Za a kafa kwamitin tattaunawa da Taliban

Firaministan Pakistan, Nawaz Sharif ya ce zai kafa kwamiti mai wakilai hudu da zai tattauna da 'yan Taliban na kasar.
A jawabinsa ga majalisar dokoki a karo na uku tun zabensa a bara, Mr Shariff ya ce yanason a samu zaman lafiya a maimakon kaddamar da yaki a kan tsageru.
A bana kungiyar Taliban ta kashe mutane fiye da 100 a hare-haren da ta kai a Pakistan .
Masu sharhi na kallon shugabanni a kasar sun gaza wajen kawo karshen matsalar tsaro.






