Kim Jong-un: Abubuwan da suka faru a shekaru 10 da ya zama shugaban Koriya Ta Arewa

    • Marubuci, Daga Laura Bicker
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Seoul

Shekaru 10 kenan da shugaban da ba a taba gwada shi ba, matashi dan shekara 27 ya soma shugabancin Koriya ta Arewa; cikin wadannan shekaru shugabannin kasashen duniya kalilan ne suka ja hankali kamar yadda ya yi. Amma yaya rayuwa take karkashin mulkin Kim Jong-un?

Koke-koke da tsananin damuwa ne suka cika titunan birnin Pyongyang.

Dalibai sanye da kayan makaranta ne suka durkusa kan gwiwoyinsu, suna kuka da kururuwa. An dauki hotunan mata suna kuka da dukan kirjinsu tamkar za su fito da zukatansu waje.

Kafar yada labaran Koriya ta Arewa mai tsananin tsaro ce ta sanar da mutuwar shugaban kasar abin kaunarsu Kim Jong-il yana da shekaru 69 a duniya. Ranar ta kasance 19 ga watan Disambar 2011.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum na Koriya ta Arewa da ke sassa daban-daban na duniya sun bazama domin yin rubutu kan mutum daya tilo da ya dauki hankalinsu.

Kim Jong-un

Yana da shekara 27 aka bayyana shi a matsayin magajin mahaifinsa. Amma daidaikun mutane ne suka yi tunanin zai kai labari. Ta yaya al'ummar da ta yi fice wajen amfani da yawan shekaru da gogewa za ta zabi wanda kwata-kwata ya yi hannun riga da wadancan abubuwan?

'Yan kasar da dama sun yi tunanin za a yi juyin mulkin soji, ko 'yan bokon Koriya ta Arewa su karbi ragamar kasar. Ba matsayin shugaba kadai Kim Jung-Un ya zama ba, ya share wata hanya ta sabon babin mulkin da ake kira "Kim Jong-unism".

Ya fara salon mulkin ta hanyar kawar da abokan gabarsa, da zartar da daruruwan hukunci, sannan ya mayar da hankali kan harkokin kasashen waje. Gwajin makaman nukiliya hudu, harba makamai masu linzami 100 da ke cin dogon zango, da tattaunawa da shugaban Amurka.

Kafiya da tsagerancin ci gaba da harbawa da kera makaman nukiliyar sun janyowa kasar matsala. Koriya ta Arewa na tsaka mai wuya, bakin talauci da zama cikakkiyar saniyar-ware daga idon duniya ya karu a lokacin mulkinsa.

Abin tambayar shi ne, yaya rayuwa take karkashin mulkinsa?

Mutum goma da suka bijire wa gwamnatinsa, ciki har da manyan jami'an difilomasiyya sun yi waiwayen yadda rayuwa take karkashin Kim Jong-un a shekaru 10 da suka gabata.

Sabuwar duniya

Dalibi Kim Geum-hyok ya yi wani abu da ka iya janyowa a harbe shi, a ranar da mahaifin Kim Jong-un ya mutu. Ya shirya gagarumar dabdala.

"Lamari ne mai matukar hadari. Amma muna cike da farin ciki a lokacin," in ji shi.

Yana ganin sabon shugaba, kuma matashi wanda zai kaunaci wasan kwallon kwando a matsayin wanda zai daga murya domin kawo sauyi.

"Muna da kyakkyawan fata ga Kim Jong Un. A kasashen turai ya yi karatu, watakila ya dinga tunani irin namu, domin kawo sauyi.''

Geum-hyok dan babban gida ne, ya samu gatan yin karatu a Beijing, wanda tsiraru ne suka samu gata irin wannann a Koriya ta Arewa.

Rayuwar China ta bude masa ido, kan sanin wata sabuwar duniyar yana kuma bincike a intanet domin sanin halin da kasarsa ke ciki.

"Da farko, ban yadda da abin da ke faruwa ba. Kasashen yamma karairayi suke yadawa kan yadda Koriya take. Amma sai hankalina ya rabu gida biyu, wani bangaren na fada min 'ba ka bukatar gani, amma zuciyata na son sanin halin da ake ciki'."

'Yan Koriya ta Arewa miliyan 25 a takure suke, ba su san abin da duniya ke ciki ba, ba su san kallon da kasashen duniya ke yi wa kasarsu ba.

An sanya su amince da shugabansu a matsayin wani dan baiwa ne mai tarin mu'ujizoji, da ya cancanci su mika wuya gare shi da amincewa da sharudan da ya gindaya musu.

Amma ga Guem-hyok, matashin shugaban na wakiltar wani abu da suka rasa.

Masu shakku

Sai dai wasu daga cikin 'yan kasar na da tababar hakan. Idan ana batun cancanta a Pyongyang, akwai masu rade-radin Kim Jong-un ya yi nasara ne ba wai cancantar shugabancin ba.

Tsohon jakadan Koriya ta Arewa a Kuwait Ryu Hyun-woo, ya shaida wa BBC abokan aikinsa da suka koma karkashin Da bayan mutuwar Uba.

"Tunanin farko da ya fara zuwa min, shi ne, 'wa zai gaje shi?' 'yan Koriya ta Arewa sun gaji da mulkin mulaka'u. Musamman tsakanin masu fada aji, muna bukatar ganin wani abu na daban, muna son sauyi da ci gaba, wannan shi ne tunanin mu."

Tun daga shekarar 1948 iyalan gidansu Kim ke mulki a Koriya ta Arewa. An cusawa 'yan kasar cewa jinin 'yan gidan mai karfi da daukaka ne.

"Na sha jin kalamai irin wannan, "hakan na nufin za mu yi ta musu bauta har karshen rayuwarmu?'

"Me dan shekara 27 ya sani kan yadda za a tafiyar da mulkin kasa? Ya yi maganar da jan numfashi."

Alkawari

A wani jawabi a shekarar 2012, sabon shugaban ya yi wa 'yan Koriya ta Arewa alkawarin babu wanda zai daure damara da sunan wahala ko tashin hankali.

Ga kasar da ta ji jiki da mace-macen mutane a lokacin da fari ya fada mata a shekarun 1990, wanda dubban mutane suka mutu, alamu sun nuna sabon shugaban zai kawo karshen fatarar abinci da azabar da suke sha. Lokaci ne mai cike da kyakkyawan fata.

Jami'an ofisoshin kasashen waje an ba su umarnin mayar da hankali wajen kawo masu zuba jari. An kuma ga alamun sauyi a cikin kasar.

Yoo Seong-ju direba ne mazaunin yanki mai tashar ruwa, ya kuma lura da ganin sauye-sauyen kayayyakin da Koriya ta Arewa ke samarwa a manyan shaguna.

"Gare mu abin mamaki ne da alfahari, ganin kayan abincin da Koriya ta Arewa ke samarwa sun fi na China inganci ta fuskar dandano, kunshewa da wadata. Sai muka yi ta kwambo da dagawa."

Tankade da rairaya

Fatan alkhairin da Kim Jong-un ke yi wa 'yan kasar bai kai ga wadanda suke yi masa barazana ba.

Kawun shi Jang Song-thaek ya hada kawancen manyan kungiyoyi a kasar.

Tafiyar daruruwan kilomita daga Pyongyang da ke arewacin kasar kusa da iyaka da China, dan kasuwa Choi Na-rae na tunanin ko Mista Jang zai kasance sabon shugaban Koriya ta Arewa.

"Yawancin mu na fatan wata dama za ta bude tsakanin kasar da China, ta yadda za mu dinga balaguro a saukake ba ta da wata matsala ba," in ji shi.

"Mun zaci Jang Song-thaek shi zai gaji dan uwansa, ta yadda zai ciyar da tattalin arzikinmu gaba da sauye-sauye. Tabbas ba mu isa fadar haka a bayyane ba, amma fata na gari kawai muke yi a zukatanmu."

Ana bukatar shafi irin wadannan tunanin da jita-jita.

An ayyana Jang Song-thaek a matsayin mai yi wa kasa barazana da zagon kasa, daga nan aka zartar ma sa da hukunci kan zargin amfani da mukami ba bisa ka'ida ba da kuma jagorantar wata jam'iyya.

Matashin shugaban ya fara nuna tsageranci da salon mulkinsa.

Karbe iko da komai

Daruruwan 'yan kasar sun tsere iyakarsu da China, wasu sun yi kokarin tsallakawa makofciya Koriya ta Kudu domin neman mafaka daga tankade da rairayar da sabuwar gwamnati ta fara. Kim Jong-un ya yanke shawarar magance matsalar masu bijire wa gwamnati. An zagaye iyakar kasar da sauran kasashe da kakkaifar waya ta sama da kasa, babu hanyar tserewa ko gudun hijira kenan.

Ha Jin-woo ya taimakawa 'yan Koriya ta Arewa 100 tserewa daga kasar a lokacin da yake aikin mai fasa kwaurin mutane.

"Kasar na da jami'an tsaron da ke gadin iyaka na musamman. An ba su umarnin harbe duk wanda ya yi kokarin tsallaka iyakar, kuma babu wani hukunci da za a yanke musu ko da wadanda suka harba sun mutu."

"Na matukar tsorata a lokacin da na fara harkar. Tun ina karami na ke da shakku kan Koriya ta Arewa. Me ya sa aka haife ni a irin wannan kasar na ke kuma rayuwar da ba ta da bambanci da ta dabbobi ba, saboda rashin 'yanci? Don haka na yi kasadar fara wannan aikin."

Amma a hankali aka fara gano shi, dole ta sanya ya tserewa daga kasar. An kulle mahaifiyarsa a sansanin da ke kama da kurkuku, azabar da ake gallaza mata ta janyo ta samu lalurar shanyewar barin jiki.

Wannan ya sanya Jin-woo cikin tashin hankali, wanda ba zai iya tuna yadda muryar mahaifiyarsa take ba.

Sanannen mutum

Duk da tankade da rairayar kan wadanda suka bijirewa gwamnati, King Jong-un na kokarin bayyana a lokuta daban-daban, yana kuma nuna wayewa da sakin fuska fiye da mahaifinsa.

Ya auri wata kyakkyawa kuma 'yar gayu mai suna, Ri Sol-ju. An dauki hotunansa ya rungumar ta, da hotunan da ya yi fara'a a wuraren da ya kai ziyara, wasu ma har da daga hannu ga jama'ar garuruwa da kauyukan da ya kai ziyara yankunansu. Akwai hotunan sa ya sukuwa a kan doki, da zamiyar kankara, da hawa lilon sululu.

An kuma ga hotunan ma'auratan a manyan kamfanonin da ke yin kayan kwalliya da kayan kawa.

Amma an haramtawa 'yan kasar nuna su wayayyu ne ko nuna rayuwar jin dadi.

Yoon Mi-so na son a dama da ita a fagen wayayyu, ta taba ganin wani wasan kwaikwayo kan wadanda aka yi fasa kwaurinsu zuwa Koriya ta Kudu. Ta za ku ta sanya 'yan kunnaye masu reto da zabba, da sarka kai har da wandon Jins.

"An taba kama ni saboda kin bin dokokin aka kuma yanke min hukuncin kunyata ni a bainar jama'a, inda dandazon mutane suka yi ta sukar abin da na yi, har sai da na fashe da kuka. Suna kuma ce min "ba ki da tarbiyya, ko kunya ba ki ji ba?'"

Hyun-young mawakiya ce, Kim Jong-un. Amma an tilasta mata dukkan wakokinta na kamba shugabancin Mista Kim ne. Ta yi kokarin yin tawaye, amma aka ci ta da yaki.

"Ba a taba ba ni damar yin abin da nake son yi ba a matsayi na mawakiya ba. Na kuma yi matukar shan wahala kan dokokin da ke karkashin yin wakoki a Koriya ta Arewa.

"Gwamnati ce ke iko da wannan fannin, saboda tsoron kada 'yan kasashen waje su san abin da ake ciki. Wadannan dokoki da sa ido sun nuna ba su amince da tsarin mulkkinsu ba.''

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin dan adam ta fitar a baya-bayan nan, ya nuna cikin shekaru 10 an yanke wa mutum bakwai hukuncin kisa, saboda laifin kallon bidiyon wakokin mawakan makofciyar kasar Koriya ta Kudu.

Kim Jong-un ya bayyana tasirin irin wadannan abubuwan na kasashen waje da illarsu ta fi ta "cutar kansa".

Ashe matsala na nan kusa.

Kowanne harba makami mai linzami da aka yi ya dau hankalin kasashen waje, amma a cikin kasar babu wani abin tinkaho ko alfahari da hakan.

"Mutane na cewa suna kera makamai, ta hanyar gallazawa mutane da sanya su gumi kashirban domin tsananin wuya," in ji wani da ya bijire wa gwamnati.

"Ba ma kallon hakan da nasara. Tunanin mu na cewa ah sun kashe makudan kudade wajen gwaje-gwajen. Duk kudaden da suke biyan mu albashi, na sake komawa wajensu,'' in ji wani na daban.

Ashekarar 2016 a ofishin jakadanci, an bai wa Ambasada Ryu sabuwar doka. Hankalin ba wai kan kasuwanci aka dora shi ba.

"Ana bukatar mu fadi dalilin da ya sa Koriya ta Arewa ke bukatar makaman nukiliya, abin da ya sa da kuma alfanun hakan."

Fatan shi ne ya yin da jami'an diflomasiyya ke tattanawa kan batun, thakan zai zama ba bakon abu ba a kunnuwan 'yan kasashen waje. Amma hakan bai yi wani tasiri ba.

Babbar cacar mai makaman roka

Karuwar barazana tsakanin shugaban Amirka Donald Trump da Kim Jong-un ta karkare musu daukar sabon diflomasiyya.

Matashin shugaban, mai mulkin mulaka'u, tumbuleke dan baba, da kafafen yada labarai na kasashen waje suka yada shi kafada da kafada da shugaban Amirka tsaye a kan dandamali.

Yajridun Koriya ta Arewa sun yi ta wallafa hotunan yadda shugabannin suka sha hannu a haduwarsu ta farko a Singapore a shafin farko na jaridun kasa.

Saidai ba da jimawa ba, aka fara antayawa kasar takunkuman tattalin arziki. Duk da cewa duniya ta kalli hotunan, amma ba a yada komai ga mazauna kauyuka da ke wajen birnin Pyongyang.

"Ba mu da hanyar da za mu iya tantance ko sharhi kan abin da hakan ke nufi ba. Ba mu taba gano alfanun haduwarsu ba, ko ci gaban da ta kawo ga kasarmu ba," in ji dan kasuwa Choi Na-rae.

Babu wata matsaya da aka cimma, kuma ambasada Ryu ya yi amanna duk bigi-ba-giro ce, kawai domin samun saukin takunkumai.

"Arewa ba za ta taba daina kera makaman nukiliya ba, saboda a ganin ta su ne kadai za su ci gaba da rike gwamnati ta nuna karfinta."

Annobar Korona

Adhe wani bala'in mafi girma na tunkaro Kim Jong-un.

A lokacin da barkewar annobar korona ta daki makofciyarta China a watan Junairun 2020, Koriya ta Arewa ta rufe iyakokinta baki daya, ba wai ga mutane kadai ba, har da kasuwanci.

An ki amincewa a shiga da kayan abinci da magunguna ta iyakar Dandong. Sama da kashi 80 cikin 100 na kasuwancin kasar na zuwa ne daga China.

"Abubuwa sun yi matukar sauyawa tun barkewar annoobar korona," in ji Ju Seong wanda direba ne a Koriya ta Arewa. Ya yi kokarin yin magana da mahaifiyarsa a takaice a kusa da iyakar kasar da China.

"Tattalin arzikin ya kara durkushewa, farashin kayayyaki ya kara tashi. Ana rayuwa cikin kunci da matsi. Iyayena na iya samo abinci, amma matsalar farashin ne ya rubanya fiye da kima. Rayuwar akwai tsauri da wuya, lamarin ya munana."

Akwai rahotannin mutane na fama da tsananin yunwa.

Shi kan shi shugaba Kim Jong-un ya bayyana halin da na ''tashin hankalin da aka dade ba a gani ba'' har da kwallarsa a a lokacin da ya ke gabatar da jawabi. Lamarin da ba a taba gani ba ga shugaban Koriya ta Arewa.

Wani tsohon likita, Kim Sung-hui, ya ce sai ta kasuwar bayan fage ake siyan magunguna.

Ana samun daukewar wutar lantarki a wasu dakunan tiyata na asibiti, likitoci na amfani da hannunsu idan za su yi tiyata saboda babu safar hannu.

"Ya yin da na lura da banbancin kasashen nan biyu da ke yanki guda, ina addua'ar wata rana Koriya ta Arewa ta samu tallafi nan gaba, inda za a mutunta hakkin dan kas da su kansu jami'an lafiya."

Babu wani shiri da Koriya ta Arewa ta yi wa barkewar annobar korona, sannan 'yan kasa ba a fada musu halin da ake ciki na wadanda suka kamu da cutar.

Karfin fada aji na Kim

Yawancin wadanda suka bijire da tserewa kasar sun shiga matukar damuwa kan halin da ake ciki a Koriya ta Arewa, har su na hasashen anya ba za a yi juyin mulki ba. Amma shiru ka ke ji, babu wata alama da ke nuna hakan mai yiwuwa ne.

Karfin ikon Kim da iyalan gidansu ya kara tabbata, duk hasashen da ake yi na wargajewar gwamnati ya zama ta zo nu jita.

Bayan shafe kusan shekaru 70 suna damawa da gwamnati, yawancin wadanda na zanta da su fatan da suke da shi shi ne Koriya ta Arewa ta bude iyakokinta domin mutane su dinga shiga da fita kasashe makofta ba tare da matsala ba. Wasu kuma suna kishirwar gain 'yan uwansu.

Suna da 'yancin daga muryoyinsu, su kuma bayar da labaransu karkashin mulkin Kim Jong-un. Amma wadanda ke makale a cikin kasar ba su da damar yin hakan.

"Kasada ce ta sanya na ke yin waka," in ji mawakiya Hyun-hang. "Wadandahar yanzu suke cikin Koriya ta Arewa sai dai su hadiye a zukatansu, har sai sun koma ga Allah."

Ya yin da ake bikin cika shekara 10 kan karagar mulki, alhakin halin da kasar ke ciki ya rataya a wuyan Kim Jong-un. Ya na da gwamman sabbin makaman nukiliya, amma al'ummarsa na fama da matsananciyar yunwa.

An sanya wani katon allo dauke da hoton shi a babban birnin kasar Seoul, a shekarar 2018 jim kadan bayan ziyarar da shugaban Koriya ta Kudu ya kai ziyara kasar. Hoton Kim Jong-un ya nuna yadda zai hade dan yatsunsa wuri guda a abin da ake gani a kasar alamun mawakan K-POP da ke wakiltar soyayya.

A rubutun da aka yi a wancan lokacin, da alamun wannan dan yatsan, ana tunanin Mista Kim ka iya sauya rayuwar mutanensa.

Zai iya ba su 'yanci, saboda ya na da karfin ikon haka.

Amma maimakon hakan, mutum miliyan 25 a Koriya ta Arewa na rayuwa cikin duhun kai da rashin 'yanci, kuma ba su san me ke faruwa a duniya ba.

Dukkan wadanda aka tattauna da su, sun sanya rayuwarsu cikin hadari, tare da barin Koriya ta Arewa, inda a halin yanzu su ke zaman gudun hijira a makofciyarsu Koriya ta Kudu. Amma an sauya wasu daga cikin sunayensudomin bai wa iyalkansu da ke Koriya ta Arewa kariya.

Illustrations by Gerry Fletcher