Wani babban jami'in Koriya ta Arewa ya tona wa Kim Jong-un asiri

    • Marubuci, Daga Laura Bicker
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC, Seoul

Kim Kuk-song bai rabu da tsohuwar ɗabi'ar ɓoye sirri ba wadda aka san jami'an Koriya ta Arewa da ita.

Sai da aka ɗauki tsawon lokaci na makonni kafin ya yarda a tattauna da shi kuma duk da haka ya damu a kan wanda zai iya kasancewa yana sauraren tattaunawar da shi. Ya sanya baƙin tabarau a lokacin da za a ɗauki bidiyon hirar tasa, kuma mutum biyu ne daga cikin tawagarmu kawai suke iya sanin ainahin sunansa.

Mista Kim ya shafe shekara 30 daga mataki zuwa mataki har ya kai ga matsayin manyan jami'an hukumomin leƙen asiri na Koriya ta Arewa. ''Hukumomin su ne idanuwa da kunnuwa da kuma ƙwaƙwalwar Shugaban ƙasar'', in ji shi.

Ya yi iƙirarin cewa shugaban ne ke ɓoye sirrinsu, shi ne ke tura mutane su hallaka masu sukar gwamnatinsu, har ma da kafa haramtattun wurare na haɗa miyagun magunguna domin samun kuɗaden da ya kira na juyin-juya hali.

Yanzu dai wannan tsohon kanar ya yanke shawarar gaya wa BBC labarinsa. Wannan shi ne karon farko da wani babban jami'in soji daga Koriya ta Arewa ya tattauna da wata babbar kafa ta yada labarai ta duniya.

A tattaunawar ta musamman Mista Kim ya bayyana kansa a matsayin ɗaya daga cikin mafiya kusanci ga shugabancin gwamnatin kwaminisanci ta ƙasar.

Amma matsayi da biyayyarka ga gwamnatin ba tabbaci ne na zamanka lafiya ko tsira daga gwamnatin ta Koriya ta Arewa ba.

A dole ya tsere domin cetar ransa a 2015, kuma tun daga wannan lokacin yake zaune a Seoul inda yake aiki da jami'an leƙen asiri na Koriya ta Kudu.

Ya bayyana shugabancin Koriya ta Arewa da ya duƙufa domin samun kuɗi ta kowa ne hali, kama daga hada-hadar miyagun ƙwayoyi zuwa ga sayar da makamai a Gabas ta Tsakiya da Afirka.

Ya bayyana mana dalilan da ke sa gwamnati a Pyongyang, ke son kai hari da sukar Koriya ta Kudu da kuma iƙirarin yadda masu leƙen asiri na ƙasar da harkokinta na intanet za su kai wa ga sassan duniya.

Ko da yake BBC ba za ta iya tabbatar da iƙirarin nasa ba, amma duk da haka mun yi ƙoƙarin gano ko shi waye, sannan kuma inda za mu iya mu gano shedu da ke tabbatar da zargin nasa.

Mun tuntuɓi ofishin jakadanci na Koriya ta Arewa da ke London da wanda ke New York domin samun wata sanarwa, amma kawo yanzu ba mu ji daga garesu ba

Rundunar ta'addanci :

Ƴan shekaru na ƙarshe na aikin Mista Kim a sashen leƙen asiri na Koriya ta Arewa suna bayar da ɗan haske game da rayuwar farko-farko ta shugaban ƙasar na yanzu, Kim Jong-un.

Ya gabatar da rayuwa irin ta mutumin da yake cike da burin nuna kansa a matsayin mayaƙi.

Koriya ta Arewa ta ƙirƙiro wata sabuwar hukumar leƙen asiri (Reconnaissance General Bureau) a 2009, yayin da ake renon Kim Jong-un ta yadda zai gaji mahifinsa, wanda ya gamu da cutar bugun jini.

Shugabn hukumar shi ne Kim Yong-chol, wanda ya kasance ɗaya dga cikin amintattun shugaban Koriya ta Arewa.

A watan Mayu na 2009 Mista Kim ya ce, an aiko da saƙo daga sama (shugabancin ƙasar) domin kafa wata runduna ta musamman domin kashe wani tsohon jami'in Koriya ta Arewa wanda ya sauya sheƙa zuwa Kudu.

Mista Kim ya ce,"A wurin Kim Jong-un, aiki ne na gamsar da shugaban ƙasar (wato mahifinsa).''

Daga nan ne aka ƙirƙiro ''rundunar ta'addanci'' domin hallaka Hwang Jang-yop a asirce. Ni da kaina na bayar da umarni da kuma yin aikin."

A wani lokaci can baya Hwang Jang-yop na ɗaya daga cikin manyan jami'an ƙasar masu ƙarfin faɗi a ji. Ya kasance mai matsayi sosai a wajen tsara manufofin Koriya ta Arewa.

Hukumomin ƙasar ba su yafe masa ba kan sauya sheƙar da ya yi zuwa Koriya ta Kudu a 1997. Yana tsallakawa Seoul, sai ya fara sukar gwamnatin Arewa inda kuma iyalin Kim suka lashi takobin ramuwa.

Sai dai yunƙurin kisan nashi bai yi nasara ba. Har zuwa yanzu wasu sojojin Koriya ta Arewa biyu masu muƙamin manjo suna zaman gidan yari na shekara 10 a Seoul saboda samunsu da laifin yunƙurin kisan.

A ko da yaushe gwamnati a Pyongyang na musanta hannunta a shirin tare da ƙari da cewa Koriya ta Kudu ce ta shirya harin.

Bayanin Mista Kim na nuna alamun saɓanin hakan.

"A Koriya ta Arewa ta'addanci wata hanya ce ta siyasa ta kare martabar Kim Jong-il da Kim Jong-un", a cewarsa. "Wani tukuci ne na nuna biyayyar mai gadon ga shugabansa."

Akwai ƙarin wasu abubuwa kuma da za su biyo baya.

Sheƙara ɗaya bayan nan a 2010, wani jirgin ruwan Koriya ta Arewa mai suna Cheonan, ya nutse a teku bayan da aka harbe shi da wani makami, inda mutane 46 da ke cikinsa suka mutu. Har kullum gwamnatin Koriya ta Arewa na musanta hannu a harin.

Sannan kuma a watan Nuwamba na wannan shekara, gomman makaman atilare na Koriya ta Arewa suka fada wa tsibirin Yeongpyeong na Koriya ta Kudu, inda sojoji biyu da farar hula biyu suka rasa ransu.

An yi ta muhawara kan wanda ya bayar da umarnin kai harin. Mista Kim ya ce ba shi da hannu kai tsaye a harin na tsibirin Cheonan ko Yeonpyeong'', to amma wannan ba wani abin sirri ba ne ga jami'an rundunar leken asiri ta Koriya ta Arewa ta RGB. Abu ne da suke cike da alfahari a kansa.

Tsohon jami'in ya ce waɗannan hare-hare ne da ba ta yadda za a kai su ba tare da umarni daga sama ba.

Ya ce, "A Koriya ta Arewa ko da titi za a gina, ba ta yadda za a yi shi ba tare da umarni daga shugaban ƙasar ba.

Nutsar da jirgin ruwan Cheonan da ruwan makaman atilare a tsibirin Yeongpyeong abu ne da ba ta yadda muƙarraban shugaban ƙasar za su yi gaban kansu su aikata.

"Irin wannan aiki na soji abu ne da Kim Jong-un ke tsarawa da aiwatarwa da kuma bayar da umarni. Wani ci gaba ne."

'Dan Leken Asiri a Fadar Koriya ta Kudu'

Mista Kim ya ce ɗaya daga cikin ayyukansu a Koriya ta Arewa shi ne yin tsare-tsare domin ladabtar da Koriya ta Kudu. Manufar ita ce sabauta shugabancin ƙasar".

Wannan ya ƙunshi sanya ido da kunne a kan abubuwan da ke faruwa.

"Akwai lokuta da dama da na bayar da umarni ga masu leƙen asiri da suka je Koriya ta Kudu kuma na yi amfani da su wajen gudanar da aiki ta hanyarsu. Da dama,'' kamar yadda ya yi iƙirari.

Ba ya bayar da cikakken bayani amma ya ba mu misalin wani labarin mai ɗaure kai.

Ya ce akwai wani lokaci da aka aika wani ɗan leken asiri na Koriya ta Arewa ya yi aiki a Ofishin Shugabn ƙasa a Koriya ta Kudu har ya gama kuma ya koma Koriya ta Arewa lami lafiya.

Ya ce abin ya faru ne a farkon shekarun 1990, inda jami'in ya yi aiki na shekara biyar ko shida.

"Ina tabbatar maka da cewa 'yan leƙen asiri na Koriya ta Arewa da dama suna aiki sosai a ƙungiyoyin fararen hula na Koriya ta Kudu da sauran hukumomi na ƙasar.

Babu hanyar da BBC za ta tabbatar da wannan iƙirarin.

Na haɗu da jami'an leƙen asiri na Koriya ta Arewa da yawa waɗanda aka yanke musu hukunci a Koriya ta Kudu, kuma a matsayina na wanda ya ƙirƙiro NK News founder Chad O'Carroll ya wallafa a wata maƙala ta kwanan nan cewa gidajen yarin Koriya ta Kudu na cike da jami'an leƙen asiri na Koriya ta Arewa da aka kama da laifi.

Har yanzu ana samun, rahotanni amma kaɗan na irin waɗannan jami'ai na leƙen asiri daga Koriya ta Arewa a Koriya ta Kudu.

Amma bayanan NK News na nuna cewa waɗanda ake kamawa na Koriya ta Arewa a Koriya ta Kudu idan aka kwatanta yawansu tun 2017, sun ragu sosai saboda yadda Arewa ta karkata ga sabbin dabaru na fasaha maimakon hanyoyi irin na da na leƙen asiri da satar bayanai.

Koriya ta Arewa ka iya zama ɗaya daga cikin ƙasashe matalauta da kuma aka ware su a duniya, amma kuma wasu daga cikin manyan jami'anta da suka sauya sheƙa zuwa Kudu na gargadin cewa ƙasar ta ƙirƙiri gwanayen kutse a intanet 6,000.

Mista Kim ya ce "jami'ar Moranbong tana zabar ɗaliban da suka fi hazaka daga ko ina a fadin ƙasar ta sa su ƙarƙashin wani shiri na musamman na koyarsa tsawon shekara shida."

Jami'an tsaron Birtaniya sun yi amanna cewa wani sashe na 'yan Koriya ta Arewa da ake kira Lazarus Group shi ne ke da alhakin kai harin da ya durƙusar da ayyukan hukumar lafiya ta ƙasar da sauran wasu hukumomi a duniya a 2017.

Haka kuma wannan sashe ne aka yi amanna ya kai gagarumin harin intanet a kan kamfanin Sony Pictures a 2014.

Hada-hadar miyagun ƙwayoyi domin samun dala

A kwanan nan Kim Jong-un ya sanar cewa ƙasar na shirin sake faɗawa yanayi na yunwa kamar yadda aka gani a shekarun 1990, lokacin mulkin mahaifinsa Kim Jong-il.

A wannan lokacin, Mista Kim yana sashen Ayyuka a don haka aka ba shi umarnin samar da kuɗade ga shugaban ƙasar. Ya ce hakan na nufin ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.

Ya ce "Aikin samar da miyagun ƙwayoyi ya bunƙasa a lokacin da ƙasar ta faɗa yanayi na yunwa a zamanin Kim Jong-il, wanda a wannan lokaci Sashen Ayyukn ya rasa kuɗin gudunmuwa na shugaban ƙasa.

Bayan da aka ɗora masa wannan aiki sai ya ɗauko wasu ƴan ƙasar waje uku zuwa Koriya ta Arewa, inda suka kafa masana'anta da suka rika samar da miyagun ƙwayoyi.

Suka riƙa samar da ƙwayar ICE, da suke sayarwa su samu dalolin da za su ba wa Shugaba Kim Jong-il, a cewarsa.

"Da na tambayi Mista Kim abin da ake yi da kuɗin da ake samu daga cinikin miyagun ƙwayoyin. Ko ana juya su ne domin amfanin jama'a?"

Sai ya ce "Ta yadda za ka fi fahimtar abin shi ne duk wani kuɗi na ƙasar mallakar Shugaban ne, saboda haka da wannan kuɗin zai gina manyan gidaje, ya sayi motoci ya sayi abinci da tufafi ya rika holewa.''

An yi ƙiyasin mutanen da suka mutu a lokacin matsalar yunwa da aka dade ana fama da ita a Koriya ta Arewa a shekarun 1990 sun kai daga dubbai zuwa miliyan uku.

Wata hanyar samun kuɗi kuma ga ƙasar in ji Mista Kim ita ce ta haramtaccen cinikin makamai, inda take sayar wa da Iran makamai a boye, abin da Sashen Ayyuka ke tafiyarwa.

Tsohon jami'in na Koriya ta Arewa, ya ce ƙasar ta ƙware wajen ƙera ƙananan jiragen ruwa na ƙarƙashin teku da makamantansu.

Mista Kim ya ce Koriya ta Arewa tana kuma sayar da makamai da fasaha ga ƙasashen da suka daɗe suna yakin basasa. A shekarun baya-bayan nan Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Koriya ta Arewa da samar da makamai ga Syria da Myanmar da Libya da kuma Sudan.

Majalisar ta ma yi gargadin cewa makaman da ake ƙerawa a Pyongyang ka iya kai wa ga sassan duniya da dama da ake fama da rikici.

'An ci amanar jami'i mai biyayya'

Ba da daɗewa da hawan mulkin Kim Jong-un a 2011, sai ya yanke shawarar yin tankaɗe da rairaya na waɗanda ya dauka a matsayin barazana gare shi, ciki har da kawunsa, Jang Song-thaek.

An daɗe ana ɗaukar Mista Jang a matsayin wanka ke jan ragamar shugabancin ƙasar ta bayan fage yayin da rashin lafiyar Kim Jong-il ke kara tsanani.

Kamar yadda Mista Kim ya ce, sunan Jang Song-thaek na ƙara fice a lokacin fiye da na Kim Jong-un.

"Daga nan ne na ga cewa lalle Jang Song-thaek ba zai jima ba. Na ga cewa lalle za a kawar da shi zuwa ƙauye," in ji shi.

To amma kwatsam sai kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Koriya ta Arewa a watan Disamba na 2013 ta bayar da sanarwar cewa an kashe shi.

"Na yi matuƙar mamaki, abin ya tayar min da hankali," in ji Mista Kim. "Nan da nan na ga irin haɗarin da rayuwa ke ciki. na san cewa ba zan iya ci gaba da rayuwa a Koriya ta Arewa ba."

Mista Kim yana ƙasar waje a lokacin da ya samu labarin kisan a jarida. Daga nana ya yanke shawarar ya shirya ya tsere tare da iyalinsa zuwa Koriya ta Kudu.

"Barin ƙasata, inda kabarin kakannina yake da iyalina, na gudu zuwa Koriya ta Kudu, wadda a lokacin wata baƙuwar ƙasa ce a wurina, shi ne abu mafi wahala da muni.'' ya ce

Tambayar da na riƙa tambayarsa a yayin tattaunawar tamu ita ce me ya sa a yanzu ya yanke shawarar yin magana."

Wannan ce sadaukar kawai da zan iya yi," ya ce. "zan bayar da himma sosai daga yanzu domin na ƴanto ƴan uwana na Arewa daga hannun mulkin kama-karya, domin su ji daɗin cikakken ƴanci."

Akwai ƴan Koriya ta Arewa da suka tsere zuwa Koriya ta Kudu sama da 30,000. Kaɗan ne daga cikinsu kawai ke yard su yi magana da ƴan jarida.