Super Eagles ta ziyarci Saliyo sun kuma tashi ba ci a wasan shiga kofin Afirka

Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Saliyo da ta Najeriya sun tashi 0-0 a wasa na hur-hudu a cikin rukuni a neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka kara ranar Talata.

Da wannan sakamakon Super Eagles ta ci gaba da zama ta daya a teburin rukuni na hudu da maki takwas, ita kuwa Saliyu tana ta uku da maki uku.

Benin ce ta biyu da maki shida, sai Lesotho ta karshe da maki biyu.

Wannan shi ne wasa na biyu da kasashen suka gwabza a rukuni na 12 da ya hada da Benin da Lesotho.

Ranar Juma'a Super Eagles ta karbi bakuncin wasan farko inda tun kan minti 30 ta ci kwallo hudu.

Najeriya ta ci kwallayen ta hannun Alex Iwobi a minti hudu da fara wasa sai Victor Osimhen ya ci na biyu a minti na 21.

Minti shida tsakani Alex Iwobi ya kara na biyu kuma na uku sannan Samuel Chukwueze ya ci na hudu, yayin da Saliyo ta zare daya ta hannun Kwame Quee daf da za a yi hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Saliyo ta kara farke daya ta hannun Alhaji Kamara, sannan Mustapha Bundu ya kara na uku sai Alhaji Kamara ya kara na biyu kuma na hudu a wasan.

Kasashe biyu ne za su wakilci wannan rukunin a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Kamaru a 2022.

Kamaru ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka a 2022, bayan da cutar korona ta kawo tsaikon gudanar da wasannin a 2021.

Masar ce ta karbi bakuncin fafatawar da aka yi a 2019, wacce Aljeriya ta lashe kofin.