Bayanan hoto, Ana samun yawaitar yara da mata masu gudun hijra da rikicin ya ɗaiɗaita tun bayan da ƴan tawayen M23 suka ƙwace iko da Goma, birni mafi girma da albarkatun ƙasa a gabashin jamhuriyar Congo.
Lokacin karatu: Minti 3
Bayanan hoto, Yadda jama'a jama'a ke ɗibar kaya a bayansu sakamakon rikicin da ke ɗaiɗaita su. Da dama na barin unguwanninsu domin tsoron abin da ka iya faruwa tun bayan ƙwace iko da birnin Goma da ƴan tawayen M23 suka yi.
Bayanan hoto, Wata yarinya da ta samu rauni sakamakon rikicin na DR Congo. Yarin tare da iyayenta sun kasance a wani tanti da ke sansani masu neman mafaka.
Bayanan hoto, Nan wasu kabura ne da aka baje su sakamakon rikicin na DR Congo.
Bayanan hoto, Yadda mayaƙan M23 ke sintiri a kan titunan birnin Goma tun bayan ƙwace iko da birnin makonni biyu da suka gabata.
Bayanan hoto, Wasu yara a wani sansanin ƴan gudun hijra da rikicin ya ɗaiɗaita bayan umarnin da ƴan tawayen M23 suka bai wa jama'a na su bar wuraren.
Bayanan hoto, Marasa lafiya a tantin masu neman mafaka ke shirin kwashe kayansu su bar wurin sakamakon umarnin da ƙungiyar ƴan tawayen M23 ta ba su na su bar tantinan kafin daga bisani ta nemi su zauna.
Bayanan hoto, Wasu mata tare da ƙananan yara ɗauke da kaya a hanyarsu ta neman mafaka bayan barin tantinan masu ƙaura.
Bayanan hoto, Mayaƙan M23 na sintiri a birnin Goma mai albarkatun ƙasa.
Bayanan hoto, Nan wata maƙabarta da aka binne mutanen da rikicin ya yi sandiyyar mutuwarsu.
Bayanan hoto, Mayaƙan M23 yayin da suke sintiri a birnin Goma makonni bayan ƙwace iko.
Bayanan hoto, Masu gudun hijra na ƙoƙarin cire rumfunan da tantunan da suke fakewa a cikin bayan umarnin da mayaƙan na M23 suka ba su na su bar wurin.