Makiya fina-finan Indiya da ke watsa labaran karya kan taurari a YouTube
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Wani bincike da sashen binciken kwakwafa na BBC Disinformation Unit ya gudanar bankado yadda ake amfani da shafin YouTube domin yada labaran karya kan taurarin fina-finan Indiya.
Masu fada a ji a shafukan sada zumunta irin su YouTube wadanda suke da dimbin mabiya, suna kan gaba wajen yada kiyayya, da zarge-zarge da kalaman batanci kan taurarin fina-finan Indiya - kuma suna samun makudan kudade daga wannan harkar.