Dabarun zubar da ciki na ƙarya da ake yaɗawa a intanet

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Rachel Schraer
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC kan kiwon lafiya da labaran karya
Missy daya ce daga cikin mata miliyan 90 da aka yi kiyasin suna zaune a kasar da aka haramta zubar da ciki.
Rashin kudin sayen magani a kasuwar fage domin zubar da cikin a kasar Philippine, ya sanya ta shiga intanet domin neman shawarar yadda za ta yi, ta ci karo da wasu bayanai kan yadda za ta hada abin zubar da ciki a gida da kuma wasu magunguna.
Bayan bincike a Google da dandalin Facebook, Missy ta yanke shawarar fara gwada abin da ta gani wato amfani da ganye ta hanyar cusawa a Farjin ta, da gahawa mai karfin gaske da kuma man jikin aloe vera, babu wata shawarar likita, kuma ba hanya ce sahihiya ta zubar da ciki ba.
"Mako guda bayan amfani da wanna hadin, babu abin da ya faru" in ji Missy. "Babu abin da ya haddasa min sai gudawa da matsanancin ciwon kai."
Amfani da hadin gargajiya
Kungiyar da ke yaki da kiyayya ta intanet (CCDH) ta gano a kasashe 48, da zarar ka shiga Google ka rubuta "yadda za a zubar", kafin ka karasa rubuta sauran bayanin za ka ga hanyoyin zubar da ciki ta amfani da wasuu abubuwa a gida za su fito, ciki har da amfani da danyen kwai ko kuma ruwan gishiri.
Har wa yau, babu wani bayani kan ko hanyoyin za su iya zubar da cikin.

Asalin hoton, CCDH/ Google
Google ya amince da abubuwan da aka zayyana, tare da cewa yana aiki tukuru don ganin an kauce sanya abubuwan da za su cutar da mutane, har ma ya kafa wata tawagar ma'aikata da ke duba irin wadannan sakwanni.
A kasashe da dama kamar su Afirka ta Kudu da Kenya da Indiya da Philippines da Poland da Ukraine da Australia da Birtaniya da Amirka duka ana bincike kan yadda za a zubar da ciki.
Toshe bayanan gaskiya kan yadda za a zubar da ciki
A bangare guda kuma, wadanda suke zubar da ciki na gaskiya sun shaidawa BBC suna kokarin rufe bayanan yadda ake yi ko magunguna ko hanyoyin zubar da cikin ke gudana a shafinsu na intanet, ba kuma tare da sun yi karin bayani ba:
- Daya daga cikin manyan wuraren zubda ciki na duniya da ake kira MSI Reproductive Choices, suna da shafin Youtube, wanda aka dakatar na makwanni da sakwannin Facebook har da Google, da shi ne mamallakin Youtube ya ce an samu matsala ne amma yanzu an bude shafukan
- Kungiyar iyaye ta kasa da kasa (IPPF), wadda ke wakiltar kasashe 146, ta ce ta dan dakatar da talla a google da facebook na dan lokaci
- Kungiyoyi da dama da ke taimakawa mata da maganin zubar da ciki, ciki har da kungiyar Women On Web da ke aiki a kasashe 200, ta wallafa bayanan yadda aka yi ta rufe shafinta na intanet.
Google ya ce yana da ka'idojin da ake amfani da su musamman wajen binciken abin da ya shafi zubarda ciki, wasu daga cikin dokokin yankin da mutum yake ne ke sanya su wasu kuma na google din ne.
Shi ma Facebook ya ce an cire wasu daga cikn tallace-tallacen da ba su dace ba.
Idan ana batun tallan da ya ke fara fitowa a cikin jeri wadanda ake da su, Google ya ce wannan ya danganta da wanda ya fara biyan kudi, amma duk da hakan suna duba abin da ya dace.
Sai dai MIS sun ce sun ga irin wadannan tallace-tallace da ba su dace ba sun sake bullowa da zarar ka shiga sashen binciken Google.
Amfani da magani da hanyar hadawa a gida
Missy ta ce ta yi amfani da hanyoyi da dama domin ganin ta zubar da cikin ke da ke jikinta.
MIS ya ce yana bibiyar dukkan bayanan da ake tattaunawa ta dandalin intanet, inda mutane ke tallan hajarsu ta magungunan zubar da ciki kama daga na asibiti har gargajiya.
BBC ta ga bayanan mutane daban-daban a shafin Facebook, da matan da suka bukaci hadin gida domin zubar da ciki cikin gaggawa, wasu na sake dawowa dandalin su yi korafin bai yi aiki ba, sai kuma su kara haduwa da wasu da za su ba su maganin asibiti.
Mara Clarke, shugaban kungiyar agaji ta Abortion Support Network wadda ke taimakawa mata da zubar da ciki, da kuma suke amfani da magungunan da suka dace ga matan.
"Babban abin damuwar shi ne, daya daga cikin magunguna masu arha da ake amfani da su wajen zubda ciki a asibiti wato Misoprostol da Mifepristone, arharsa ta janyo ana amfani da shi sosai sannan za a iya, sayar da maras kyau ga matan".
Sannan shafukan da za ka ga ana tallansu ka iya zama na 'yan damfara ne, "damfarar ka za su yi sai ka aika da kudi, magani ya ki samuwa ko ma su toshe ka daga shafin," in ji Clarke.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu daga cikin matan da ke dandalin sun ce suna zaune a kasashen da aka haramta zubarda ciki, suna kuma ganin wannan ita ce hanya daya tilo da za su bi wajen samun waraka, ta ganin magungunan da ake tallansu ta intanet, musamman matan Afirka ta Kudu.
"An amince? to haka ne, amma duk da hakan ana nuna kyama," in ji Miss Chinogwenya MSI.
"Idan ka dubi wuraren da ya kamata ace suke aikin zubda ciki, ba lallai ka samu wasu karin bayanai akai ba.
"Batun shi ne samun hanyar, ba wai samun magani ba samun bayanai yana da muhimmanci".

Asalin hoton, Getty Images
Karin bayanan karya kan zubda ciki
Bayanan karya da shawarwari kan fannin lafiya da zubar da ciki sune manyan kalubalen da ake fuskanta a shafukan intanet.
Abigal Sambo, matashiya a Lusaka, Zambia wanda ke aikin sa kai kan wayar da kan matasa kan ilimin jima'i, ta ce ta san mutane da dama da suka yi amfani da hanyoyin gida kamar amfani da ganyen rogo wajen cusawa a farji, da tafasa lemon kwalba na garin rogo Coca-Cola.
Tana aiki da kungiyar ci gaban matasa, wadda ke bai wa mutane bayanai kan yadda za su yi amfani da maganin tsarin iyali domin kaucewa daukar cikin da ba a shirya ba, wanda kuma hakan amintacce ne a kasar Zambia.
Wadannan matasa ne da ba su da wata hanyar amfani da intanet, maimakon hakan suna samun bayanan komai daga wurin kakanninsu mata da sauran mutane.
Bambancin shi ne intanet ta fi yada bayani cikin sauri, sannan samun magani da biyan kudi cikin sauri da sirri, sannan hakan rufin asiri ne ga masu kudin da ba sa son a san halin da suke ciki.
Yayin da kamfanonin ke sahun gaba tsakanin masu ''matsala da saida magani'' da wallafa bayanan da suka ga dama, a bangare guda kuma sun zama kaifafan takubban da ke sara ta kowanne fanni.












