Roe v Wade: Me ya sa dokokin zubar da ciki ke haddasa zanga-zanga a Amurka?

Asalin hoton, Getty Images
Wasu takardun da aka bankado na cewa Kotun Kolin Amurka na iya sauya dokar da ta amince wa 'yan kasar su zubar da ciki, matakin da ya haddasa zanga-zanga daga masu goyon bayan zubar da ciki da wadanda ke adawa da matakin.
Shafin intanet na mujallar Politico ya bankado wani daftarin ra'ayin Mai Shari'a Samuel Alito, wanda ke cewa "an yi babban kuskure" a muhimmin hukuncin da aka yanke na Roe v Wade a 1973, kuma ya ce ya kamata a soke shi.
Idan Kotun Kolin Amurka ta soke wannan hukuncin, zubar da ciki zai zama laifi a jihohi 22 na kasar. A watan Yuli ake sa ran bayyana sabon hukuncin.
Saboda haka mene ne ne tasirin daukar wannan matakin?
Mene ne aka bankado?
Mujallar Politico ta wallafa wani rahoto da ke cewa Mai Shari'a Alito ya rubuta wani "cikakken ra'ayi na soke dokar" cikin wani daftarin hukuncin da zai kasance matakin da Kotun Kolin za ta dauka.
Mujallar ta ruwaito Alito na cewa "Lokaci ya yi da za a koma ga abin da tsarin mulki ya nufa kuma a mayar da batun zubar da ciki ga wakilan da al'umma suka zaba."
Wannan batun bankado bayanai ba kasafai yakan faru ba a Kotun Kolin Amurka, kuma Amurkawa sun yi mamaki cewa yawancin alkalan Kotun na iya sauya hukuncin wanda ya zama ginshikin da masu zubar da ciki a kasar ke dogara da shi.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai wasu masu shari'a hudu da ake zaton za su mara wa Alito baya; Clarence Thomas da Neil Gorsuch da Brett Kavanaugh da kuma Amy Barret.
Dukkansu alkalai ne da jam'iyyar Republican ta nada. Sai dai babu wanda ya san inda Mai Shari'a na shida John Roberts ya karkata kan batun.
Mujallar Politico ta ce su kuwa alkalai ukun da jam'iyar Democrat ta nada - Stephen Breyer da Sonia Sotomayor da Elena Kagan - na kokarin bayyana nasu ra'ayin da zai ci karo da na masu shari'ar da ke goyon bayan alkali Alito.
Wane ne Samuel Alito?
Mai Shari'a Samuel Alito na cikin alkalai shida na Kotun Kolin Amurka da shugabannin kasar 'yan jam'iyyun Republican suka nada.
Ana kallon Mai Shari'a Alito a matsayin daya daga cikin alkalai mafiya tsattsauran ra'ayi a Kotun Kolin.
Yayin wani jawabi da ya yi a watan Nuwambar 2020, mai shari'ar ya soki auren-jinsi, kuma ya soki dokokin da ke bai wa mata damar zubar da ciki inda ya kara da cewa matakan hana cutar korona yaduwa na take 'yancin fadar albarkacin baki da na addini da tsarin mulkin Amurka ya tabbatar wa 'yan kasar.
Masu sukar lamirinsa na cewa ya karkata gefe guda kan muhimman abubuwa saboda haka ba zai yi adalci ba.
Me ake nufi da Roe v Wade?

Asalin hoton, Getty Images
Roe v Wade wata shari'a ce da Kotun Kolin Amurka ta yanke hukunci a kai a 1973 wadda ta ba matan Amurka damar zubar da ciki idan sun so.
Shari'ar ta shafi wata mata mai suna Norma McCorvey, wadda aka sakaya sunanta da Jane Roe, wadda ta dauki ciki a 1969 na danta na uku.
Ms McCorvey ta so ta zubar da cikin amma dokar jiharta ta Texas ta hana yin haka. Daga nan ne ta kai karar jihar a kotu.
Hukuncin ya ba mata damar zubar da ciki idan bai wuce watanni uku na farkon shigar cikin ba.
'Yaki ne na siyasa'
Yayin sauraren wata shari'a daga jihar Mississippi a watan Disambar bara, Mai Shari'a Sotomayor ta yi gargadi kan mayar da batun ya zama na siyasa.
Ta gaya wa sauran Alkalan Kotun cewa: "Shin wannan Kotun za ta iya wanke kanta daga laifin da al'ummar kasa za su dora mata cewa ta mayar da muhimman batutuwa zuwa na siyasa ne?"
Ta amsa tambayar da kanta: "Ina ganin ba abu ne mai yiwuwa ba."

Asalin hoton, Getty Images
Wa wannan hukuncin zai fi shafa?
Hana mata zubar da ciki zai fi shafar talakawan cikinsu - wadanda dama su ne suka fi kokarin zubar da ciki tsakanin matan kasar.
Lamarin zai kuma shafi mata bakaken-fata da mata 'yan asalin Latin Amurka - inda kashi 6 cikin 100 na masu zubar da ciki daga cikin wadannan al'umomin suka fito.
A shekarar 2019, cibiyar da ke yaki da da cututtuka masu yaduwa ta Amurka ta ce matan kasar 630,000 ne suka zubar da ciki. An sami karuwar kashi 18 cikin 100 ke nan idan aka kwatanta da shekarar 2010.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan da aka wallafa daftarin, masu goyon bayan zubar da ciki, da wadanda ba sa goyon bayan zubar da ciki sun hallara a wajen ginin Kotun Kolin Amurka da ke birnin Washington DC.
Wadanda ba sa goyon bayan zubar da ciki sun ji dadin wannan matakin, kuma sun rika yin maci suna cewa "A soke hukuncin Roe vs Wade".
Su kuma masu goyon bayan zubar da ciki na cewa "Jikina ne, zabina ne".
Wata mata cikin masu zanga-zangar, Emma Heussner, ta ce "ba gudu ba ja da baya kan batun kare rayukan 'ya'yan da ba a haifa ba." Ta ce ta halarci wannan taron ne domin "kafa tarihi."
Ita kuwa Rabaran Wendy hamilton 'yar jam'iyyar Democrat mai son tsayawa takarar mukamin 'yar majalisar wakilai ta kasar, ta ce a shirye take ta kare muradun mata na zubar da ciki.
"Ba za mu bari su yi nasara ba. Ba za su yi wa Amurka haka ba. Mun fi su yawan al'umma, kuma za mu yaki wannan batun."










