Polio: An kashe 'yan sanda biyu a Pakistan

'Yan sanda a arewa maso yammacin Pakistan sun ce an harbe jami'anta biyu a kan hanyarsu ta baiwa ma'aikata diga Polio kariya.
An kaiwa mazan hari ne lokacin suna tafiya a kan babur a garin Topi dake da nisan kilomita 100 daga Peshawar.
'Yan Taliban na kallon shirin bada allurar Polio a matsayin wata hanya da kasashen waje ke yi wa kasarsu leken asiri.
Mayaka a Pakistan sun kashe fiye da ma'aikatan bada Polio 12 a cikin shekara guda.
Kawo yanzu babu kungiyar da ta amsa kai wannan harin.






