Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Koriya ta Arewa ta saki hotunan da makami mai linzaminta ya dauko daga sararin samaniya
Koriya ta Arewa ta saki wasu hotuna da ta ce an ɗauke su ne da makamai mai linzaminta mafi ƙarfi da ta ƙaddamar a cikin shekara biyar.
An ɗauki hotunan waɗanda ba a saba gani ba daga sarrain samaniya da ke nuna sassan yankin Koriya da kuma maƙwabtanta.
A ranar Litinin ne Pyongyang ta yi gwajinta na makami mai linzami samfurin Hwasong-12.
Yayin da yake kan ganiya makamin na iya yin tafiyar dubban kilomitoci, ta yadda hakan zai sa wasu yankunan Amurka a cikin haɗari.
Gwajin na baya-bayan nan ya ɗaga hankalin manyan ƙasashen duniya.
A wata guda da ya gabata kaɗai Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami har bakwai - wani lamari mai kama da tsokanar faɗa da Amurka da Koriya ta Kudu da Japan da sauran ƙasashe suke Allah-wadai da shi.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta haramta wa Koriya ta Arewa gwaje-gwajen harba makamai masu linzami, ta kuma ƙaƙaba mata takunkumai kan hakan. Amma Koriyan ta yi kunne uwar shegu da haramcin.
Jami'an Amurka a ranar Litinin sun ce ci gaba da harba makaman da Koriya ke yi na buƙatar a sabunta tattaunawa da ƙasar.
Me ya faru a yayin harba makamin Hwasong-12?
Koriya ta Kudu da Japan su ne na farko da suka bayar da labarin ƙaddamar da harba makamin a ranar Lahadi bayan da na'urorinsu masu gano makamai masu linzami suka ba da alama.
Sun yi ƙiyasin cewa an harba makamin ya yi tafiya ta nisan kilomita 800 a sama kafin daga bisani ya sauka a cikin tekun da ke kusa da Japan.
Idan aka ƙure masa gudu, makamin na iya yin tafiyar kilomita 4,000.
Koriya ta Arewa ta tabbatar da harin makamin a ranar Litinin a ta bakin kafar yaɗa labaranta ta ƙasar. Yawanci sai bayan kwana ɗaya da harba makaman ne sannan kafar yaɗa labaran ƙasar ke fitar da labarin.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasar KCNA, ya ce an harba makami mai linzamin don gwada ƙarfin aikinsa. Ana sane aka tsara yadda zai faɗo don kare tsaron maƙwabtan ƙasashe".
Kafar yaɗa labaran ƙasar sun wallafa wasu hotuna da ba a saba gani ba, waɗanda suka ce an ɗauki wasun su ne da kyamarar da aka maƙala a kan makami mai linzamin.
Ɗaya daga cikin hotunan ya nuna lokacin da aka ƙaddamar da makamain da kuma wani da ya nuna makamin lokacin da ya yi tsaka da tafiya da aka ɗauka daga can sararin samaniya.
Shugaban ƙasa Kim Jong-un bai halarci ƙddamar da makamin ba, ba kamar mako uku da suka gabata ba da aka gan shi a hotuna yana halartar gwajin ƙaddamar da wani makamin mai linzami - da aka ƙera shi ta yadda na'urorin da ke gano makamai ba za su iya ganinsa ba.
Sau uku kacal Koriya ta Arewa ta gwada harba irin wannan makamin.
Me ya sa Koriya ta Area ta harba makami mai linzami?
Wata mai sharhi kan Koriya ta Arewa Ankit Panda ta ce, rashin halartar Shugaba Kim da kuma salon da aka yi amfani da shi wajen bayyana harin, na nuna cewa wannan gwaji an yi shi ne don gano ko na'urorin da ke gane an harba makamin na aiki, ba wai don nuna bajinta kan sabuwar fasahar ba.
Sai dai duk da haka, wannan ne karo na farko da Koriya ta Arewa ta harba makami samfurin Hwasong-12, tun lokacin da ta tattauna da Amurka lokacin mulkin Shugaba Donald Trump - wanda ya jawo aka samu raguwar gwaje-gwajen makamai masu linzamin.
Rabon da a yi gwaji da harba makami samfurin Hwasong-12 tun 2017, a lokacin da Pyongyang ta ƙaddamar da shi har sau shida kuma biyu daga ciki an harba su ne a Tsbirin Hokkaido na Japan, abin da ya ɗaga hankalin mazauna wajen.
A shekarar 2018 bayan da Shugaba Kim ya gana da Mista Trump, Koriya ta Arewa ta sanar da dakatar da gwaje-gwajen makaman nulikiya. Amma a lokacin da dangantaka ta yi tsami a shekarar da ta biyo bayanta, Shugaba Kim ya yada wannan shirin.
A ranar Lahadi, shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya ce gwajin baya-bayan nan ya sa Koriya ta Arewa na dab da lalata wannan yarjejeniyar.
Akwai dalilai da dama du suka sa Koriya ta Arewa ta ke ƙara ƙaimi wajen gwaje-gwajen makaman a bana, wanda dama tun a jawabinsa na sabuwar shekara Shugaba Kim ya bayyana hakan.
Masu sharhi sun ce gwaje-gwajen na nuna buƙatar Shugaba Kim ta son matsa wa Amurka lamba don komawa teburin tattaunawa ne, da nuna ƙarfinsa ga manyan ƙasashen duniya da kuma nuna sabbin na'urorin fasaha da yake da su.
Waɗannan abubuwa na faruwa ne a lokacin da Gasar Olympics ta hunturu ke gabatowa da za a fara a wannan makon, da kuma zaɓen shugaban Koriya ta Kudu da za a yi a watan Maris.
"Wannan halayya ce da suka saba don neman tsokanar Koriya ta Kudu da sabon shugabanta da za a zaɓa," a cewar Dr Daniel Pinkston, wani mai sharhi kan harkokin ƙasashen waje daga Jami'ar Troy da ke zaune a Koriya ta Kudu.
Ana samun ƙaruwar gwaje-gwajen makaman a yayin da tattalin arzikin Koriya Ta Arewa ke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi sakamakon takunkuman Amurka da tasirin annobar cutar korona.
A farkon wannan watan ne Amurka ta sake ƙaƙaba wa Koriya ta Arewa sabbin takunkumai.