Pakistan ta dakatar da tattaunawa da Taliban

Asalin hoton, AP
Wakilan gwamnatin Pakistan sun ce an dakatar da tattaunawar sulhu da 'yan kungiyar Taliban.
Wani jami'i ya ce suna jiran karin bayani daga 'yan Taliban na Pakistan a kan wakilinsu a kwamitin da kuma yadda za a yi tattaunawar.
Wani dan Taliban na Pakistan ya ce sun ji takaicin wannan matakin.
Firaministan Pakistan, Nawaz Sharif ya ce yanason kawo karshen zubar da jini, amma idan tattaunawar taki za su dauki matakin soji.
Kungiyar Taliban ta Pakistan hadaka ce ta masu tsatsauran ra'ayin Musulunci wacce keson kafa doka shari'ar Islama.
An kashe fararen hula da jami'an tsaro fiye da 1,200 a bara sakamakon hare-hare 'yan Taliban a Pakistan.






