Yadda aka ƙona motum 20 har lahira ciki har da marasa lafiya a Kongo

DRC

Asalin hoton, AFP

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an kashe mutum 20, tare da yin garkuwa da wasu gommai, a wasu jerin hare-hare a gabashin Jamhuriyar Dimumokraɗiyyar Kongo.

Cikin waɗanda aka kashe har da ƙananan yara, tare da marasa lafiya aƙalla hudu da aka ƙone da ransu a cikin wani karamin asibiti da ke arewacin yankin Kivu

Ana ɗora alhakin harin kan reshen kungiyar ISIS da ke ayyukanta a kasar.

Kungiyar wacce Amurka ta ayyana a matsayin kungiyar ta'addanci ta yi kaurin suna wajen daukar alhakin muggan hare-hare a kasar.

DRC

Asalin hoton, AFP

Shaidu sun ce ana ci gaba da gwabza kazamin fada a yankin arewacin Kivu, tsakanin dakaraun kasar masu samun goyon bayan jami'an kiyaye zaman lafiya na Majalaisar Dinkin Duniya da kuma 'yan tawayen a daya bangaren.

A ranar Alhamis ne dai 'yan tawayen dauke da makamai suka kai wa asibitin garin Lume hari, inda suka kashe mutane da dama ciki har da marasa lafiya hudu da ke kwance a asibitin. Jami'an kiyaye zaman lafiya a kasar sun ce an rusa daruruwan gidaje a kauyukan da ke kewayen garin Lume.

An bayar da rohoton cewa goman mutane cikin har da kananan yara 30 ne ba a gani ba kawo yanzu, wadanda aka yi amanna cewa suna hannun 'yan tawayen.

Haka kuma an samu musayar wuta tsakanin jami'an kiyaye zaman lafiyar da 'yan tawayen a yankin Ituri .

A baya-bayan nan dai kasar Jamhuriyar dumokradiyyar Kongo mai arzikin ma'adinai na fuskantar rikice-rikicen kungiyoyin tawaye da suka hada da M23 movement da kuma kungiyar ADF mai alaka da ISIS.

A watan da ya gabata, shugabannin kasashen yankin gabashin Afirka suka aika wata tawagar dakaru domin taimaka wa gwamnatin Kongo yakar 'yan tawaye a yankin gabashin kasar.