'Yan Kongo na fuskantar hauhawar laifuka da na farashi ƙarƙashin mulkin M23

An binne mutum 12 da suka mutu a wata fashewar bam yayin gangamin ƙungiyar M23 a makon da ya gabata

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An binne mutum 12 da suka mutu a wata fashewar bam yayin gangamin ƙungiyar M23 a makon da ya gabata
    • Marubuci, Priya Sippy
  • Lokacin karatu: Minti 4

A safiyar wata Juma'a a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), wasu mambobin ƙungiyar M23 na tsaye a kan wani dandamali suna kallon dubban sauran 'yan ƙasar.

Ƙungiyar wadda ta ƙwaci iko da yankin a kwanan nan, ta shirya wani gangami ne a birnin.

Kiɗa na ta tashi daga lasifikoki yayin da wani mawaƙi ke rera waƙar "Congo itajengwa n sisi wenyewe", wadda ke nufin "me kaɗai ne za mu gina Kongo".

Kowa na ta murna yayin da dandazon mutane ke raye-raye tare da tafi. Sai dai babu jimawa hankula suka fara tashi.

Bidiyoyin da aka wallafa a shafukan zumunta sun nuna dubban mutane na gudun tsira saboda ƙarar harbin bindiga da fashewar bama-bamai da ke tashi a birnin.

M23 ta zargi dakarun gwamnatin Kongo da kai harin, sai dai babu wani tabbaci game da wanda ya kai harin.

Waɗanda suka yi magana da BBC sun ce wannan taron ya fito ƙarara da irin halin da ake ciki a hannun M23. Sun ce suna iya yin tafi cikin murna a fili, amma zuciyarsu na cike da fargaba.

Taron na M23 da aka yi a Place de l'indépendance kafin a fara harbe-harbe da fashewar bama-bamai

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Taron na M23 da aka yi a Place de l'indépendance kafin a fara harbe-harbe da fashewar bama-bamai

'An tilasta mana yin aiki'

Mayaƙan da ke samun goyon bayan Rwanda na cewa suna fafutikar neman 'yancin 'yan ƙabilar Tutsi ne, waɗanda su ne tsirari a DRC.

A 'yan makonnin da suka wuce ne suka ƙwace wurare mafiya girma tun bayan fara gwagwarmaya a 2021.

Yanzu suna iko da manyan garuruwa a gabashin DRC: Goma da Bukavu, kuma rahotonni na cewa sun doshi Uvira, wani birnin da ke kudancin Kivu.

Wasu kan ce hatta aikin gyara unguwanni da M23 ke jagoranta a yankunan da take iko da su, tilasta wa mutane suke yi shiga aikin.

"Sun faɗa mana cewa idan ba mu shiga aikin ba, za su yi mana abin da suka yi wa mutane a Goma. An ga yadda ake zalintar mutane a bidiyo. Mu dai tilasta mana aka yi," a cewar wani da ya nemi a sakaya sunansa.

"Cikin tsoro mutane ke tafa wa abin da ke faruwa," in ji wani mazaunin Bukavu a hirarsa da BBC.

Hauhawar farashin abinci

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mazauna yankunan kan ce saboda ƙarancin ƙwarewarsu wajen jagorancin manyan birane, mambobin M23 sun kasa farfaɗo da harkokin kasuwanci.

Wata sanarwa da gwamnatin Kongo ta fitar ta ce za ta saka haraji kan kayayyakin da ke fitowa daga yankunan da M23 ke iko da su, ciki har da Goma, da Bungana, da Ishasha, abin da zai ƙara daƙile hada-hada.

Kafin sanarwar, tuni farashin kayan abinci da na man fetur suka hauhawa saboda ƙalubalen da ake fuskanta wajen shigar da kayan kasuwanni.

Wani mazaunin wurin ya fada wa BBC cewa farashin kilo ɗaya na sikari ya ƙaru daga tsakanin 2,000 da 3,000 CFA zuwa 5000 ko 6000 CFA (kamar dala biyu kenan), wake kuma shi ma ya ninka kuɗinsa.

Binciken da shirin tallafin abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya na World Food Programme (WFP) ya yi ya nuna cewa farashin kayan abincin da aka fi amfani da su kamar fulawa ta tashi da kashi 70 cikin 100.

Shelley Thakral, shugabar sashen hulɗa da jama'a na WFP a DRC ta faɗa wa cewa "suna cikin damuwa sosai" game da tasirin ƙarancin abinci, musamman a kan yara.

"Muna duba yiwuwar kafa wuraren ajiyar kayayyaki don duba abubuwna da za mu sarrafawa mu kawo daga wasu ƙasashen, da kuma abin da za mu iya saya a gida," a cewar Thakral.

Mazauna birnin Bukavu suna hada-hadar kasuwancinsu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mazauna birnin Bukavu suna hada-hadar kasuwancinsu

Thakral ta ƙara da cewa mazauna Bukavu na fuskantar ƙarancin takardun kuɗi yanzu haka.

Har yanzu bankunan da ke ƙarƙashin ikon gwamnati na rufe, yayin da mutane ke kafa dogayen layuka domin samun kuɗi.

"Rayuwa ta yi tsada sosai," a cewar wani ɗanjaridar yankin.

"Mutane na buƙatar kuɗi, amma kuma babu su. Abu ne mai wuya ka samu abinci saboda babu kuɗin saye."

Yayin wani gangami na baya-bayan nan, M23 ta ce za ta ɗauki mataki idan gwamnati ba ta buɗe tare da bai wa sababbin bankuna lasisi ba.

Laifuka ma na ƙaruwa.

A ranar da M23 ta ƙwace birnin, dubban ɗaurarru sun gudu daga babban gidan yari bayan an cinna masa wuta. Har yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba.

Azuzuwa fayau

A duka faɗin Bukavu, yara ƙalilan ne suka koma makaranta.

Wata mazauniyar garin da ke da 'ya'ya huɗu, ta ce tana jiran ganin yadda lamarin tsaron yankin zai sauya.

"Akasarin iyaye sun ƙi yarda su tura yaran nasu makaranta saboda mun samu saƙonni da bidiyoyi daga iyaye a Goma da suka tura yara makaranta kuma aka yi garkuwa da su," in ji ta.

Sai dai, wani jami'in ma'aikatar ilimi a Kudacnin Kivu ya faɗa wa BBC cewa labarin satar yaran ba gaskiya ba ne.

Ya ƙara da cewa ana sa ran za a biya malamai albashinsu a wannan watan.

Yayin da mayaƙan M23 ke nausawa kudanci, mazauna garuruwan sun shaida wa BBC fargabarsu da ke ƙara yaɗuwa.

A cewar rahotonni, ƙungiyar na kusantar birnin Uvira. Mazauna yankin sun ce tuni mutane sun fara guduwa.

"Muna zaune cikin fargaba," in ji wani mazaunin Uvira. "Ba mu san abin da ke shirin faruwa ba, ba mu sani ba ko gwamnati za ta cece mu."

Waɗanda ke zaune ƙarƙashin mulkin M23 a Bukavu ba su da tabbas game da rayuwarsu.

"Halin da muke ciki kenan a yanzu," kamar yadda wani ya bayyana.