Priyanka Chopra ta bayyana yadda rayuwa ta kasance ma ta bayan aure

Bayanan bidiyo, Priyanka Chopra ta bayyana yadda rayuwa ta kasance mata bayan aure

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Fitacciyar ƴar fim din Bollywood Priyanka Chopra Jonas ta saki tarihin rayuwarta da ta rubutawa, inda ta bayyana labaran da suka shafi zama shahararre da yadda al’umma ke kallonta, da batun aurenta da mawaƙi Nick Jonas.

Kullen annobar cutar korona ya rutsa da ƴar fim ɗin a Landan tun watan Nuwamba lokacin da ta je ɗaukar sabon fim ɗinta.