Uefa da kasashe na yunkurin yi wa VAR garambawul

Filin wasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, VAR ta soke wata kwallo da Sterling ya ci Chelsea a watan Nuwamba

Za a yi garambawul wurin amfani da na'urar VAR yayin duba satar gidan da 'yan kwallo ke yi a kakar wasanni mai zuwa dan wata bukatar hadin gwiwa tsakanin hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa da hukumomin kwallon kafa na kasashe ya yi nasara.

Shugaban hukumar ta Uefa Aleksander Ceferin ya shaida wa jaridar the Times cewa akwai matsaloli game da yaddda na'urar ke taimakawa a fili yayin yanke hukunci.

Uefa za ta yi aiki da wasu kungiyoyi hudu wadanda kowaccensu ke da kuri'a cikin kwamitin dokokin duniya na harkar kwallon kafa.

Duk wani canjin doka da aka samu za'a gabatar da shi ne a yayin taron kwamitin na shekara da zai gudana a Belfast a ranar 29 ga watan Fabariru mai zuwa.

An yi ta samun satar gida masu cike da rudani a wannan kakar a gasar Premier.

Dan wasan Liverpool Roberto Firmino ya ci kwallon da aka hana a wasan kungiyar da Aston Villa ranar 2 ga watan Nuwamba, bayan ganin gefen kafadarsa ya haura layi.

Irin wannan dalilin aka kafa kan wata kwallo da Raheem Sterling na Manchester City ya ci a wasansu da Chelsea a ranar 23 ga watan Nuwamba