An raba takalmin zinare tsakanin Mohamed Salah da Son Heung-min

Salah and Son

Asalin hoton, Getty Images

An raba takalmin zinaren gasar Premier League tsakanin Mohamed Salah da Son Heung-min a matakin wadanda ke kan gaba a zura kwallaye a raga a bana.

Dan wasan Liverpool, Salah da na Tottenham, Son Heung-min kowanne ya ci 23 a raga a kakar 2021/22.

A ranar ta Lahadi da aka karkare Premier League, Salah ne kan gaba da kwallo daya tsakaninsa da dan wasan Tottenham, Son.

Tottenham ta yi nasarar doke Norwich City 5-0, inda Son ya zura biyu a raga, shi kuwa Salah daya ya ci Wolverhampton a wasan da aka saka shi daga baya, inda Liverpool ta yi nasara da ci 3-1.

Wannan shi ne karo na uku da dan kwallon tawagar Masar, Salah ke lashe takalmin zinare a matakin na daya a yawan cin kwallaye a gasar Premier League.

Salah ya lashe kyautar a 2017/18, inda ya ci 32 da kuma a kakar 2018/19, wanda ya zura 22 a raga.

An raba safar hannu ta zinare tsakanin Ederson da Alisson:

An raba safar hannu ta zinare tsakanin golan Manchester City, Ederson da na Liverpool Alisson, wadanda suka yi wasa 20 kowanne kwallo bai shiga raga ba.

Wasa daya ne Ederson bai tsare raga ba a kakar nan, shi ne wanda City ta yi nasara a kan Burnley da ci 2-0 cikin watan Oktoba.

Shi kuwa golan Liverpool bai tsare raga a fafatawar da kungiyar Anfield ta casa Watford 5-0 da wanda ta tashi 2-2 da Chelsea a Stamford Bridge cikin watan Janairu ba.