Manchester City ta lashe Premier League na bana 2021/22

Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta lashe kofin Premier League na bana na takwas jumulla, bayan da ta doke Aston Villa 3-2 ranar Lahadi a Etihad.

Matty Cash ne ya fara ci wa Villa kwallo a minti na 37 da fara tamaula, sannan Philippe Coutinho ya kara na biyu, bayan da suka koma zagaye na biyu.

Cikin minti biyar City ta zura kwallao uku a ragar Villa, inda Ilkay Gundogan ya farke ta farko a minti na 76, minti biyu tsakani Rodrigo Hernandez ya farke na biyu, sannan Ilkay Gundogan ya kara na uku a minti na 81, kuma na biyu da ya ci a karawar.

Wannan shi ne karon farko da aka ci City kwallo biyu a gasar Premier daga baya ta farke ta kuma kara na uku, tun Fabrairun 2005 da ta doke Norwich City 3-2.

Da wannan sakamakon City ta dauki kofin Premier na bana da tazarar maki daya kenan mai maki 92, ita kuwa Liverpool ta biyu ta karkare da 91.

Cikin karawa 38 da kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama ta yi a kakar nan ta ci wasa 29 da canjaras shida aka doke ta wasa uku.

Haka kuma kungiyar ta Etihad ta ci kwallo 99 aka zura mata 26 a raga a bana.

Cikin kofin Premier League shida da City ta dauka, hudu daga cikin biyar a ranar karshe ta yi nasarar lashe shi, kuma karo na tara ana fitar da zakara a fafatawar karshe.

City ta dauki Premier League shida kenan tun bayan da aka sauya masa fasali 2011/12, 2013/14, 2017/18, 2018/19, 2020/21, 2021/22.

Haka kuma wannan ce kaka ta 25 da kungiyar Etihad ke buga babbar gasar tamaula ta Ingila, wadda ta fara dauka a 1936/1937, sai a 1968, sannan ta dauka a lokacin da aka sauya fasalin gasar.