille Nangaa, wanda ke jagorantar ƙungiyoyin haɗaka na ƴan tawaye ciki har da M23.

Har yanzu Makenga mai faɗa a ji ne, inda yake tsara abubuwa a bayan fage.

Ya ce faɗan da yake yi na ƴaƴansa guda uku ne, "saboda watarana su samu makoma mai kyau a ƙasar nan".

"Ba na son a riƙa kallona a matsayin mutumin da ba ya son zaman lafiya. Ina da zuciya da iyali da kuma mutanen da nake kula da su," in ji Makenga.

Sai dai miliyoyin mutane na ɗanɗana kuɗarsu a wannan rikici, kuma idan sojojin Kongo suka kama shi, zai fuskanci hukuncin kisa.

Ba shi da tsoro ko kaɗan.

"A shirye nake na sadaukar da komai," in ji shi.