Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Balotelli, Bellingham, Guardiola, Pogba, Traore

Asalin hoton, EPA
Tsohon dan wasan Manchester City da Liverpool, Mario Balotelli ya fara tattaunawa da kungiyar Barnsley. Dan Italiyan mai shekara 30 ba shi da kungiya tun da Brescia ta kore sshi saboda kin zuwa atisaye. (Sun)
Chelsea na son sayen dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund da Ingila Jude Bellingham, kuma za ta fi amince da dan wasan mai shekara 17 maimakon Declan Rice na kungiyar West Ham mai shekara 21. (Eurosport)
Kocin Manchester City Pep Guardiola bai yanke hukunci ba kan zamansa ko barin kungiyar idan kwantiraginsa ta kare a karshen kakar wasa ta bana. (Goal)
Leicester na sa ido kan dan wasan Portugal Nuno Mendes mai shekara 18 wanda Sporting Lisbon ta sanya wa £40m ga duk kungiyar da ke bukatarsa . (Mail)







