Pakistan: 'Yan Taliban sun kashe soja 20

Asalin hoton, Reuters
'Yan sanda a Pakistan sun ce, harin bam da aka kai akan wani jerin gwanon motocin soja ya hallaka soja akalla ashirin a yankin arewa maso yammacin kasar.
Wasu sojan fiye da talatin sun jikkata.
Harin dai ua auku ne yayin da ayarin motocin dake dauke da sojan ke barin wani bariki a yankin arewacin Waziristan da ya jima yana fama da tashin hankali.
Reshen Pakistan na kungiyar Taliban ya dauki alhakin kai harin.
Kungiyar Taliban dama dai tayi alwashin zafafa hare-hare akan jami'an tsaro.






