Abin da BBC ta gani a birnin Goma wanda ke 'hannun ƴan tawayen M23'

Nathaniel Cirho likita ne da aka jikkata a wani harin bam a gidansa da ke Goma
Bayanan hoto, Nathaniel Cirho likita ne da aka jikkata a wani harin bam a gidansa da ke Goma
    • Marubuci, Paul Njie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Goma
  • Lokacin karatu: Minti 6

A lokacin da na shiga birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, da motata, zai yi wahala ka fahimci ka shiga yankin da ake yaƙi.

Mazauna birnin Goma sun cike tittunan da ke iyaka da Rwanda - akwai ma'aikata da ke tururuwan tafiya aiki, masu talla na cinikinsu a bakin hanya, ga kuma ƴan tasi da ke neman fasinjoji.

Amma bayan wani ɗan lokaci kana iya fahimtar akwai sabuwar gwamnati a birnin.

A lokacin da na isa shingen bincike kusa da ƴansanda da a baya hukumomin Congo ke iko da shi, karar harbe-harbe na 'yan tawayen M23 suka yi mana maraba, da hanyar tsayar da motata.

A makon da ya gabata M23 suka kame Goma, yankin gabashin kasar mai al'umma kusan miliyan biyu, bayan danna kai da suka rinka yi a kokarin mamaya a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo, DRC.

Akalla mutane 700 aka kashe, sannan kusan dubu uku sun jikkata lokacin da 'yantawaye ke gumurzu da dakarun DR Congo da masu taimaka musu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin Congo.

M23 da galibi 'yan kabilar Tutsis ne, sun ce suna wannan yaki ne domin tabbatar da adalci da 'yanci tsiraru, yayinda gwamnatin DR Congo ke cewa 'yantawayen da Rwanda ke marawa baya na kokarin kwace gabashin kasar mai dimbin arzikin ma'adinai.

A shingen binciken, 'yantawayen M23 sun leka cikin motarta, sannan suka yi wa direba na 'yan tambayoyi kana daga bisani suka ce mu wuce harda daga mana hannu.

Da alama 'yantawayen ba su fuskanci wata turjiya ba - saboda za ka yi tunanin dama sun jima a wannan wurin.

Na doshi daya daga cikin asibitocin da ake kula da masu raunuka, kukan radadin ciwo ya karade ko ina a asibitin.

Na hadu da Nathaniel Cirho, wani likita da ke tsakiyar aiki bam ya tashi da shi a gidansa.

Ya na zaune a bakin gado ya shiga ba ni labari cewa bam ya tashi da shi da makwafcinsa, Mista Cirho. Ya kuma ba ni labarin yadda wani mutum mai shekara 65 da ya yi wa aiki ya mutu.

A dakunan asibitin na kuma riski wata tsohuwa kwance an sanya mata abin taimakawa wajen numfashi.

An harbe ta a hannunta lokacin musayar wuta tsakanin dakarun Congo da 'yantawaye.

"Kawai na ji sanyi a hannuna, nan na fahimci an harbe ni," a cewarta, tana kokarin magana da kyar.

M23 na karakaina a birnin Goma ba tare da wata matsala ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, M23 na karakaina a birnin ba tare da wata matsala ba

Matar ta bukaci a mayar da ita asibitin Kudi, inda yanzu ake ba ta kulawa, saboda ba ta samun kulawar da ta dace a asibitin gwamnati, saboda cunkoso.

Sai dai duk da an sauya mata asibiti, mutane sun yi wa likitoci yawa saboda yawan marasa lafiya da ake kawo wa.

"Galibinsu muna ba su kulawa saboda tsarin bukatar gaggawa da muke da shi", a cewar wani likita, wanda ba ya so mu ambaci sunansa saboda dalilai na tsaro.

Ya kara da cewa: "A ranar Lahadi lokacin da aka soma fada, mun karbi mutane 315 kuma duk mun ba su kulawa."

Amma a yanzu, asibitin na maganar mutane sun haura 700 da raunuka daban-daban, a cewar likitan.

Ya ba mu labarin yadda aka rinka kawo mutanen da "harbin bindiga ya same su a kai, wasu a kirji, wasu a ciki da hannu da kafafu".

Wata motar sojojin Congo da aka lalata lokacin kwace birnin Goma

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata motar sojojin Congo da aka lalata lokacin kwace birnin Goma
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yayinda gabashin Jamhuriyar Congo, DRC ya fada a rikicin siyasa, Ofishin kare hakkin bil adama a Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi amfani da wannan dama wajen cin zarafi ta hanyar lalata tsakanin bangarorin biyu.

Likitan da ke aiki a asibiti mai zaman kasa da ke hadin-gwiwa da MDD, ya ce sun karbi mata 10 da aka ci zarafinsu ko yi musu fyade daga soma wannan rikici.

Duk da cewa a yanzu abubuwa sun dan lafa har mutane na fita harkokinsu na yau da kullum a Goma, har yanzu akwai harkoki kasuwanci da ba su dawo ba. A wasu yankunan ma babu shaguna da suka bude, haka bankuna.

Babu mamaki akwai fargabar cewa komai mai iya yiwuwa ne ta fuskar tsaro.

"Mutane na tsoro...Ni kai na ina cikin fargaba mutanen da suka haddasa wannan rikici na tare da mu kuma ba mu fahimci abin da ke faruwa a," a cewar Sammy Matashi da ke harkar kasuwanci.

"Abin takaicin shi ne mutane ba sa iya cinikayya a wurinmu, galibi sun koma Rwanda, Bakavu, Kenya da Uganda."

Ya ce 'yan kasuwa da ke shigo da kayayyaki daga kasashe makwafta ba sa iyawa a yanzu.

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:
Hular sojoji da aka yasar a wajen sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD
Bayanan hoto, Hular sojoji da aka yasar a wajen sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD

Mutane da dama dana tattauna da su sun ce suna harkoki da mayakan M23 a wurarensu.

Kuma a matsayina na bako ina ganin yadda 'yantawayen suka karbe ragamar komai da tafiyar da lamura.

Sun kwace ofishin gwamnan soji da ke arewacin Kivu, wanda suka kashe a lokacin dannan kai Goma.

Mayakan sun kuma warwatsu a wurare da dama na birnin, yayinda wasunsu ke sintiri a motocin yaki dauke da makamansu.

A tsawon lokacin da na kwashe a Goma, ban ci karo da soja ko guda na Congo ba.

A kusa da sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD, (Monusco) - wanda ke da alhakin kare fararan-hula daga mayakan 'yan tawayen - kana iya ganin tarkacen abubuwan yaki da takardu da harsasai a tittuna.

"M23 sun zo wannan wuri, suka kewaye sojojinmu," a cewar Richard Ali da ke makwaftaka da wurin.

"Galibin su sun cire kakinsu na soja, sun jefar da makamansu da sanya kayan farar-hula. Wasu kuma sun tsere."

Ginin shirin samar da abinci na MDD da aka yi wawaso a lokacin kokarin kwace Goma da kuma lalata motar agaji ta ICRC

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ginin shirin samar da abinci na MDD da aka yi wawaso a lokacin kokarin kwace Goma da kuma lalata motar agaji ta ICRC

Yayin da M23 ke murnar nasararsu, gwamnatin Congo na cigaba da kalubalantar ikirarin 'yan tawayen na kwace ikon Goma.

Gwamnati ta zargi M23 da mamaye yankin ta haramtacciyar hanya - da taimakon Rwanda - da alkawarta dakile su nan ba da jimawa ba.

Duk da cewa Rwanda ta sha musanta wannan zargi na mara baya ga ƴan tawaye, martanin da take mayarwa ya zama kamar na kare kai, abin da ya sa kakakin gwamnati ke cewa fada a kan iyakasu barazana ce a garesu.

'Yan tawayen a yanzu sun doshi kudanci zuwa yankin Bukavi, wato birnin Kudancin Kivu, kuma sun lashi takobin kai wa ga birnin Kinshasa,

A yanzu, Goma ya kasance makaminsu. Kuma abubuwa za su cigaba da sauyawa 'yan Congo muddin 'yan tawayen suka cigaba da samu nasara.

Tare da gudumawar wakilan BBC Robert Kiptoo da Hassan Lali da ke a Goma.