An bai wa shugaban riko na Premier aikin dindindin

Richard Masters

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bai wa Richard Masters aikin zai kawo karshen wata 18 da aka shafe ana nemar wa hukumar shugaba

Shugaban rikon kwaryar gasar Premier Richard Masters ya zama shugaban gasar na dindindin.

Hakan na zuwa ne mako biyu bayan shugaban yada labarai na gasar David Pemsel ya yi murabus kafin fara aiki biyo bayan wani zargi da wata jarida ta wallafa a kansa game da rayuwarsa.

Masters wanda shi ne babban daraktan da ke gudanar da hukumar, shi ne mutum na hudu da aka yi wa tayin aikin.

Ya kasan ce yana gudanar da aikinsa na wucin gadi tun bayan tafiyar Richard Scudamore a Nowamban 2018.

Bai wa Masters aikin zai kawo karshen wata 18 da aka shafe ana nemar wa hukumar shugaba.

Tun da farko an sa ran Susanna Dinnage zai gaji Scudamore amma daga baya sai ya yi watsi da tayin, ya gwammace ya ci gaba da aikin a bangaren yada labarai.

Kazalika, babban ma'aikacin BBC Tim Davie ma ya yi watsi da tayin shugabancin.

Masters ya burge kociyoyin kungiyoyi, wadanda ake zaton za su kada kuri'a kan nadin nasa yayin wani taro da za a yi a yammacin Alhamis.