Ana karancin zura kwallaye a raga a gasar La Liga ta Spaniya a bana

Football

Asalin hoton, Getty Images

Gasar cin kofin La Liga ta Spaniya ta yi kaurin suna wajen cin kwallaye a kowace kakar tamaula, sai dai a bana ta ci karo da koma baya.

Yadda alkaluma suka nuna da fara kakar 2020/21, Spaniya ce ta kasa a karancin zura kwallaye a raga a manyan gasa biyar ta Turai.

A kakar shekarar nan a Serie A da Premier League da Bundesliga da Ligue 1, an samu sakamakon wasa kamar 7-2 ko 5-2 ko 3-3 ko kuma 4-2, amma a La Liga an fi samun 1-0 da yawa ko kuma 0-0.

An samu gagarumin sauyi a bana, inda Gasar Serie A, wacce ta yi kaurin suna wajen tsare baya, yanzu tana kan gaba a cin kwallaye.

A gasar ta Italiya ana cin kwallaye matsakaici 3.41 a kowanne wasa a kakar 2020/21.

Ta biyu ita ce Bundesliga da ake cin kwallaye 3.21 matsakaici a duk wasa.

Sai gasar Premier League ta uku da ake zura kwallaye 3.14, sai ta Ligue 1 da ake cin kwallaye 2.82 a duk wasa.

Gasar La Liga ita ce ta biyar da ake cin kwallaye 2.41 a kowacce karawa.

Wannan sakamakon a gasar Spaniya shi ne mai muni tun bayan kakar tamaula ta 2008/09.

A kakar 2017/18 an zazzaga kwallaye a raga a kowanne wasa a Spaniya 2.69, sai dai kuma a 2018/19 aka ci kwallaye 2.59.

A kakar bara da aka karkare a La Liga wadda aka ci karo da cutar korona, an zura kwallaye a raga a kowane wasa 2.48.

Gasar Premier League ta Ingila

An buga wasa 78

An ci kwallo 245 (3.14 kowanne wasa)

Wadanda ke gaba a cin kwallaye da takwas-takwas:

  • Dominic Calvert-Lewin
  • Mohamed Salah
  • Son Heung-min
  • Jamie Vardy

Wasannin mako na tara da za a buga a Premier League

Ranar Asabar 21 ga watan Nuwamba

  • Newcastle United da Chelsea
  • Aston Villa da Brighton & Hove Albion
  • Tottenham da Manchester City
  • Manchester United da West Bromwich Albion

Ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba

  • Fulham da Everton
  • Sheffield United da West Ham United
  • Leeds United da Arsenal
  • Liverpool da Leicester City

Ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba

  • Burnley da Crystal Palace
  • Wolverhampton Wanderers da Southampton

Gasar Bundesliga ta Jamus

An buga wasa 63

An ci kwallaye 202 (3.21 kowanne wasa)

Wanda ke gaba a cin kwallo 11

Robert Lewandowski

Wasannin mako na takwas da za a buga a Bundesliga

Ranar Asabar 21 ga watan nuwamba

  • Arminia Bielefeld da Bayer 04 Leverkusen
  • FC Bayern Munich da Werder Bremen
  • Borussia Monchengladbach da FC Augsburg
  • FC Schalke 04 da VfL Wolfsburg
  • TSG 1899 Hoffenheim da VfB Stuttgart
  • Eintracht Frankfurt da RB Leipzig
  • Hertha Berlin da Borussia Dortmund

Ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba

  • SC Freiburg da FSV Mainz 05
  • 1. FC Koln da Union Berlin

Gasar La Liga ta Spaniya

An buga wasa 83

An ci kwallaye 200 (2.41 kowanne wasa)

Wadanda ke gaba a cin kwallo 6

Mikel Oyarzabal

Wasannin mako na 10 a gasar Spaniya

Ranar Juma'a 20 ga watan Nuwamba

  • Osasunada Huesca

Asabar 21 ga watan Nuwamba

  • Levante da Elche
  • Villarreal da Real Madrid
  • Sevilla da Celta de Vigo
  • Atletico Madrid da FC Barcelona

Ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba

  • SD Eibarda Getafe
  • Cadiz da Real Sociedad
  • Granada da Real Valladolid
  • Deportivo Alaves da Valencia

Ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba

  • Athletic Bilbao da Real Betis

Gasar Serie A ta Italiya

An buga wasa 70

An ci kwallaye 241 (3.44 kowanne wasa)

Wanda ke kan gaba a cin kwallaye 8

Zlatan Ibrahimović

Wasannin mako a takwas a gasar Serie A

Ranar Asabar 21 ga watan Nuwamba

  • Crotoneda LazioMatch details
  • Spezia da Atalanta
  • Juventus da Cagliari

Ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba

  • ACF Fiorentina da Benevento
  • Inter Milan da Torino
  • AS Roma da Parma
  • Sampdoria da Bologna
  • Hellas Verona da Sassuolo
  • Udinese da Genoa
  • Napoli da AC Milan

Gasar Lique 1 ta Faransa

An buga wasa 98

An ci kwallaye 276 (2.82 kowanne wasa)

Wanda ke kan gaba a cin kwallaye 8

Boulaye Dia

Wasannin mako na 11 a gasar Ligue 1

Ranar Juma'a 20 ga watan Nuwamba

  • Stade Rennais da Bordeaux
  • AS Monaco da Paris Saint-Germain

Ranar Asabar 21 ga watan Nuwamba

  • Stade brestois da Saint Etienne
  • Olympique Marseille da Nice

Ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba

  • FC Nantes da FC Metz
  • Montpellier da RC Strasbourg
  • FCO Dijon da Racing Club de Lens
  • Stade Reims da Nimes Olympique
  • Angers da Olympique Lyonnais
  • Lille da Lorient