An kaiwa masu aikin Polio hari a Pakistan

Akalla mutane biyu cikinsu har da wani jami'in dan sanda, sun rasa rayukansu a wani harin bam din da aka kai kusa da ofishin yaki da cutar shan inna ko Polio, a Penshawar dake Pakistan.
Yayin da wasu mutane 12 suka jikkata, kuma rahotanni sun ce mafi yawansu 'yan sanda ne, amma an nuna wata yarinyar da ta ji rauni a hoton bidiyon harin.
Rahotanni sun ce tawagar dake cikin motar da aka kaiwa harin, na rakiyar ma'aikatan polio ne domin basu kariya.
Masu ta da kayar baya dai sun kai hare-hare a kan ma'aikatan rigakafin shan inna, tare da haramta ayyukansu a wasu yankunan kasar, lamarin da ya sa dole ba a samu yiwa dubban yara rigakafin ba.






