Gasar La Liga za ta ci gaba da gudana ko ba Messi

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban gasar La Liga, Javier Tebas ya ce a shirye yake idan Messi zai bar Spaniya - ya kuma soki Manchester City da ake sa ran za ta sayi dan kwallon.
Messi ya bukaci izinin barin Barcelona a cikin watan Agusta - kungiyar da ya je yana da shekara 13 daga baya batun ya lafa, bayan da aka tsawaita yarjejeniyar zamansa a Camp Nou.
Kyaftin din tawagar Argentina ya samu rashin jituwa da Josep Bartomeu - wanda ya ajiye aikin shugabantar Barcelona a cikin watan Oktoba.
Shi dai Tebas na son Messi ya ci gaba da taka leda a Spaniya, amma ya ce ko ba dan kwallon za a ci gaba da gudanar da wasannin.
Shugaban La Liga ya ce Neymar ya bar Spaniya a 2017 daga Barcelona zuwa Paris St Germain, kuma a 2018 Cristiano Ronaldo ya bar Real Madrid zuwa Juventus an kuma ci gaba da buga gasar.
Messi mai shekara 33, yarjejeniyarsa zai kare a karshen kakar bana, daga nan kowace kungiya za ta iya daukar sa.
Tebas ya yi nuni da cewar watakila Messi ya koma buga gasar Premier League a filin wasa na Etihad - koda yake wata majiya ta ce babu wani daga mahukuntan Manchester City da ya yi magana kan sayo Messi.











