Labarai biyar na matan da suke zubar da ciki a duniya

Asalin hoton, Getty Images/BBC
- Marubuci, Daga Pooja Chhabria
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Ko ya kamata a halatta zubar da ciki? Wannan tambaya ce da ake ci gaba da yin muhawara a kanta a fadin duniya.
A jihar Texas ta Amurka, an fara amfani da wata doka ta haramta zubar da ciki a mako shidan farko. Yayin da a jihar Coahuila ta Mexico kuwa ake kara samun karuwar haramta zubar da cikin.
"Maganar gaskiya ita ce samun hanyar zubar da ciki a ko yaushe ba shi da tabbas," a cewar Anu Kumar, shugabar wata kungiya ta fafutukar hakkokin haihuwa mai cibiya a Amurka.
Amma ta yi amannar cewa abubuwa na tafiya yadda ya dace. "Tun shekarar 1994, fiye da kasashe 40 sun sassauta dokokinsu na zubar da ciki," ta kara da cewa.
Baya ga wannan muhawarar akwai mutanen kuma da suke adana sirrukan zubar da cikinsu.
A wannan ranar ta zubar da ciki ta duniya ba tare da matsala ba, mun tambayi mata biyar su ba mu labarinsu na yadda suka zubar da ciki. Sun fito daga wurare daban-daban a duniya, wasu daga cikinsu sun so a boye sunayensu.
'Nan da nan na gane cewa ba na son wannan mutumin ya kasance mahaifin dana'- Sandra, Bangok
Sandra ta fara jin sauyi a jikinta yayin da take dauke da cikin sati takwas. Ta yi gwaji ya tabbatar mata tana dauke da ciki.
"Nan da nan na san cewa ba na son wannan mutumin a matsayin baban dana," ta fada wa BBC. "Kawai abokin jima'ina ne', kuma aikina ya fi komai muhimmanci a wurina.
Ta san labarin kungiyar Tamtang a Thailand, da ke taimakawa da bayanai kan hanyar zubar da ciki marar hadari, sai ta yi masu magana su taimake ta. "Na nemo asibitin amma sai na fara jin tsoro kwana daya kafin aikin.
Kafin wannan lokacin, zubar da ciki haramun ne a Thailand sai dai idan an samu cikin ne ta hanyar fyade ko dan uwa na jini, ko kuma lafiyar maman na cikin hadari. Sandra ta yanke hukuncin zubar da ciki tun wadannan dokokin na aiki.
"Ina ta tunani- na fada masu cewa fyade aka yi min, ko kuma za su ji tausayina idan na ce masu ba zan iya biya ba? Ba abin da ban yi tunani ba," in ji ta.

Asalin hoton, Getty Images
A ranar, ta amsa tambayoyi don bayyana masu damuwar da take ciki. Amma ta yi tunani idan kasancewarta 'yar shekara 27 mai samun kudaden shiga zai zama mata matsala.
"Na kasance ni kadai kuma na yi tunanin babu mai ba ni uzuri," in ji ta.
"Na kasa fadawa aminiyata saboda a al'adarmu, akwai camfe-camfe kan da zubar da ciki. Akwai wani shiri a talbijin da ke yada ra'ayin cewa matar da ta zubar da ciki za ta goyi fatalwar jaririnta aa tsawon rayuwarta."
Ta dan samu kwanciyar hankali bayan ta shiga dakin tiyatar."A cikin minti 15 aka gama, bayan na dan huta kadan, na tuka kaina zuwa wajen aiki."
"Na yi ta fada wa kaina cewa babu komai- har sai ranar da na ga wasu mugayen maganganu kan zubar da ciki a soshiyal midiya kawai sai na fashe da kuka."
Ta ce tana fatan mata za su iya samun cikkaken 'yanci na jikinsu wata rana. "Saboda duk da akwai sabbin dokoki, akwai tsangwama da dama da ke damun mu."
'Yawaita magana a bayyane game da zubar da ciki zai karfafa al'ummominmu'- Erin, Amurka
Erin tana shekara 28 a lokacin da ta zubar da ciki a karon farko, na baya-bayan nan tana shekara 36. "Da ina tunanin cewa na fita daban don 'na zubar da ciki sau da dama," ta fada wa BBC.
"Amma a cikin wannan aikin nawa na fafutukar zubar da ciki, na koyi cewa zubar da ciki ba sabon abu ba ne."
Amma ta yi imanin cewa yawan zubar da cikin bai rage tsangwama da ake yi ba idan mutum ya zabi yin hakan. "Har yanzu ana kyamar magana a kai, ko a cikin kungiyoyin da suka ci gaba da al'ummoin da ke kare hakkin haihuwa," ta ce. "Ina fatan hakan zai canja da wuri."
Erin na fafutukar hakkokin haihuwa a wata kungiya da ke Amurka da ake kira Shout Your Abortion. Ta ce ya taimaka mata wajen yin magana a kan zubar da cikin da ta sha yi.
"Sauyi ne babba a gare ni- da na fara yin wannan aikin, na samu matsalar furta kalmar "zubar da ciki" da karfi," in ji ta. "Yau, abu ne mai sauki na yi magana a kan zubar da ciki a bayyane."

Asalin hoton, Getty Images
Ta girma a al'umma mai addini da ta ba ta yarda da zubar da ciki ba. "Na ji kunya sosai na zubar da ciki kuma ban tambayi 'yan uwa da abokan arziki su taimake ni ba.
"Ballantana bayan zubar da ciki daya, ban yi tunanin cewa zan iya neman taimako ba bayan zubar da ciki da yawa.
Bai yi wa Erin wuyar gane cewa tana da ciki ba bayan batan wata. "Jikina nan da nan yake sauyawa ko yaushe na samu ciki, na san cewa akwai wani abu."
Amma yanke hukuncin zubar da ciki bai taba ba ta wahala ba. "Ba na so na zama uwa, kuma ba na so na tarbiyyantar da yaro," in ji ta.
"Ina tunanin cewa yadda ake ganin yanke shawarar zubar da ciki na da wahala ga kowace mace, ya yi barna ga kungiyoyin kare hakkokin haihuwa."
Ta yi bayanin cewa kadaici bayan zubar da cikin da tsangwamar za su ragu.
"Idan muka yawaita magana a kan zubar da ciki a bayyane, hakan zai karfafa mana al'umma, za a daina tsangwamar. Za mu iya taimakawa juna ta wannan hanyar."
'Kunyar ta sa na ji kamar a killace nake'- Indu, Indiya
"Shekaruna 31 lokacin kuma a lokacin wayata ta bata," Indu ta fada wa BBC. "Na je sayo sabuwar waya sai na fara jin amai. Lokacin ne saurayina ya ba ni shawarar yin gwajin ciki."
Ya nuna cewa tana dauke da ciki, kuma ta san cewa ba ta da zabi illa zubar da cikin. "Na fara aiki kenan a matsayin mai zane-zane, kuma saurayina ya amince da hakan.
Ta je wurin likitar mata wadda suka yi makaranta tare. Ta zubar da cikin a cikin sauki ta hanyar shan wasu kwayoyi. Amma bayan haka, ta shiga wani hali."Saboda tsangwama da ake wa wadanda suka zubar da ciki dole ta yi shiru da maganar. Wannan kunyar ce ta sa ta ji kamar a killace take," in ji ta.
"Jinin da ya ta zuba bayan na zubar da cikin ya sa na fara jin amai da tsoro. Na yi ta kuka kamar raina zai fita."

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu ana tsangwamar mutane kan zubar da ciki a Indiya.
"Na ji bakin cikin cewa ni ce na ji radadin abin, duk da cewa ya shafi mu biyu," in ji ta. "Kafin skekara guda, na fara shan maganin rage tsananin damuwa.
Ta ce hakan ya yi tasiri a dangantakarta ta gaba. Ta ji tsoron yin jima'i na tsawon lokaci. Hakan ya sa ta gane muhimmancin samun goyon baya.
"Yanzu idan na yi tunanin abin, ina ganin cewa da na samu filin yin maganan a bayyane, da abin ba haka ba."
'Ana yi wa zubar da ciki kallon zunubi a wannan al'ummar'- Jocelyn, Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo
Jocelyn ta haifi danta na biyu wata hudu da suka wuce. "Na fara nuna alamu kamar kumburin nono, rashin cin abinci da gajiya," ta ce.
Nan da nan ta gano cewa tana da wani cikin, ta yanke hukuncin zubarwa. "Lafiyar dana shi ne abin da na fara tunani kenan. Tsoron zubar da cikin dama shi ne tunanin tasirin da zai yi a kan kiwon lafiya, amma mijna ya ba ni kwarin gwiwa."

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da take tasowa, ba ta taba jin maganar zubar da ciki ba al'ummarta. "Zubar da ciki abin sirri ne da ake yi wa kallon zunubi a al'umma," ta ce. "Mutane suna tsangwamar wadanda suka zubar da ciki."
Jocelyne ta ce da kyar ta samu ta gamsar da likitan da ya yi mata. "Bai gamsu da hukunci da na yanke ba kuma ya yi ta ba ni shawara, amma na roke shi ya yi."
Ta yanke hukuncin zubarwa a gida saboda ka da a sani. "Na ji tsoro saboda ban taba yi ba, amma ina da karfin halin," in ji ta.
"Ma'aikatan lafiya sun taimake ni, kuma na samu kwanciyar hankali bayan an gama."
Jocelyn ta ce zubar da cikin da ya faru tana shekara 31, ya sa ta kara wayewa. "Yanzu ina shan magunguna da ke hana ciki don kaucewa samun wani cikin. Ya tabbatar mun da cewa hakan ba zai kara faruwa da ni ba.
'Ina fatan cewa wata rana mata za su samu 'yancinsu'- Maria, Mexico
Lokaci na farko da Maria ta ga likita abu ne marar sauki a gare ta.
Ta kasance mace mai shekara 35 da ke son zubar da ciki amma ta girma da tunanin cewa zubar da ciki 'kisa ne' wani abu ne da ke da hadari, tamkar daddatsa mutum ne.
Amma hakan na kan hanyar sauyawa. "Wannan lokacin ya kawo sauyi. Likitan ya yi bayani cewa aikin tamkar aiki ne ko wani ciwo," in ji ta.
"Ba ta yi min tambayoyi ba, ba ta yi min fada ba, ba ta yi mun kallon wata wadda da ta san ciwon kanta ba. A nan na gane nauyin kyamar zubar da ciki."

Asalin hoton, Getty Images
Ta ce akwai wahala samun hanya mai inganci ta zubar da ciki duk da cewa halal ne a garin mexico. Kudaden da ake kashewa a asibitoci masu zaman kansu na da yawa, amma duk da haka ta zabi yi a nan maimakon na gwamnati don kare kai.
"Iyalaina ba su san na zubar da ciki ba. Ban san yaya za su yi ba... amma na san cewa zai yi wa wasun su ciwo sosai balle mamata."
Ta tuna wata tattaunawa da suka taba yi da 'yan uwanta a kan zubar da ciki lokacin da kanwarta mai shekara 14 ta yi ciki. Maria ta ba da shawarar a zubar. "Sun ji haushi sosai, ban kara magana akai ba."
Maria a kidime ta shiga a yi mata aikin, da sauranyinta a gefenta. "Ya dauki kamar minti 30 ko kasa da haka," in ji ta.
"Na yi mamakin cewa an magance abin da nake yi wa kallon babbar matsala a cikin dan kankanin lokaci.
Yanzu a shekaru 38, ta san cewa ba ta son haihuwar yara. "Na san matsayin kasancewa uwa ko uba, duniyar nan na da matsaloli, ni da saurayina mun yanke hukuncin a'a," in ji ta.
"Ina fatan wata rana mata za su samu 'yancin yanke hukuncin abin da za mu yi a rayuwarmu, musamman a jikinmu. Ina fatan wata rana hakan zai zama gaskiya a fadin duniya."
*An sauya sunayen matan domin kare su
KArin bayani daga Emery Makumeno











