Cannes: Yadda taurarin Bollywood suka mamaye bikin baje-kolin fina-finai na duniya a Faransa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Suparna Sharma
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
Masana'antar fina-fianan Indiya ta Bollywood ta tattara bisa alfahari a fagen cinima ranar Talata yayin da tauraruwa Deepika Padukone ta shiga cikin kwamatin alƙalan bikin Cannes International Film Festival karo na 75 a Faransa.
Kwamatin ƙarƙashin jagorancin tauraron fim ɗan Faransa Vincent Lindon, zai kalli fim 21 kuma su zaɓi ɗaya da zai lashe kyautar Palme d'Or, kyauta mafi daraja da ake lashewa a harkar fim a duniya.
Ms Padukone mai shekara 36 wadda ta fi dukkan 'yan fim din Bollywood albashi, an san ta da rawar da ta taka a fina-finan Padmaavat, Piku da Gehraiyaan, kuma nan gaba kaɗan za ta fara kallon fina-finan "don jin daɗin ƙirƙira da kuma jin daɗin yanayin".
Ms Padukone ce za ta zama tauraruwar fina-finan Indiya da za a fi ɗauka a hoto a bikin baje-kolin fina-finai na Cannes, amma ba ita kaɗai ba ce za ta halarcia taron da ake gani a matsayin mafi kima a duniyar fina-finai.

Asalin hoton, Getty Images
Kusa da inda Ms Padukone za ta zauna ta kalla kuma ta yi wa fina-finai hukunci, akwai wata tawagar 'yan fim da za ministan yaɗa labarai na Indiya zai jagoranta tare da ɗan jarida Anurag Thakur, waɗanda za su nemi masu zuba jari a harkokinsu a Marché du Film, kasuwar fim mafi girma da ke ci tare da bikin na Cannes.
Duk watan Mayu, wurin shaƙatawa na Cannes da ke yankin Riviera na Faransa na samun tagomashi, inda yake shiga halin dabdala 'yan kwanaki kafin fara bikin.
Dabdalar da ke faruwa duk shekara abu ne mai yiwuwa yayin mutum 120,000 ke hallara a garin da bai wuce na mutum 74,000 don shaida bikin.
Amma wannan shekarar, saboda birnin na farfaɗowa daga annobar korona, wani abu ne sabo zai faru.
A wannan shekarar, Indiya da ta fi kowace ƙasa samar da fina-finai, an ba ta matsayin "Ƙasa ta Musamman" a Marché du Film.
A matsayinta na ƙasar farko da aka taɓa ba wa wanna matsayi, za a bai a Indiya filin ta nuna basirarta. Daraktoci na Indiya da masu shirya fina-finai za su samu damar tallata fina-finansu don neman masu zuba jari ga sabbin 'yan kasuwa.
"Indiya na da labarai da yawa da za su iya bayarwa kuma ƙasar na da cikakkiyar basirar da za ta zama cibiyar haɗa fina-finai ta duniya," a cewar Mista Thakur cikin wani saƙon Twitter yana mai ambato Firaminsitan Indiya Narendra Modi.
Wani fim da za a gabatar yayin bikin shi ne Rocketry: The Nambi Effect.
Fim ɗin da ya ƙunshi sabon tauraro R. Madhavan, an shirya Rocketry ne kan wani injiniyan roka mai suna Nambi Narayanan, wanda aka tuhuma da leƙen asiri, aka kama shi, aka tsangwame shi sannan daga baya aka wanke shi.
Bikin Cannes da ake yi tsakanin 17 zuwa 28 ga watan Mayu, na ƙunshe da sabbin fina-finai daga shahararrun taurarin Hollywood (kamar Top Gun: Maverick na Tom Cruise, Elvis na Baz Luhrmann), da kuma wasu daga shahararrun jarumai kamar Javier Bardem da Mads Mikkelsen.
Fim ɗin The Adversary) na Satyajit Ray da The Circus Tent na Pratidwandi da G. Aravindan za a haska su yayin bikin, wanda tuni tikitin zuwa ya fara wuya.
Amma babban abin farin ciki ga zuwan Indiya wanan biki a yanzu shi ne fim ɗin documentary na wasu 'yan uwa biyu da ke zaune a birnin Delhi da aka shirya kan ceto rayuwar tsuntsaye - musamman shirwa - wadda gurɓacewar yanayi ke kashewa.
Fim ɗin na Shaunak Sen mai suna All That Breathes da aka fara haskawa a bikin Baje-Koli na Sundance a farko shekarar nan, za a tantance shi a matsayin wani ɓangare na bikin.
"Ban zaci fim ɗin zai kasance a Cannes ba, saboda mun yi sa'ar ƙaddamar da shi a bikin Sundance kuma muka yi nasara, kuma abu ne da ba a saba gani ba wani fim da aka riga aka nuna a baya ya samu shiga Cannes...muna cike da murna," kamar yadda Sen ya faɗa wa BBC Africa.
All That Breathes na cikin fina-finai 12 da za a haska a Cannes da ba sa cikin gasar, ciki har da Jerry Lee Lewis: Trouble in Mind na Ethan Coen.
Wani fim na Indiya da ke cikin jerin Cannes shi ne Nauha, wanda Pratham Khurana ya shirya. Nauha na nufin "makoki" a harshen Hindi, kuma an shirya shi ne kan wani yaro da ke kula da wani dattijo mai shekara 75.
An tsamo shi daga cikin fina-finai 1,500 da suka miƙa buƙatar neman shiga gasar daga faɗin duniya, kuma ya samu shiga finap-finai 16 da ke fafatawa a gasar.
A gefe guda kuma, Ms Padukone ta shirya tsaf wajen fara aikinta a majalisar alƙalan, kamar yadda suka bayyana. Suka ƙara da cewa "za ta manta da duk wani nauyi da ke kansu" wajen zaɓo gwarzon fim kuma a madadi hakan "za ta mayar da hankali kan masu kallo...".
"Ina ganin sinima babbar hanya ce ta aika saƙo. Tana da damar yin tasiri da kuma sauya rayuwar mutane," a cewa Padukone.











