Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Rice, Alonso, Phillips, Lingard, Leno, Saliba

Rice

Asalin hoton, Reuters

Declan Rice zai ci gaba da zama a West Ham duk da zawarcin da Manchester United ta rinka nunawa kan ɗan wasan mai shekara 23. (Mirror)

Ɗan wasanChelsea mai buga baya Marcos Alonso, ɗan shekara 31, na son yin bankwana da Stamford Bridge inda ya shafe shekara shida yana taka leda, kuma Barcelona ta yi nisa a tattaunawa da shi. (Fabrizio Romano, Twitter)

Mai bugawa Monaco da Faransa baya Aurelien Tchouameni ya daidaita da Liverpool, sai dai duk da haka kungiyar na fuskantar kalubale wajen cimma yarjejeniya da ɗan wasan mai shekara 22, wanda ita ma Real Mardrid ke hari. (Mirror)

Aston Villa ta sanya ɗan wasan Leeds United da Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 26, a jeren mutanen da take hari a sabuwar kaka. (Telegraph - subscription required)

Real Madrid na son saye ɗan wasan AC Milan Rafael Leao, mai shekara 22, bayan Kylian Mbappe ya yanke hukuncin ci gaba da zama a Paris St-Germain. (Marca)

West Ham ta gabatar da tayinta kan ɗan wasan Manchester United Jesse Lingard, mai shekara 29, wanda kwatiraginsa ke karewa a watan Yuni. Lingard ya zura kwallaye 9 a league din 2020-21. (Mail)

Benfica za ta sayo ɗan wasan Arsenal dan asalin Jamus da ke tsaron raga Bernd Leno. (Correio da Manha - in Portuguese)

Porto ta matsu ta dauko ɗan wasan Manchester United da Brazil Alex Telles, mai shekara 29, a wannan kakar. (Correio da Manha - in Portuguese)

Ɗan wasan Arsenal da Faransa William Saliba, mai shekara 21, na son ya ci gaba da zama a Marseille. (Goal)

Newcastle na aikin ganin ta daidaita da ɗan wasan Faransa mai buga gaba Hugo Ekitike, ɗan shekara 19, da yanzu ke taka leda a Reims - amma tana fuskantar kalubale daga Borussia Dortmund.(Fabrizio Romano, Twitter)

Aston Villa na gab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan Farasna Boubacar Kamara, mai shekara 22, daga Marseille.(Matteo Moretto, Twitter)

Kamara ya kasance ɗan wasan da Atletico Madrid ke zawarci, sai dai matashin ɗan wasan ya fi son ya je kungiyar da zata haska a Champions League a sabuwar kaka. (Football Espana)

Wolves na son dauko ɗan wasan Faransa Thomas Henry, mai shekara 27, da ke taka leda a kungiyar Italiya ta Venezia.(Matteo Moretto, Twitter)

Bournemouth da Sheffield United sun matsu su saye dan wasan Ingila Joe Rothwell, mai shekara 27,da ke shirin bankwana da Blackburn Rovers. (Yorkshire Live)