Wane hali ake ciki kan ceto ƴan matan sakandaren Jangebe?

mace na kuka Jangebe

Asalin hoton, Getty Images

Ana ci gaba da kiraye-kirayen neman a kuɓutar da 'yan matan makarantar Sakandaren Jangebe fiye da 300, da 'yan fashin daji suka sace ranar Juma'a a jihar Zamfara.

Sai dai a cewar gwamnatin jihar, ɗalibai 279 aka sace.

Daga cikin manyan mutanen duniya da suka yi tur da sace 'yan matan Jangebe, waɗanda suka shiga kwana na uku da sacewa har da jagoran ɗariƙar Katolika na duniya, Fafaroma Francis.

A wata hira da BBC Hausa, kwamishinan ilimi na jihar Zamfara Ibrahim Abdullahi Gusau ya ce nan ba da jimawa ba suke sa ran dawo da yaran nan ga iyayensu cikin koshin lafiya.

A ranar Lahadi wasu kafafen yaɗa labaran Najeriya suka ruwaito cewa an sako ƴan matan, sai dai gwamnatin jihar ta ƙaryata batun.

Sanarwar da fadar gwamnatin jihar ta fitar a ranar Lahadi ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an sako ɗaliban kuma gwamnan jihar Bello Matawallen Maradun yana ƙoƙarin bin hanyoyin da suka dace domin ganin an sako ƴan matan.

A tsakiyar dare zuwa wayewar garin Juma'a ƴan bindiga suka abka makarantar sakandare ta mata suka yi awon gaba da ɗaliban.

Kwamishinan ilimin ya ce: "Tun da aka tashi da labarin satar yaran nan ranar Juma'a da safe muke ta ƙoƙari mu ga an dawo da su ga iyayensu cikin koshin lafiya, kamar yadda muke tunani In Shaa Allah hakan zai faru nan ba da jimawa ba."

Ya ce wasu ƴan jarida a ranar Lahadi sun yi azarɓaɓin cetwa an ceto yaran nan ba tare da samun tabbaci daga gwamnati ba, amma in Allah Ya so ana kan hanya.

Kwamishinan ya ce ba ya so ya ce wani abu mai yawa kan batun dawo da yaran amma nan ba da jimawa ba za a samu labari mai daɗi.

"Mai girma gwaman ba ya ko iya bacci, kullum yana kan waya yana tsara yadda abubuwa za su kasance."

Kwamishinan ya ce gwamnatin Zamfara ta san inda yaran suke kuma yawansu bai kai yadda kafafen yada labarai ke fada ba, "su 279 ne aka dauke ba 317 ba."

Matawalle

Asalin hoton, Zamfara Govt

Bayanan hoto, "Mai girma gwaman ba ya ko iya bacci, kullum yana kan waya yana tsara yadda abubuwa za su kasance," in ji kwamishinan ilimi na jihar Zamfara.

Sai dai ya ce ba zai ce komai ba kan batun ko su waye suka sace yaran, "ba na ason amsa wannan tambayar amma dai ana nan ana bincike."

Ya yi kira ga iyayen yara da cewa su ƙara haƙuri ita ma gwamnati tana cikin fargaba kamar su, amma ya ba su ƙwarin gwiwar cewa komai ya kusa zuwa karshe don har shugaban kasa ya shiga cikin maganar.

"Shi kansa Shugaba Buhari ransa ya baci da batun satar yaran amma ya jinjina wa gwamnan jihar Zamfara kan ƙoƙarin ceto yaran da yake yi.

Ibrahim Gusau ya ce da zarar an dawo da yaran za su koma makaranta su ci gaba da karatu don "mu a jihar Zamfara mun gane ilimin ƴaƴa mata na da matuƙar muhimmanci, don haka ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba."

Satar ɗumbin 'yan makaranta a Najeriya, matsala ce da ta zama ruwan dare tun bayan mummunan lamarin 'yan matan Chibok a 2014, waɗanda har yanzu ba a gano wasunsu ba.