Ƴan tawaye sun ce sun karɓe iko da birnin Goma na ƙasar Kongo

Mutane na tserewa daga birnin Goma

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Malu Cursino
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan tawayen sun ce sun karɓe iko da garin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, duk da cewa gwamnati ta musanta hakan.

Mazauna birnin sun yaɗa hotunan bidiyo da ke nuna ƴan tawayen M23 na sintiri kan tituna bayan dannawa da suka yi don gamuwa da sojojin ƙasar ranar Lahadi, abin da ya janyo tserewar dubun-dubatar mutane da ke maƙwabtan garuruwa.

Bayan sa'o'i da aka ɗauka ana musayar wuta da kuma fashewar abubuwa, titunan birnin Goma - da suka kasance gida ga sama da mutum miliyan ɗaya - ya yi tsit, a cewar kafofin yaɗa labaran ƙasar.

Hakan na zuwa sa'o'i bayan da ministan harkokin wajen ƙasar ta Kongo ya zargi Rwanda da ayyana yaƙi ta hanyar tura dakaru zuwa kan iyaƙa domin taimakon ƴan tawayen M23. Rwanda ta ce Kinshasa na mara wa mayaƙa da ke son ganin an sauya gwamnati a Kigali.

Kenya ta yi kira da a tsagaita wuta, kuma ta sanar da cewa shugabannin ƙasashen Kongo da Rwanda za su halarci wani taron gaggawa a cikin kwanaki biyu masu zuwa.

Shugaban Kenya, William Ruto, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ƙasashen Gabashin Afrika, ya ce ya zama dole shugabanni su taimaka wajen laluɓo hanyar mafita na warware rikicin.

Ƴan tawayen M23 sun ƙwace iko da yankuna da dama na Kongo mai albarkatun ƙasa tun 2021. A makonni da suka gabata, sun cigaba da dannawa zuwa birnin Goma yayin da ake cigaba da gwabza faɗa.

Tun shiga 2025, an tilasta wa mutum sama da 400,000 tserewa gidajensu a arewaci da kuma kudancin Kivu, kusa da iyaƙa da Rwanda, a cewar hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wata mata, Alice Feza, ta ce ta rasa abin da za ta yi, bayan tserewa daga Kiwanja da Rutshuru da Kibumba, yanzu kuma Goma.

"Mutane na ta tserewa, kuma ba mu san inda za mu je ba yanzu, saboda mun yi ta tserewa na tsawon lokaci," in ji Ms Feza, ta ƙara da cewa: "Yaƙi ya cimmana a nan tare da iyalanmu, a yanzu ba mu da wurin zuwa."

An toshe muhimman hanyoyi da suka dangana da birnin Goma, kuma ba a iya amfani da filin jirgin saman birnin yanzu wajen kwashe mutane da kuma kai taimakon jin-kai, a cewar MDD.

A wata sanarwa da gwamnati ta fitar a safiyar yau Litinin, ta ce dakarunta na cigaba da iko da muhimman wurare a birnin ciki har da filin jirgin sama.

"Saɓanin bayanai da ke yawo kan kafofin sada zumunta, muna son tabbatar da cewa dakarunmu na cigaba da iko da filin jirgin saman Goma... da kuma muhimman wurare a yankin," in ji ta.

Ta ƙara da cewa a shirye sojoji suke domin kare ƙasar ga duk wata barazana.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "akwai ruɗani a birnin; a nan kusa da filin jirgin sama, mun ga sojoji. Ban ga ƴan M23 ba zuwa yanzu", inda ya ƙara da cewa akwai bayanai da fasa shaguna tare da satar kayayyaki.

Wani ɗan jarida a yankin Akilimali Selah Chomachoma ya faɗa wa BBC cewa ana cigaba da musayar wuta kuma lamarin yana ƙara yin "muni".

Rabaren Damiri, shugaban wani asbiti a Goma, ya shaida wa BBC cewa hankali na kwance a inda yake, duk da cewa yana jin ƙara harbe-harbe daga wani ɓangare na birnin.

"Goma babban birni ne... Akwai sojoji da yawa da suke can, sojojin gwamnati, sai dai babban ɓangare na yankin na karkashin ikon ƴan tawaye," in ji shi.

Mutane na tserewa

Asalin hoton, Getty Images

Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres ya yi kira ga Rwanda da ta janye sojojinta daga Kongo da kuma cewa M23 su dakatar da dannawa zuwa birnin Goma.

A wata sanarwa da aka fitar, Guterres ya yi kira ga Rwanda ta "dakatar da goyon baya da take bai wa M23 da kuma janyewa daga Kongo". Ya kuma yi kira ga ƴan tawayen M23 da su "gaggauta fita da kuma barin yankuna da suka mamaye a Kongo".

Wannan na zuwa bayan kashe sojoji 13 da suke wanzar da zaman lafiya, bayan artabu da ƴan tawaye.

Birtaniya ta yi kira da a kawo karshen hare-hare kan dakarun wanzar da zaman lafiya, yayin da wakilin Faransa a MDD, Nicolas de Rivière, ya nanata kiran da Guterres ya yi na cewa Rwanda ta janye dakarunta daga Kongo.

Kongo da MDD duka sun ce M23 na samun goyon baya daga Rwanda.

Rwanda ba ta musanta hakan ba, sai dai jagororin ƙasar sun ɗora laifin rikicin kan Kongo.

Da yake magana a taron kwamitin tsaro, wakilin Rwanda a MDD Ernest Rwamucyo ya nuna rashin jin daɗin Alla-wadai da ƙasashen waje suka yi wa ƴan tawayen M23 maimakon sojojin Kongo, wanda ya ce, ta saɓawa yarjejeniyar tsagaita wuta.

A ranar Asabar, MDD ta ce za ta ɗebi yawancin jami'anta daga birnin Goma.

An kirkiro da ƴan tawayen M23 ne a 2012, da nufin kare al'ummar Tutsi da ke gabashin Kongo, waɗanda suka daɗe suna korafin cewa ana musguna musu.

A baya, Rwanda ta ce hukumomin Kongo na aiki da waɗanda take zargi da hannu a kisan kare dangi a ƙasar a 1994, waɗanda suka tsere ta kan iyaƙa zuwa Kongo.

Sai dai, masu sukar Rwanda sun zarge ta da amfani da M23 domin satar albarkatun ƙasa kamar zinare da cobalt a gabashin Kongo.