Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa Koriya Ta Arewa ke ci gaba da harba makamai masu linzami
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Duk da sukar da kasashen duniya suke yi, Koriya Ta Arewa da ke gabashin nahiyar Asiya na ci gaba da gwajin makamai masu linzaminta, wadanda wasu sun karya dokar yarjejeniyar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
To ko me ya sa Koriya Ta Arewan take ci gaba da kai wadannan hare-haren, wadanda take kashe kudade masu yawa a kansu?