Kai Havertz: Dan wasan da duniya ke rububi

Kai Havertz

Asalin hoton, Getty Images

A yanzu kusan babu wani matashin dan wasa a duniya da kungiyoyi ke rububinsa musamman a Turai kamar Kai Havertz mai shekaru 20 daga kasar Jamus.

Havertz a yanzu na wasa ne a kungiyar Bayer Leverkusen, kuma matashin ya nuna kansa ne a wasannin gasar zakarun turai da na gasar Bundesliga.

Kai Havertz ya fara jan hankali tun a wasannin share fagen gasar nahiyar turai da kuma na sada zumunta, musamman lokacin da Jamus ta casa Estonia da ci 8-0.

Matashin wanda aka haifa a shekarar 1999, ya fara bugawa Jamus wasanni tun a matakin yan kasa da shekaru 16 da 17 da kuma 19.

Haka ma ya fara bugawa babbar tawagar kasar a wasan sada zumunta da ta yi da Peru a watan Yunin 2019.

A yanzu dai manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya tuni sun fara rububin Havertz.

Kungiyoyin kuwa sun hada da Real Madrid da Barcelona da Bayern Munich da kuma Manchester United.

Rahotanni sun ce tuni Manchester United ta ware fam miliyan 80 don taya dan wasan tsakiyar na Bayer Leverkusen, yayin da ake dab da bude kasuwar saye da sayarda yan wasan a watan Janairun 2020.