Liverpool ta kare matsayinta a gasar Premier

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Salah da Mane na murna yayin cin kwallo

Liverpool ta casa Watford da ci 2-0 ta kuma hada maki 49 a teburin Premier.

Duk da cewa a Anfield aka buga wasan, amma Watford ta fi samun damar zura kwallo a minti 45 na farkon wasan.

A minti na 38 ne da fara wasan Mohammed Salah ya jefa kwallon farko a ragar Watford, abin da ya ba wa Liverpool jan ragamar wasan a minti 45 din farko.

Abdoulaye Doucoure da Ismaila Sarrna na daga cikin wadanda suka samu damar zura kwallon da za ta taimaka wa Watford amma suka gaza amfani da damar.

Bayan cikar minti 90 ne Salah ya kara samun wata dama da yayi amfani da ita ya ci kwallo ta biyu a wasan, wato kwallonsa ta tara kenan a gasar Premier.

Wasa na 33 kenan da Liverpool ta yi ba tare da an samu nasara a kanta ba a gasar Premier, kuma na 17 kenan daga watan Maris din da ya gabata zuwa Oktoba.

Wannan ne lokaci mafi tsayi da kungiyar ta dauka tana wasa a gasar Premier ba a doke ta ba.

Liverpool ta samu nasara a wasanni 99 da ta buga a gida, inda da ta samu galaba a minti 45 din farko, tun bayan cin da Arsenal ta yi mata na 1-2 a Disambar 2009. Ta yi nasara a 90 ta kuma yi canjaras a guda tara kacal.