An kashe masu aikin Polio a Pakistan

Asalin hoton, AFP
An kashe mutane bakwai a Pakistan a wani harin bom da aka kai wa jami'an tsaron ma'aikatan rigakafin Polio a arewa maso yammacin kasar.
Harin ya kashe 'yan sanda shida da yaro daya a garin Charsadda.
Akalla wasu mutanen tara ne kuma suka jikkata.
Harin na zuwa ne kwana guda bayan dakatar da rigakafin Polio a birnin Karachi dake kudancin kasar sanadiyyar kashe masu aikin rigakafin su uku.
A baya dai 'yan bindigar Taliban sun yi ikirarin kashe jami'an kiwon lafiyar saboda kallon da suke wa aikin rigakafin Polio a matsayin mafakar 'yan leken asirin kasashen duniya.






